Kano: Jigon ADC Ya Maka Ganduje a gaban Kotu kan Kafa Hisbah Fisibilillahi

Kano: Jigon ADC Ya Maka Ganduje a gaban Kotu kan Kafa Hisbah Fisibilillahi

  • Jigo a jam'iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC, Alhaji Ibrahim Ali Amin Little ya bayyana takaicin yadda Abdullahi Umar Ganduje ya yi biris da korafinsa
  • Little ya rubuta wasika ga masu ruwa da tsaki, daga ciki har da tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje game da kafa hukumar Hisbah mai zaman kanta
  • Ya ce da alama Ganduje ya ki sauraron korafinsa, saboda haka ya dauki mataki na gaba domin hana tsohon gwamnan daga kafa wata Hisbah a jihar Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wani jigo kuma jagora a jam’iyyar ADC a jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Amin “Little”, ya shigar da kara a Babbar Kotun Jihar Kano, yana kalubalantar kafa wata hukuma ta Hisbah mai zaman kanta a jihar.

Kara karanta wannan

Barau ya bukaci a dauki matakin gaggawa game da harin 'yan bindiga a Kano

Little ya dauki wannan mataki ne bayan ya ce duk kokarin da ya yi na neman a dakatar da shirin bai samu nasara ba, duk da gargadin da ya yi cewa hakan na iya zama barazana ga zaman lafiya a jihar.

Little ya kai Ganduje gaban kotu
Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Twitter

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Ibrahim Al'amin Little ya bayyana takaici a kan yadda ake shirin jawo wa Kano matsala da rashin kwanciyar hankali a Kano.

Jagora a ADC ya fusata da yunkurin Ganduje

A baya, Little ya rubuta wasika zuwa ga dukkannin bangarorin da abin ya shafa, inda ya bukace su da su dakatar da yunkurin kafa Hisbah mai zaman kanta, domin kare zaman lafiya da hadin kan al’umma.

An aika kwafin wasikar ga tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da Gwamnan Kano na yanzu, Abba Kabir Yusuf, da Baffa Babba Danagundi, Haruna Ibn Sina, da kuma Hukumar Tsaro ta Farar Hula (DSS).

A sanarwar da ya fitar, Ibrahim Little ya yanke shawarar garzayawa kotu ne sakamakon yadda aka yi burus da gargadin da ya yi.

Dalilin jigon ADC na zuwa kotu

Sanarwar ta kara da cewa Ibrahim Al'amin Little ya dauki matakin ne domin kare jawo babbar matsalar rashin zaman lafiya a Kano.

Kara karanta wannan

'Ku yi likimo', Ganduje ya fadawa 'yan APC dabarar nasara a 2027

Sanarwar ta ce:

“Bayan nuna rashin jin dadi kan matakan da suka dauka a baya-bayan nan da kuma dagewarsu na ci gaba da aiwatar da kafa Hisbah mai zaman kanta, Little ya nemi mafita a Babbar Kotun Jihar Kano.”
Ganduje ya fitar da fom na daukar aikin Hisbah
Ibn Sina rike da fom din sabuwar Hisbah a Kano da Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: Alameen Muhammad Gama|Abdullahi Umar Ganduje
Source: Facebook

Daga cikin wadanda aka sanya a matsayin wadanda ake kara a shari’ar akwai Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Majalisar Dokokin Jihar Kano, da Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Kano.

Sauran wadanda ake kara sun hada da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Baffa Babba Danagundi, da tsohon Shugaban Hisbah, Haruna Ibn Sina.

Ya ce:

“Ina ganin wannan yunkuri (na kafa Hisbah) hanya ce ta tayar da rikici da rusa zaman lafiya, musamman a wannan lokaci da jihar ke fuskantar kalubalen tsaro.”

Kano: Barau na son a magance rashin tsaro

A baya, mun wallafa cewa Sanata Barau I. Jibrin, mai wakiltar Kano ta Arewa a Majalisar Dattawan Najeriya kuma Mataimakin Shugaban Majalisar, ya magantu kan harin 'yan bindiga a Kano.

Kara karanta wannan

Abba ya yi ta maza, ya murkushe yunkurin Ganduje na kafa sabuwar Hisbah a Kano

Sanata Barau ya yi kakkausar suka kan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Zurin Mahauta da ke garin Lakwaya a karamar hukumar Gwarzo, jihar Kano, inda aka sace jama'a.

Sanatan ya bayyana harin a matsayin abin takaici matuka, yana mai jaddada cewa dole ne hukumomin tsaro su dauki mataki cikin gaggawa domin hukunta wadanda suka aikata laifin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng