Abin Tausayi: Matashi Ya Shiga Masallaci Ya Kashe Mutane 3 a Wani Yanayi a Abuja
- Wani matashi da ake zargi ya sha miyagun kwayoyi, ya kashe mutane uku a lokacin sallar Asubahi a wani masallaci a Abuja
- Rahotanni daga shaidun gani da ido sun nuna cewa matashin mai suna, Laminde Boka ya kashe mutanen ana dab da fara sallah a Gwarimpa
- Mutane sun yi kokarin kama wanda ake zargin, kuma sun lakada masana na-jaki har ya mutu a kusa da masallacin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Mutane sun shiga tashin hankali da wani matashi ya hallaka mutane uku da suka fito sallar Asuba a unguwar Gwarimpa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Lamarin ya faru ne a masallacin Kado Bimko da ke shiyyar First Avenue, inda matashin ya yi wa mai kula da masallacin da wasu mutane biyu kisan gilla ta hanyar soka musu wuƙa.

Source: Original
Jaridar Aminiya ta tattaro cewa matashin ya aikata wannan danyen aiki ne gabanin karisowar Liman domin fara sallar Asuba kamar yadda aka saba a masallacin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda matashi ya kashe mutane a masallaci
Wani shaidar gani da ido, Muhammad Auwal, mai shago a kusa da masallacin, ya ce wanda aka fara kashewa shi ne Alhaji Wanzam, dattijo ne mai sana’ar wanzanci a yankin.
Ya ce:
"Alhaji Wanzam yakan fito daga gidansa da ke kusa da masallacin tun ƙarfe 4:000 na asuba. Idan ya fito zai shiga ya share masallacin gaba daya.
"A ranar da abin ya faru, ya fito kamar yadda ya saba ya fara aikinsa na taaftace masallaci, kwatsam wanda ake zargi ya danno kai da wuka, ya rinka caka masa ita har ya rasu.
Shaidar ya kara da cewa matashin wanda ake kira da Laminde Boka, ya tunkari sauran mutanen da suka fito sallah da wuri, ya fara farmakarsu da wuka bayan ya kashe Alhaji Wanzam.
Ana zargin matashin ya sha miyagun kwayoyi
An ce matashin, wanda ake zargin ya sha kwayoyin maye, ya kuma kashe wani mai injin nika a kasuwar da ke kusa da masallacin lokacin da ya yi kokarin tare shi ya kwace wukar.
Bayan haka, Laminse Boka ya sake bin wasu da suka fito sallah, inda ya cimma daya daga cikinsu da ya fadi yana tsakiyar guda, ya soka masa wuka har lahira.

Source: Getty Images
Mutane sun kashe matashin a Abuja
A ƙarshe, jama’a sun yi nasarar kama shi a harabar masallacin, suka fara jifansa da duwatsu, sannan daga baya suka buge shi da sanda, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take.
Ƙoƙarin da aka yi domin jin ta bakin DPO na Gwarimpa bai yi nasara ba, domin an shaidawa manema labarai cewa ba ya ofis a lokacin, kamar yadda Punch ta kawo.
Matashi ya kashe ladani a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa al’ummar Hotoro Maraba a Kano sun shiga firgici bayan wani matashi ya kashe ladanin masallaci a lokacin sallar Asubahi.

Kara karanta wannan
Lamari ya munana: An hallaka matashi bayan zargin daɓawa mahaifiyarsa wuƙa a Niger
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da Asubah, inda matashin ya zo masallaci domin yin Sallah, ya tarar da ladan da wasu mutane uku a ciki.
Bisa bayanan da aka samu, matashin ya bukaci a tayar da sallah, amma ladan ya sanar da shi cewa lokacin sallar Asuba bai yi ba tukuna, kawai gani aka yi ya zaro wuka ya caka wa ladan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

