Burkina Faso: Sojojin Najeriya da Traore Ya Tsare na Neman Daukin Gaggawa
- Jami’an sojin Saman Najeriya sun ce tsawon zaman da suke yi a kasar Burkina Faso ya koma kama da tsarewa
- Sun musanta duk wani zargi na leƙen asiri ko karya dokokin sararin samaniya, suna cewa aikin hukuma suka tafi yi
- Ma’aikatar harkokin waje ta ce ana tattaunawa mai zurfi domin ganin an sake su kafin Kirsimetin 2025 da ke tafe
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Wasu jami’an sojin saman Najeriya (NAF) da aka rike a Burkina Faso tun makon da ya gabata sun bayyana damuwa kan tsawon lokacin da suka shafe a kasar.
Jami’an, da aka ce su 11 ne, sun bayyana cewa duk da cewa an sanar da su cewa ana gudanar da tattaunawar diflomasiyya, har yanzu ba su ga wani sauyi ba.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya ce jami’an sun sauka ne a birnin Bobo-Dioulasso bayan jirginsu na C-130 ya samu matsala jim kadan bayan tashinsa daga Legas a hanyarsa ta zuwa Portugal.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin saukar jirgin Najeriya a Burkina Faso
A cewar sojojin saman Najeriya, jirgin ya sauka ne bisa ka’idojin sufurin jiragen sama na duniya bayan samun wasu matsaloli.
Sun ce suna da dukkan takardun tashi da saukar jirage, har da tanadin saukar gaggawa idan wata matsala ta taso.
Sai dai hukumomin Burkina Faso sun bayyana cewa an karya dokokin sararin samaniyarsu, lamarin da ya haifar da tsare jami’an da jirgin.
Abin da sojojin da aka tsare suka ce
Jami’an da ke tsare, ta bakin abokan aikinsu, sun karyata dukkan wadannan zarge-zarge, suna cewa ba su da tushe ko hujja.
Sun ce jirgin ya tafi wani aiki ne, ba shi da kayan leƙen asiri ko tattara bayanan wata kasa kamar Burkina Faso.
Dakarun sun kuma zargi ma’aikatar harkokin waje da jinkirin daukar mataki, suna cewa akwai yiwuwar su yi bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara a tsare a wata kasa.
Duk da haka, sun jaddada cewa hulɗarsu da hukumomin Burkina Faso na tafiya cikin ladabi, kuma sun riga sun tuntubi iyalansu.
Jaridar Aminiya ta wallafa wani sako a shafinta na Facebook da ke nuna cewa sojojin sun koka da zaman da suke a Burkina Faso.

Source: Getty Images
Martanin ma’aikatar harkokin waje
Da aka tuntubi kakakin ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya ce ba daidai ba ne a ce ma’aikatar ba ta daukar mataki.
Ya bayyana cewa mukaddashin jakadan Najeriya ya je Burkina Faso tun makon da ya gabata domin ganin jami’an, amma aka hana shi ganinsu.
Ebienfa ya ce ana gudanar da tarurruka da dama da hukumomin Burkina Faso domin ganin an warware matsalar cikin gaggawa.
Jirgin Najeriya ya kai farmaki Benin
A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar sojin saman Najeriya sun kai farmaki ta sama kasar Benin ana shirin kifar da gwamnati.
Rahotanni sun bayyana cewa kai farmakin ya taimaka wajen tarwatsa sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki a kasar Benin.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta tura dakarun kai dauki ne bayan taimakon da jami'an gwamnatin kasar suka nema.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


