Aisha Ta Fadi yadda 'Cin Abinci' Ya Jawo wa Buhari Rashin Lafiya a 2017
- Aisha Buhari ta ce ba guba ba ce ta jawo rashin lafiyar da ta kai shugaba Muhammadu Buhari jinyar kwanaki 154 a 2017 London
- Ta bayyana cewa jita-jita a fadar Aso Rock sun jawo tsaiko da katse shan magani da aka saba ba shi a lokuta na musamman
- Bayanan Aisha Buhari sun fito ne daga wani sabon littafin tarihin marigayin da aka ƙaddamar a fadar shugaban kasa a Abuja
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Aisha Buhari ta bayyana cewa rashin lafiyar da ta tilasta marigayi Muhammadu Buhari daukar hutun jinya na tsawon kwanaki 154 a shekarar 2017 ta samo asali ne daga lalacewar tsarin cin abinci.
Matar marigayin ta bayyana haka ne yayin da ta karyata cewa ba wai guba ko wata cuta ta dabam ba ce ta kama Buhari ba.

Source: Getty Images
Punch ta wallafa cewa ta jaddada cewa mijinta bai kamu da wata cuta ba, illa dai katsewa da tangarda a tsarin abinci da shan magani da ta saba kula da su tun kafin su koma zama a fadar Aso Rock.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayyanan nata na cikin wani sabon littafi mai taken From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari, wanda Dr Charles Omole ya rubuta.
Bayani kan lafiyar Muhammadu Buhari kafin 2017
Littafin ya ruwaito cewa Aisha Buhari ta dade tana kula da tsarin abincin mijinta, tana ba shi abinci da sinadaran karin lafiya a lokuta domin taimaka wa jikinsa.
Daily Post ta wallafa cewa ta ce jikin tsofaffi na bukatar kulawa, tana mai cewa Buhari ba shi da wata cuta mai tsanani, kawai yana bukatar kiyaye masa tsarin shan magani ne.
A bayanin da ta yi, Aisha Buhari ta ce wannan tsari ya yi aiki tsawon lokaci tun suna Kaduna kafin su koma Aso Rock Villa.
A cewar littafin, Aisha Buhari ta tara wasu muhimman jami’ai da suka hada da likitan Buhari, Suhayb Rafindadi, da CSO Bashir Abubakar, da mai kula da gida, da shugaban SSS, inda ta yi musu bayani kan yadda tsarin zai kasance.
Dalilin rashin lafiyar Buhari a 2017
Sai dai littafin ya bayyana cewa tsarin ya fara rushewa bayan yaduwar jita-jita da tsoratarwa a cikin fadar shugaban kasa.
A cewar Aisha Buhari, an fara yada jita-jitar cewa tana shirin kashe mijinta, lamarin da ya jefa Buhari cikin shakku na wani lokaci.
Ta ce Buhari ya yarda da labarin na kusan mako guda, inda ya fara kulle kansa, abin da ya fi muni shi ne jinkirtawa ko tsallake abinci, tare da dakatar da shan magungunan gaba daya.

Source: Twitter
Wannan tabarbarewa ce, inji littafin, ta kai ga tafiyarsa sau biyu zuwa Birtaniya domin jinya a 2017, inda ya mika mulki ga mataimakinsa, Yemi Osinbajo.
An kaddamar da littafin tarihin Buhari
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sabon littafin marigayi Muhammdu Buhari.
Legit Hausa ta gano cewa an kaddamar da littafin ne a fadar shugaban kasa, a gaban matarsa, Aisha Buhari da manyan kasa.
Matar shugaban kasa, Remi Tinubu, mai alfarma Sarkin Musulmi na cikin manyan da suka halarci kaddamar da littafin a Abuja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


