Gwamna Aiyedatiwa Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Gwamnonin PDP Ke Komawa APC
- Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta karbi wasu gwamnonin jam'iyyun adawa da suka sauya sheka zuwa cikinta bayan lashe zabe
- Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya yi tsokaci kan dalilin da ya sa gwamnonin jam'iyyun adawa ke tururuwar komawa jam'iyyar adawa
- Aiyedatiwa ya nuna cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, sun taka rawar gani wajen jan hankalin gwamnonin zuwa APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya yi magana kan sauya shekar da wasu gwamnonin adawa ke yi zuwa jam'iyyar APC.
Gwamna Aiyedatiwa ya ce tasirin sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa ne ya ja hankalin wasu gwamnonin jam’iyyun adawa zuwa jam'iyyar APC.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana hakan ne a yayin rangadin da ya kai wasu kananan hukumomin jihar domin godiya ga al’umma.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya je rangadi
Rangadin ya fara ne da kananan hukumomin Akoko guda hudu da suka hada da Akoko ta Arewa maso Yamma, Akoko ta Arewa maso Gabas, Akoko ta Kudu maso Gabas da Akoko ta Kudu maso Gabas.
Gwamna Aiyedatiwa ya gode wa mazauna yankin bisa goyon bayan da suka ba shi a bana, tare da karfafa musu gwiwar goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.
A sakatariyar karamar hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma, gwamnan ya kaddamar da motocin aiki guda biyar da aka tanadar wa sarakunan gargajiya, da kuma bas daya ga kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya (NULGE).
Meyasa gwamnoni ke komawa APC?
Yayin da yake jawabi a taron, Gwamna Aiyedatiwa ya danganta karuwar karfin APC da bunkasar ababen more rayuwa a fadin kasar nan da sauye-sauyen Shugaba Tinubu.
Gwamnan ya ce tasirin wadannan sauye-sauyen ne ya jawo gwamnonin wasu jam’iyyun siyasa zuwa APC.
Ya kuma bayyana cewa ya gana da abokin hamayyarsa a zaben gwamna na shekarar 2024 daga jam'iyyar PDP, Hon. Agboola Ajayi, kuma ya yanke shawarar shiga APC nan gaba kadan.

Source: Twitter
Gwamna Aiyedatiwa ya yi godiya
Gwamna Aiyedatiwa ya kara da cewa sauye-sauyen Shugaba Tinubu sun bude kofar samun cigaban tattalin arziki a jihar Ondo, inda ya ambaci aikin fadada titin Ikare–Akungba zuwa hannu biyu a matsayin hujjar cigaba a yankin Akoko.
“Na zo ne domin gaishe ku da kuma gode muku. Wasu na cewa ’yan siyasa ba sa dawowa bayan zabe. A halin yanzu ba ni da zabe. Na zo ne kawai domin nuna godiyata ga kowa bisa goyon bayan da kuka ba gwamnatina.”
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa
Gwamna Kefas ya yi rajista da APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya yanki katin zama mamba a jam'iyyar APC.
Shugaban jam'iyyar APC na mazabar mazabar Hospital Ward ne ya yi wa Gwamna Kefas rajista a wani karamin taro a gidan gwamnati da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Yin rajistarsa a APC na zuwa ne bayan ya rabu da jam'iyyar PDP wadda ya lashe zabe karkashinta a shekarar 2023.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

