An Fara Gunaguni bayan Mai Tsaron Tinubu Ya Zama Birgediya Janar Soja

An Fara Gunaguni bayan Mai Tsaron Tinubu Ya Zama Birgediya Janar Soja

  • An samu ƙorafe-ƙorafe a cikin sojoji kan gaggawar ƙarin girma da aka yi wa dogarin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, Nurudeen Yusuf
  • Wasu jami’an soja na ganin hakan ya saɓa da al’ada da ka’idojin aikin soja tare da jawo yanayi mara dadi a cikin rundunar tsaron Najeriya
  • Sai dai Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa akwai dalilin da ya sa aka yi saurin kara wa Nurudeen Yusuf girma a cikin kankanin lokaci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – An fara gunaguni a cikin rundunar sojin Najeriya bayan ƙarin girma da aka yi wa Kanal Nurudeen Yusuf, mai tsaron Shugaban Ƙasa (ADC), zuwa muƙamin Birgediya Janar.

Wasu jami’an soja da suka yi magana da manema labarai sun bayyana matakin a matsayin abin mamaki, musamman a ƙarƙashin tsarin mulkin dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

APC: Atiku da manyan 'yan adawa sun taso Tinubu a gaba game da mamaye Najeriya

Wasu jami'an soja sun bayyana takaicinsu
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa wani jami’i ya ce ƙanana da matsakaitan jami’ai kamar Laftanar, Kyaftin, Manjo da Laftanar Kanal za su iya samun ƙarin girma bisa bajinta na musamman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun fusata da zukun dogarin Tinubu

Premium Times ta wallafa cewa jami'in ya ce amma daga mutum zuwa Birgediya Janar ta hanyar umarnin shugaban ƙasa kai tsaye abu ne da ba a saba gani ba.

Ya kara da bayyana cewa kuma hakan yana iya haddasa mummunar gaba ga tsarin soja. A cewarsa, hakan na iya karya tsarin ladabtarwa da daidaito da aka gina tsawon shekaru.

A wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 12 ga Disamba, 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin girman Kanal Yusuf zuwa Birgediya Janar.

Takardar karin girman Nurudeen Yusuf na dauke da sa hannun Nuhu Ribadu
Mashawarcin Shugaban Kasa game da tsaro, Nuhu Ribadu Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Facebook

Shugaban Kasa ya bada umarni, an aika wasiƙar zuwa ga Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Wahid Shaibu.

Rahotanni sun ce Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro na Ƙasa, Nuhu Ribadu, ne ya sanya hannu a kan wasikar karin girman,

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

Sai dai, babu cikakken tabbaci daga ofishin NSA ko rundunar sojin kan sahihancin wasiƙar da a yanzu ta fara jawo matsala a a cikin rundunar.

Ran wasu jami'an soja ya baci

Abin da ya ƙara tayar da ƙura shi ne cewa Kanal Yusuf ya samu ƙarin girma zuwa Kanal ne kawai a watan Janairun bana, lamarin da ya sa wannan ƙarin girma ya zama na biyu cikin watanni 12.

Wasu jami’an soja sun kwatanta hakan da abin da ya faru a gwamnatocin baya, inda ADC ke bin tsarin al’ada na halartar Kwalejin Yaƙi da Kwalejin Tsaron Ƙasa kafin samun damar zama Birgediya Janar.

Wasu rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin abokan karatun Yusuf sun nuna takaici, suna zargin cewa an yi masa fifiko fiye da ka’ida.

Sai dai, wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta ce an yi ƙarin girman ne domin daidaita matsayinsa da sauran manyan jami’an tsaro a Aso Villa.

An shawarci Tinubu game da Matawalle

A baya, mun wallafa cewa kungiyar Northern Stakeholders Consultative Initiative ta sake bayyana goyon bayanta ga Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, game da Bello Matawalle.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bada umarni kan kare manyan Najeriya bayan janye 'yan sanda

Kungiyar ta kuma roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada a sauya shi daga mukaminsa duk da yadda zargin da ake yi masa ke kara yawaita da danganta Bello Matawalle da ta'addanci.

Jagoran kungiyar, Yerima Shettima, ya fitar, ta jaddada cewa ci gaba da rike Matawalle a matsayin karamin Ministan Tsaro yana da matuƙar muhimmanci wajen karfafa tsarin tsaron ƙasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng