Za a Sarara: Ranaku 3 da Ƴan Najeriya Za Su Samu Hutu a Disamba 2025, Janairu 2026
Abuja - A yayin da shekarar 2025 ke shirin karewa, ‘yan Najeriya na ɗokin zuwan ranakun hutu da za a ayyana a watan Disamba 2025 da Janairun 2026.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gwamnatin Najeriya ta kan ba da hutu ne yayin tunawa da wasu muhimman ranaku ko bukukuwa, da zai ba 'yan kasar damar gudanar da wadannan bukukuwa tare da iyalansu.

Source: Twitter
'Yan Najeriya na jiran samun hutu
Disamba da Janairu ba iya watanni ne da ke alamta karewa da farawar shekara ba; suna zama lokacin bukukuwan da ma'aikata ke yin huta daga aiki kuma su yi nishadi da iyalansu, in ji wani rahoto na BBC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin farin ciki, kungiyoyi, hukumomi, ma'aikatu da sauransu suna da al'adar rufe wuwaren aikinsu a duk lokacin da karshen Disamba ta zo.
Duk da haka, ga waɗanda ba a rufe wuraren aikinsu a Disambar, akwai kuma ranakun hutu domin ba su damar yin bukukuwan karshe da farkon shekara tare da iyalansu.
2025/2025: Ranakun hutu a Najeriya
Legit Hausa ta tattaro jerin ranakun hutun aiki da gwamnatin tarayya za ta ayyana a watan Disamba 2025 da Janairun 2026.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta tarayya, karkashin jagorancin Minista Olubunmi Tunji-Ojo, ce ake sa ran za ta fitar da sanarwar a hukumance kafin makon karshe na watan Disamba 2025.
Jerin ranakun da Legit Hausa ta tattaro zai taimaka muku wajen tsara yadda za ku gudanar da bukukuwan hutun yadda ya kamata.
Kirsimeti: 25 ga Disamba 2025
Ga mabiya addinin Kirista na duniya, ranar Kirsimeti tana zuwa ne a ranar 25 ga Disamba duk shekara, duk da cewa ana gabatar da wasu shagulgulan al’adu tun daren Kirsimeti.
Ko da yake ba a san ainihin ranar haihuwarsa ba, amma 25 ga Disamba rana ce ta tunawa da haihuwar Annabi Isa Almasihu, kuma ana bikin Kirsimeti ne tun daga karni na hudu.
A Najeriya, ana sa ran bikin Kirsimeti na 2025 zai kasance cike da farin ciki, shagulgula da nishadin iyalai, inda yara za su samu damar raya al’adu, shiga ayyukan coci da bukukuwa ba tare da matsin karatu ba.
Ranar Dambe: 26 ga Disamba 2025
Duk da cewa sunansa kenan, amma Ranar Dambe (Boxing Day) ba ta da alaka da dambe ko faɗa. Ana gudanar da bikin ranar ne duk shekara a ranar 26 ga Disamba, watau washegarin Kirsimeti.
A shekarar 2025, Boxing Day zai fado ne a ranar Juma’a, kuma ana bikin sa a Najeriya, Birtaniya, Australia, New Zealand, Canada da sauran kasashen Commonwealth, in ji rahoton Sky News.
A wannan rana, ana rufe bankuna da yawancin ofisoshi idan a ranar aiki ne. Iyalai da dama kan gayyaci juna su ci abinci cikin walwala, galibi daga ragowar abincin Kirsimeti, yayin da wasu ke fita siyayya domin samun garabasar bayan Kirsimeti.

Source: Getty Images
Sabuwar shekara: 1 ga Janairu 2026
Ranar 1 ga Janairu 2026, wacce za ta fado a ranar Alhamis, ita ce ranar sabuwar shekara, kuma ita ce farkon sabuwar shekara a kalandar Gregorian.
Shafin History.com ya ruwaito cewa an fara bikin sabuwar shekara tun kusan shekaru 4,000 da suka wuce a tsohuwar kasar Babila. A wancan lokaci, sabuwar shekara na farawa ne a wajajen 21 ga watan Maris.
Daga baya, Sarkin Roma Julius Caesar ya gyara kalandar, inda ya ayyana 1 ga Janairu a matsayin farkon sabuwar shekara.
Ga ‘yan Najeriya da dama, sabuwar shekara tana da muhimmanci matuka, domin tana nuna sabon babi na yin nazari kan abin da ya wuce, sanya sababbin buruka da fatan alheri a gaba.
Kirsimeti: An ba ma'aikata kyautar N150,000
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Ebonyi, Francis Ogbonna Nwifuru, ya sanya farin ciki a zukatan ma'aikatan jiharsa, yayin da ya ba su kyautar N150,000.
Gwamna Francis Ogbonna Nwifuru ya amince a rabawa ma'aikatan jihar wannan kudi ne a matsayin alawus domin su yi bukukuwan Kirsimeti cikin walwala.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki ya yi daidai da kudurin gwamnatinsa na inganta walwalar ma’aikata, duk da karancin kudaden shiga da jihar ke fuskanta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


