Barau Ya Bukaci a Dauki Matakin Gaggawa game da Harin 'Yan Bindiga a Kano

Barau Ya Bukaci a Dauki Matakin Gaggawa game da Harin 'Yan Bindiga a Kano

  • Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin ya yi Allah-wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Zurin Mahauta a Gwarzo, Kano
  • Sanata Barau ya yi karin bayani bayan jami’an tsaro sun ceto mutum uku daga cikin biyar da aka sace, kamar yadda rundunar soji ta tabbatar
  • 'Dan siyasar ya bukaci a kara tsaurara tsaro da daukar matakai domin kare rayuka da dukiyoyi yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar a sassan Kano

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Sanata Barau I. Jibrin, mai wakiltar Kano ta Arewa a Majalisar Dattawan Najeriya, ya yi kakkausar suka kan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyen Kano.

Mataimakin Shugaban Majalisan ya bayyana takaicin cewa harin da aka kai Zurin Mahauta da ke garin Lakwaya a karamar hukumar Gwarzo, jihar Kano abin takaici ne.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Kano cikin dare, sun sace wani adadi na mutane

Sanata Barau I Jibrin ya magantu kan harin Kano
Mataimakin Majalisar Dattawa, Barau I Jibrin Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Sanatan ya jaddada cewa dole ne hukumomin tsaro su dauki mataki cikin gaggawa domin hukunta masu laifin tare da hana sake aukuwar irin wannan hari a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barau Jibrin ya magantu kan harin Kano

Sanata Barau Jibrin ya ce mazauna yankinsa sun shaida masa cewa ‘yan bindigan da suka kai harin sun shigo ne daga wasu jihohin makwabta.

Ya bayyana cewa bayanai daga al’umma sun nuna cewa harin ya zo ne bayan makonni ana samun kwanciyar hankali ba tare da wata barazana a yankin ba.

Sanatan ya ce irin wannan kutsen ‘yan bindiga bai dace ba, musamman ga al’umma masu son zaman lafiya da ke kokarin gudanar da rayuwarsu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

An ceto wasu mutanen Kano bayan hari

Sanata Barau Jibrin ya bayyana farin cikinsa da ceto mutum uku daga cikin biyar da aka sace yayin harin. Ya ce wannan nasara ta jami’an tsaro na nuna kwazo da jajircewarsu wajen kare rayuka.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun mamaye coci suna harbe harbe, sun sace mutane a Kogi

Barau na son a kawo karshen matsalar tsaro
Taswirar jihar Kano, inda aka kai hari Gwarzo Hoto; Legit.ng
Source: Original

Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Najeriya, Birged ta uku, ya tabbatar da cewa an riga an ceto mutane uku zuwa yanzu.

Sanatan ya yaba wa jami’an tsaro bisa daukar mataki cikin gaggawa, yana mai bukatarsu da kada su yi kasa a gwiwa har sai an ceto sauran mutane biyu da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su kara zage damtse wajen karfafa tsaro a yankunan da ke fuskantar barazana, tare da kasancewa cikin shiri a kowane lokaci domin dakile ayyukan ‘yan bindiga.

Barau Jibrin ya jaddada cewa tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma shi ne abu mafi muhimmanci, yana mai alkawarin ci gaba da bai wa hukumomin tsaro cikakken goyon baya domin su yi aikinsu yadda ya kamata.

An kashe ladani a Hotoro Maraba

A baya, mun wallafa cewa an shiga firgici da tashin hankali a unguwar Hotoro Maraba da ke birnin Kano, bayan wani matashi ya kashe ladan wani masallaci a lokacin sallar Asubahin ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Wasu manya a Kano sun ajiye Abba a gefe, sun ce Barau suke so a 2027

Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da asuba, lokacin da matashin ya shiga masallacin domin yin sallah, inda ya tarar da ladan tare da wasu mutane uku a ciki.

Bayan haka, matashin ya bukaci a tayar da sallar Asubah, sai dai ladan ya sanar da shi cewa lokacin sallar bai yi ba tukuna. Bayan wannan bayani kuma ya zare wuka, ya ja ladanin waje tare da yanka shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng