'Yan Bindiga Sun Mamaye Coci Suna Harbe Harbe, Sun Sace Mutane a Kogi

'Yan Bindiga Sun Mamaye Coci Suna Harbe Harbe, Sun Sace Mutane a Kogi

  • ’Yan bindiga sun kai hari cocin ECWA a yankin Àaaaz-Kiri na karamar hukumar Kabba/Bunu, inda aka sace wasu masu ibada
  • Harin ya zo ne a lokaci guda da wasu hare-hare a Illai da Okeagi a yankin Mopamuro, lamarin da ya jefa al’ummomi cikin firgici
  • Sanata Sunday Karimi da gwamnatin jihar Kogi sun nuna damuwa tare da kira a dauki matakan gaggawa domin dakile ta’addanci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Kogi ta sake fuskantar wani sabon hari da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai, inda suka mamaye wani coci yayin ibada, suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu mutane.

Wasu rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a safiyar Lahadi, 14, Disamba, 2025 yayin da ake ibada a cikin cocin.

Kara karanta wannan

NLC: 'Yan kwadago sun saka ranar zanga zanga a jihohi 36 da Abuja

Taswirar jihar Kogi
Taswirar jihar Kogi da aka kai hari. Hoto: Legit
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ce a cocin ECWA da ke yankin Àaaaz-Kiri, a karamar hukumar Kabba/Bunu aka kai harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kai hari a cocin ECWA a Kogi

Mazauna yankin sun bayyana cewa da safiyar Lahadi ne ’yan bindigar suka shiga garin Àaaaz-Kiri, suna harbe-harbe, abin da ya tilasta wa mutane guduwa zuwa wurare mabambanta.

A cikin wannan rikici, an ce maharan sun kutsa kai har cikin cocin ECWA da ke gudanar da ibadar Lahadi, inda suka kai farmaki kan mutane.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

“Ba a san adadin wadanda aka kashe ba tukuna. Masu ibada suna tsakiyar ibada ne lokacin da aka kai musu hari.”

Ya kara da cewa an tabbatar da mutuwar mutum daya, yayin da iyalai da dama ke neman ’yan uwansu da aka dauka ko kuma suka bata a yayin harin.

“Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutum daya, kuma iyalai da dama na neman ’yan uwansu domin an sace mutane da yawa,”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mataimakin ciyaman a Zamfara bayan karbar kudin fansa

- In ji shi

Hare-haren da aka kai a garin Mopamuro

A wani harin da aka kai, ’yan bindigar sun kai farmaki a yankunan Illai da Okeagi a karamar hukumar Mopamuro da misalin karfe 4:00 na asuba.

Premium Times ta wallafa cewa sun shafe fiye da awa guda suna kai hare-hare kafin a samu damar kiran jami’an tsaro.

An bayyana cewa sun fara ne da kai hari a Jamroro, wani yanki tsakanin Okeagi da Takete Isao, inda suka kashe mutane biyu.

Gwamnan jihar Kogi
Gwamnan jihar Kogi na magana a wani taro. Hoto: Kogi State Government
Source: Facebook

Daga bisani wata kungiya ta kai hari kusa da makarantar Ilai, inda aka kashe mutum daya tare da sace mutane uku.

Martanin gwamnatin Kogi kan harin

Bayan harin, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya jajanta wa al’ummar Illai da Okeagi.

Ya ce:

“Zuciyarmu na tare da mutanen Illai da Okeagi a wannan mawuyacin lokaci. Ana ci gaba da kokarin dawo da tsaro, kuma da yardar Allah za mu yi nasara.”

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Benin bayan fatattakar sojoji masu yunkurin juyin mulki

Sanata mai wakiltar yankin, Sunday Karimi, ya yi Allah-wadai da hare-haren, yana mai kiran daukin gaggawa.

A cikin wata sanarwa, ya ce yana cike da damuwa kan rahotannin kisan kai da sace masu ibada a cocin ECWA da ke Àaaaz-Kiri a safiyar 14, Disamba, 2025.

'Yan bindiga na dabarun kai hari

A wani labarin, mun rahoto cewa Ministan sadarwa, Bosun Tijani ya yi bayani game da dabarun 'yan bindiga wajen kai hari.

Ministan ya ce 'yan ta'adda na amfani da wasu dabarun sadarwa wajen amfani da na'urori, kuma hakan ne ya sa ba a kama su.

Bosun Tijani ya tabbatar da cewa akwai kokari na musamman da gwamnati ke yi domin ganin an dakile hare-haren 'yan ta'adda.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng