"An San Maboyarsa": Masanin Tsaro Ya Yi Magana kan Kama Bello Turji

"An San Maboyarsa": Masanin Tsaro Ya Yi Magana kan Kama Bello Turji

  • Wani masanin tsaro a Najeriya, Yahuza Getso ya bayyana cewa Bello Turji bai 'buya a ko ina ba kamar yadda ake zaton cewa yana gudun neman tsira
  • Dr Getso ya bayyana cewa matukar gwamnati da gaske ta ke, tsaf za ta tabbatar da cewa dakarun Najeriya sun yi ram da shi a kasa da awanni 24
  • Bayaninsa na zuwa ne a lokacin da Najeriya ta dauki zafi game da zarge-zargen da ake yi wa Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle na ta'addanci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wani masani kan harkokin leken asiri da tsaro, Dr Yahuza Getso, ya ce shugaban yan bindiga Bello Turji bai buya ba, kamar yadda mutane da yawa ke tunani.

Masanin tsaron ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan Turji ya fito da bayanai, yana musanta cewa akwai wata alaka tsakaninsa da karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle.

Kara karanta wannan

"Sako ya kai ga Shugaban Ƙasa:" Sheikh Asada ya shirya zuwa kotu da Matawalle

Masanin tsaro ya soki gwamnatin Tinubu
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A hira da ya yi da Channels Television a ranar Litinin, Dr. Yahuza Getso ya bayyana cewa matukar gwamnati da gaske ta ke, za ta iya kama Turji a cikin awanni 24.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masanin tsaro ya magantu kan Bello Turji

Dr. Bello Turji ya bayyana cewa sau da yawa an bai wa gwamnati bayanai kan inda Turji yake, amma duk da haka ba a dauki matakin kama shi ba.

Getso ya ce wannan lamarin ba wai batun Turji da Ministan Tsaron Kasa kadai ba ne, har ma da batun tsaro na kasa da kuma karfin gwiwa wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Getso ya ce za a iya kama Turji idan an so
Jagoran 'yan ta'adda Bello Turji da Shugaban Najerya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: @ZagazOlaMakama/Bayo Onanuga
Source: Twitter

A cewarsa, akwai matsalolin magudi da rashin gaskiya a bangaren shari’a da hukumomin tsaro da suka sa ba a iya kaiwa ga nasarar kama Turji ba.

Haka kuma, ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da bincike da kuma rashin bayani daga hukumomin tsaro da shari’a kan wadanda ake zargin sun taimaka wa Turji.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya fadi gaskiya kan alakanta shi da Matawalle, ya kira sunaye a bidiyo

Yadda Turji ya kare Bello Matawalle

A wani bidiyo da Turji ya fitar a karshen mako, ya musanta zargin cewa yana hulɗa da Ministan Tsaron Kasa, Bello Matawalle.

Ya bayyana cewa wasu tsofaffin gwamnonin Arewa, inda ya ce wasu na taimakawa wajen karuwar rashin tsaro a yankin.

Har ila yau, ya ce ya shiga wasu tarurrukan zaman lafiya da gwamnatin jihar Zamfara a lokacin mulkin tsohon gwamna, Bello Matawalle.

Dr Getso ya yi tambaya:

"Ina bayanan leken asirin da aka bayar? Wa ya shirya tattaunawar? Da wa suke cikin haɗin gwiwa? A cewarsa, akwai matsalolin rashin gaskiya a shari’a da hukumomin tsaro, wanda hakan ya hana cimma nasara wajen kama Turji."

Sheikh Asada ya magantu game da Matawalle

A wani labari, mun wallafa cewa fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Murtala Asada, ya sake jaddada zarge-zargen da ya dade yana yi kan Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle.

Ya bayyana farin ciki game da yadda sakonsa ya kai wuraren da ya kamata, har kunnen Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, saboda haka Matawalle ya fito domin martani ga zargin.

Kara karanta wannan

Halin da Bello Turji ke ciki bayan hallaka na kusa da shi a Sokoto, ya zargi wasu mayaka

Sheikh Asada ya bayyana cewa Matawalle ya tura tsohon kwamishinansa don mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi masa, amma dukkaninsu babu wanda ya iya kore zargin kai tsaye.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng