Dangote Ya Fadi Yadda Trump ke Ji game da Cigaban Matatar Shi a Najeriya

Dangote Ya Fadi Yadda Trump ke Ji game da Cigaban Matatar Shi a Najeriya

  • Aliko Dangote ya ce shugaban Amurka, Donald Trump, na farin ciki da ayyukan matatar shi sabanin rade-radin da ake yadawa
  • Ya bayyana cewa Amurka na daga cikin manyan kasashen da ke sayar wa Najeriya danyen mai da ake sarrafawa a matatar
  • Rashin wadataccen danyen mai a cikin gida na tilasta wa Najeriya sayo mai daga Ghana, wasu kasashen Afirka da Amurka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Lagos – Aliko Dangote ya karyata rade-radin da ke cewa gwamnatin Amurka ko shugaba Donald Trump na nuna rashin jin dadi game da ayyukan matatar shi da ke Lekki a jihar Lagos.

Dangote ya ce akasin haka ne ke faruwa, inda ya bayyana cewa Trump “na matukar farin ciki” da yadda matatar ke aiki, duba da irin girman kasuwancin da ke tsakanin Najeriya da Amurka a bangaren danyen mai.

Kara karanta wannan

Bayan dawo da lita N699, Dangote ya sa ranar fara aikin sabon farashin fetur

Aliko Dangote da Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump da attajirin Afrika, Aliko Dangote. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Punch ta wallafa cewa Dangote ya bayyana haka ne a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a harabar matatar shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangantakar matatar Dangote da Trump

A hirar da ya yi, Aliko Dangote ya ce ikirarin da wasu ke yi cewa Amurka na adawa da matatar Dangote ba shi da tushe.

A cewarsa, Amurka ba makiya ba ce ga aikin matatar, illa ma tana daga cikin manyan kasashen da suke cin gajiyar kasuwancin da ke tsakaninsu.

Ya bayyana cewa Amurka na daga cikin manyan masu sayar wa matatar Dangote danyen mai, wanda ake sarrafawa domin samar da man fetur da sauran kayayyakin mai.

“Idan wani ya ce Trump ba ya farin ciki da matatar mu, wannan ba gaskiya ba ne. Trump ya fi kowa farin ciki da matatar Dangote saboda girman kasuwancin da muke,”

- Inji Dangote

Ya kara da cewa danyen man da ake sayowa daga Amurka na da matukar yawa, lamarin da ke sa kasar ta zama babbar mai amfanuwa daga ayyukan matatar, musamman ta fuskar ciniki da kudin shiga.

Kara karanta wannan

Jamilu Zarewa: Yadda za a magance kishi, mata su zauna lafiya a gidan aure

Wani sashe na matatar Aliko Dangote
Matatar Dangote da ke jihar Legas a Najeriya. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

Kalubalen samun danyen mai a Najeriya

Dangote ya bayyana cewa har yanzu Najeriya ba ta kai matakin samar da isasshen danyen mai da zai wadatar da bukatun cikin gida ba.

Daily Post ta wallafa cewa ya ce wannan matsala ce da ke tilasta wa kamfaninsa sayen danyen mai daga kasashen waje a halin yanzu.

Dangote ya ce:

“Ba ma samun isasshen danyen mai a cikin gida, shi ya sa muke saye daga Ghana da wasu kasashen Afirka. Haka kuma muna sayen danyen mai daga Amurka,”

Dangote ya jaddada cewa wannan yanayi na nuna bukatar kara habaka samar da danyen mai a Najeriya domin rage dogaro da kasashen waje a nan gaba.

A cewar Alhaji Aliko Dangote, Najeriya na sayen akalla ganga miliyan 100 na danyen mai daga Amurka a duk shekara.

Dangote ya magantu kan rage kudin mai

A wani labarin, mun kawo muku cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi karin haske bayan rage kudin litar man fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

Amurka: Trump ya kwace babbar tankar mai mallakar kamfanin Najeriya

'Dan kasuwar ya ce zuwa gobe Talata, 16 ga Disamban 2025 'yan Najeriya za su fara cin gajiyar rage kudin mai da ya yi.

A hira da ya yi da, Dangote ya koka kan yadda Najeriya ke cigaba da ba mutane damar shigo da fetur daga kasashen waje.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng