Matsalar Tsaro: Tsofaffin Gwamnoni 2 da Ake Zargi da Hannu a Ayyukan Ta'addanci

Matsalar Tsaro: Tsofaffin Gwamnoni 2 da Ake Zargi da Hannu a Ayyukan Ta'addanci

  • Jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji ya zargi wasu tsofaffin gwamnonin Arewa da kafa tubalin rashin tsaro a jihohin Zamfara da Sokoto
  • A cikin wani bidiyo, Bello Turji ya musanta karbar N30m a tattaunawar zaman lafiyar Zamfara, yana cewa bai taba mallakar ko N5m ba
  • Tsofaffin gwamnonin da aka ambata sun ki mayar da martani, yayin da majiyoyi ke cewa ba za a yarda da kalaman dan ta’adda ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Fitaccen jagoran ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Bello Turji, ya zargi wasu tsofaffin gwamnonin Arewa da haddasa matsalar rashin tsaro da ta dade tana addabar yankin, musamman jihohin Zamfara da Sokoto.

Turji ya kuma tabbatar da cewa ya taba shiga wasu tarukan zaman lafiya da gwamnatin jihar Zamfara ta shirya a lokacin mulkin wani tsohon gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Sababbin jakadu: Mutane 5 da Tinubu ya nada da suka fuskanci manyan zarge zarge

Bello Turji ya zargi tsofaffin gwamnonin Arewa 2 da daukar nauyin ta'addanci.
Bello Turji, jagoran 'yan ta'adda da ake nema ruwa a jallo a Arewacin Najeriya. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Bello Turji ya zargi tsofaffin gwamnoni 2

A cikin wani faifan bidiyo da Legit Hausa ta gani a shafin Zagazola Makama na X, Bello Turji ya musanta ikirarin cewa ya karbi kudi har Naira miliyan 30 ko wata alfarma domin shiga tattaunawar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan bullar wannan bidiyo, da kuma jin irin zargin da Bello Turji ya yi wa tsofaffin gwamnonin Arewan biyu, jaridar Vanguard ta yi kokarin jin ta bakin tsofaffin gwamnonin, amma abin ya ci tura.

Jaridar ta ce har zuwa lokacin da ta hada rahotonta, ba ta samu jin ta bakinsu ba, domin ba su amsa kiran waya ba, haka kuma ba su mayar da martani ga sakonnin waya da na WhatsApp da aka tura musu ba.

Sai dai wasu majiyoyi da ke kusa da tsofaffin gwamnonin sun yi watsi da kalaman Turji, suna mai cewa bai dace a yarda da furucin dan ta’adda ba.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi, mataimakin gwamna ya fadi a ofis, an wuce da shi asibiti

Wata majiya ta ce:

“Me ya sa za a dauki kalaman dan ta’adda da muhimmanci? A bayyane yake yana kokarin nuna kansa a matsayin wanda aka zalunta. Duk abin da ya fada karya ne.”

Wata majiya kuma ta kara da cewa:

“Zan iya tabbatar maka cewa Turji karya yake. Mutumin da ya yi kisan gilla sau da dama shi ne za a yarda da shi? Duk abin da ya fada karya ne tsantsa.”

Bidiyon Bello Turji ya tayar da kura

Bello Turji ya bayyana wadannan zarge-zarge ne a cikin wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, inda ya zargi tsofaffin shugabannin siyasa a Zamfara da Sokoto da aza harsashin matsalar rashin tsaro da yankin ke fuskanta tsawon shekaru.

Ya yi ikirarin cewa wasu gwamnatocin baya sun dauki nauyin makamai ga kungiyoyin sa-kai da ake kira ‘Yan Banga, inda ya ce ana amfani da su wajen kai farmaki kan Fulani, lamarin da ya kara rura wutar tashin hankali.

Kara karanta wannan

'Za a kamo shi,' Benin ta gano kasar da sojan da ya so juyin mulki ya buya

Turji ya bukaci a kama tare da binciki tsohon gwamnan Sokoto da tsohon gwamnan Zamfara kan rawar da ya ce sun taka a rikicin.

Ya ce:

“Muna fadin a bayyane cewa tsofaffin gwamnonin Zamfara da Sokoto su ne ke da alhakin masifun da suka afkawa wadannan jihohi.”
Bello Turji ya yi ikirarin cewa tsofaffin gwamnonin ne suka rura wutar ta'addanci a Zamfara da Sokoto
Bello Turji, jagoran 'yan ta'adda da ake nema ruwa a jallo a Arewacin Najeriya. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: UGC

Bello Turji ya musanta shiga harkar siyasa

Jagoran ‘yan bindigan ya nesanta kansa da duk wata alaka ta siyasa, yana mai cewa ba ya aiki a madadin wani dan siyasa ko wata kungiya.

Ya ce:

“Mu ba ‘yan siyasa ba ne, kuma ba karnukan farautar ‘yan siyasa ba ne. Babu wani mutum da ke goyon bayanmu.”

Maganar Turji na zuwa ne bayan da wani tsohon hadimin tsohon gwamnan Zamfara, Musa Kamarawa, ya zarge shi da karbar Naira miliyan 30 domin shiga tattaunawar zaman lafiya da aka gudanar a fadar gwamnatin Zamfara da ke Gusau.

Sai dai Turji ya karyata wannan zargi a bidiyon, yana mai cewa ko shi tun da aka haife shi bai taba mallakar ko Naira miliyan biyar ba.

An tsorata Bello Turji ya mika wuya

Kara karanta wannan

Manyan kasa za su taru domin kaddamar da littafi da taron tuna Buhari na farko

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Kungiyar matan Arewa maso Yamma ta bukaci dan ta'adda mai garkuwa da mutane, Bello Turji ya ajiye makamai, ya mika wuya.

Kungiyar ta ce matakin ya dace da tsarin da sojojin Najeriya ke bi na haɗa dabarun sulhu da na tsaro domin dawo da doka da oda a yankunan da rikici ya shafa.

Jami’ar hulda da jama’a ta ƙungiyar, Salamatu Bello, ta bayyana cewa mata da al’umma sun gaji da tashin hankali da rashin tsaro da ke addabar yankunan Arewa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com