Mutuwa Mai Yankar Kauna: An Tabbatar da Rasuwar Tsohon Jagora a NLC ta Kasa
- Kungiyar NLC ta tabbatar da rasuwar tsohon sakatarenta na kasa, Peter Ozo-Esan a asibitin UCH da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo
- NLC ta bayyana marigayin a matsayin dan gwagwarmaya, wanda ya ba da gudummuwa matuka wajen kare hakkin ma'aikata a Najeriya
- Ozo-Eson ya hau kujerar sakataren NLC a watan Agustan 2014, bayan hukuncin da Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (NEC) ta kungiyar ta yanke
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo, Nigeria - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta rasa daya daga cikin manyan jagororin da suka rike mukamai a baya.
Tsohon Sakatare Janar na Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Peter Ozo-Eson, ya riga mu gidan gaskiya a jihar Oyo da ke Kudancin Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa 'dan tsohon sakataren NLC na kasa ne ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa a wata sanarwa da ya fitar jiya Litinin, 15 ga watan Disamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NLC ta tabbatar da rasuwar Uzo-Eson
Haka zalika, Ƙungiyar Kwadago ta NLC ta sanar da rasuwar ta sa a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook.
NLC ta bayyana cewa marigayi Ozo-Eson ya rasu ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Disamba, 2025 a Asibitin University College Hospital (UCH) da ke Ibadan, babban birnin Oyo.
“Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya na sanar da rasuwar tsohon Sakataren Janar na ƙungiyar, Kwamared (Dr.) Peter Ozo-Eson, cikin matuƙar alhini."
"Ba za mu taba manta wa da kwazonsa, basira da sadaukarwar da ya yi ta tsawon lokaci wajen kare muradun ma’aikata da gwagwarmayar ƙwadago a Najeriya ba, ba za a iya goge gudummuwar da ya bayar ba.
“Za a yi kewarsa matuƙa tun daga Ƙungiyar Kwadago, ma'aikata baki ɗaya, da dukkan waɗanda suka yi tarayya da shi wajen burinsa na gina adalci da daidaito a cikin al’umma,” in ji sanarwar NLC.
Takaitaccen bayani kan tsohon sakataren na NLC
An naɗa Ozo-Eson a matsayin Sakataren NLC a watan Agustan 2014, bayan hukuncin da Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (NEC) ta ƙungiyar ta yanke a taronta da ya gudanar a jihar Enugu.
Kafin naɗinsa a wannan matsayi, marigayi Peter Ozo-Eson ya riƙe muƙamin Babban Masanin Tattalin Arziki na NLC tare da shugabancin sashen bincike na ƙungiyar.
Ya bar ofis a shekarar 2019 bayan kammala wa’adinsa, inda Emmanuel Ugboaja ya gaje shi.

Source: Facebook
Ƙungiyar NLC ta kara da cewa za a fitar da sanarwar karin bayani game da shirye-shiryen jana'izar marigayin nan ba da dadewa ba.
Tsohon jakadan Najeriya ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar IEDPU ta tabbatar da rasuwar tsohon shugabanta kuma tsohon jakadan Najeriya a kasar China, Sheikh Uthman AbdulAzeez.
An ruwaito cewa AbdulAzeez ya rasu yana da shekaru 71 a daren ranar Asabar, 13 ga watan Disamba, 2025 bayan gajeriyar rashin lafiya.
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, da tsohon shugaban Majalisar dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki sun mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


