Tinubu Ya Sa Labule da Hafsoshin Tsaro bayan Amincewa da Tura Sojoji Benin
- Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya kira manyan hafsoshin tsaro zuwa fadar shugaban kasa da ke Aso Rock Villa a birnin tarayya Abuja
- Shugaban kasat ya sanya labule da hafsoshin tsaron da Yammacin ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025, inda suka tattauna muhimman batutuwa
- Ganawar ta su dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kokarin samo hanyoyin da za a kawo karshen matsalolin rashin tsaro da suka addabi 'yan Najeriya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da manyan hafsoshin tsaron kasa.
Shugaba Tinubu na gudanar da taron na sirri ne da manyan hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa da ke fadar Aso Rock, a birnin tarayya Abuja.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa taron ya fara ne da misalin karfe 6:01 na yammacin ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro
Hafsoshin tsaron sun isa harabar fadar kafin a rakasu zuwa ofishin shugaban kasa.
Rahoton Daily Post ya nuna cewa wannan shi ne taron farko da Tinubu ke yi da manyan shugabannin sojoji tun bayan rantsar da Janar Christopher Musa (mai ritaya) a matsayin sabon Ministan Tsaro a ranar 4 ga watan Disamba.
Duk da cewa ajandar taron na ranar Litinin ba a bayyana ta ba a hukumance, ana gudanar da ganawar ne yayin da dalibai 115 da aka sace daga wata makarantar kwana ta Katolika a watan Nuwamba har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane.
Ana samun matsalolin rashin tsaro
A ranar 26 ga watan Nuwamba, Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan tsaron kasa tare da ba da umarnin daukar sababbin jami’ai a hukumomin tsaro.
Haka kuma, ya bayar da umarnin janye dukkan ’yan sandan da ke aiki a matsayin masu tsaron manyan mutane (VIPs).
Taron ya zo ne ’yan kwanaki bayan Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Tinubu ta tura sojoji zuwa Jamhuriyar Benin, biyo bayan yunkurin juyin mulki da aka yi a kasar.

Source: Facebook
Karanta wasu labaran kan Tinubu
- "Yana kaunar 'yan Najeriya," Tinubu ya tuno da wasu abubuwa 4 game da Buhari
- An fara gunaguni bayan mai tsaron Tinubu ya zama Birgediya Janar a soja
- Matawalle: Kungiya ta ba Tinubu shawarar abin da ya dace da karamin Ministan tsaro
- "Sako ya kai ga Shugaban Ƙasa:" Sheikh Asada ya shirya zuwa kotu da Matawalle
- Wike ya sake tabo batun goyon bayansa ga Tinubu a zaben 2023
Tinubu ya yi ta'aziyyar mataimakin gwamnan Bayelsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna jimaminsa kan rasuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.
Shugaba Tinubu ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Bayelsa kan rasuwar marigayin wanda ya yi bankwana da duniya.
Mai girma Tinubu ya bayyana marigayi Ewhrudjakpo a matsayin jajirtaccen mutum mai gaskiya da rikon amana, wanda ya yi wa jihar Bayelsa da Najeriya hidima cikin kishin kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

