Zargin Rashawa: Rigima Ta Barke tsakanin Dangote da Wani Babban Jami'in Gwamnati

Zargin Rashawa: Rigima Ta Barke tsakanin Dangote da Wani Babban Jami'in Gwamnati

  • Aliko Dangote ya zargi shugaban NMDPRA Farouk Ahmed da biyan $5m kudin makarantar sakandaren ‘ya’yansa hudu a Switzerland
  • Dangote ya bukaci a gurfanar da Farouk Ahmed a gaban kotun da'ar ma'aikata domin ya bayyana yadda ya samu wadannan makudan kudade
  • Domin kara karfafa zarginsa, Dangote ya fadi wani muhimmin mataki da zai dauka idan Alhaji Farouk ya musanta biyan wadannan kudade

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Lagos – Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya zargi shugaban hukumar kula da harkokin man fetur ta NMDPRA, Farouk Ahmed, da biyan kimanin dala miliyan biyar ($5m) domin karatun sakandaren ‘ya’yansa hudu a kasar Switzerland.

Dangote ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, inda ya bukaci a gudanar da bincike mai zurfi tare da tilasta wa Ahmed ya fito fili ya yi wa ‘yan Najeriya bayani kan yadda aka ce ya iya biyan irin wannan kudi.

Kara karanta wannan

Dangote ya rubuta wasiyya, za a cire wani kaso mai tsoka a dukiyarsa idan ya rasu

Dangote ya ce akwai bukatar a binciki shugaban NMDPRA kan kudin da ya biya na karantun 'ya'yansa a waje
Alhaji Aliko Dangote tare da shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed da ya zarga da rashin gaskiya. Hoto: @zainab_Nasir00
Source: Twitter

Aliko Dangote ya zargi shugaban NMDPRA

A cikin wani bidiyo da The Cable ta wallafa a shafinta na X, an ji Dangote ya ce ya kamata Farouk Ahmed ya gurfana a gaban kotun da'ar ma'aikata (CCT) domin fadin inda ya samu wadannan kudade.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya ce irin wannan zargi, idan aka bar shi ba tare da an samu bayanai masu gamsarwa ba, zai ci gaba da lalata amincewar jama’a da kuma masu zuba jari.

Ya ce:

“Na samu koke-koke daga mutane kan wani jami’in gwamnati da ke da alhakin zartarwa, wanda ya kai ‘ya’yansa hudu makarantar sakandare a waje. Kuma wannan karatu na tsawon shekara ya lakume wa Najeriya dala miliyan biyar.”

Dangote ya ce biyan irin wannan makudan kudade ba zai taba yin daidai da kudin shiga na ma’aikacin gwamnati ba.

Ya ce:

“Idan aka duba kudin shigarsa, bai dace da irin wannan biyan kudi ba. Ko da ni ne zan biya $5m domin kudin makarantar ‘ya’yana, to hukumar haraji za ta binciki yadda na samu kudin da kuma harajin da na biya.”

Kara karanta wannan

Minista ya yi karar malami bayan ya 'bukaci' N150m domin ba shi kujerar gwamna

Dangote zai dauki matakin shari'a

Attajirin dan kasuwar ya bayyana damuwarsa kan wannan al'amar, inda ya ce a Sokoto, jihar da shugaban NMDPRA ya fito, iyaye da dama na fama wajen biyan N100,000 kudin makaranta.

Ya ce:

“A Sokoto mutane na shan wahala wajen biyan N100,000 kudin makaranta. Yara da dama na zama a gida ba sa zuwa makaranta. Amma wani jami’in gwamnati ya biya $5m kudin makarantar ‘ya’yansa hudu. Wannan abu ne mai wuyar fahimta.”

Dangote ya kara da cewa ko ‘ya’yansa ba su yi karatun sakandare a kasashen waje ba, yana mai cewa duk sun yi karatu ne a Najeriya.

Ya ce ba ya neman a cire Ahmed daga mukaminsa kai tsaye ba ne, sai dai a gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da gaskiya, in ji rahoton Punch.

“Ba wai ina kira da a cire shi ba ne, amma a bincike shi yadda ya kamata. Idan ya musanta, zan wallafa dukkan kudin da aka biya wa wadannan makarantu, sannan zan dauki matakin shari’a domin tilasta makarantu su bayyana kudaden da Farouk ya biya.”

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

- Alhaji Aliko Dangote.

Dangote ya ce dole ne a binciki shugaban NMDPRA domin zarge-zargen na da girma.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote. Hoto: Bloomberg
Source: Facebook

Hukumar NMDPRA ta taba musanta zargin

A watan Yuli, 2025, hukumar NMDPRA ta taba musanta irin wannan zargi bayan wata kungiya ta yi zanga-zanga, tana mai cewa an shirya zarge-zargen ne domin a bata sunan Ahmed.

Sai dai Dangote ya ce ya sake tayar da batun ne yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a matatar man Dangote da ke Lekki, inda ya zargi gazawar tsari da kuma cin hanci a bangaren man fetur na kasa.

Ya ce akwai wasu tsirarun masu anfani da shigo da mai daga waje da ke cutar da cigaban kasa da kuma bangaren matatar mai a gida.

Dangote ya yi albishir kan ragin kudin fetur

A wani labari, mun ruwaito cewa, Aliko Ɗangote ya ce gidajen mai da ke sayen fetur daga matatar Dangote za su fara sayar da litar fetur a kan N739 daga 16 ga Disamban 2025.

Ɗangote ya fadi hakan ne a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai, inda ya tunatar da jama’a cewa tuni kamfanin ya rage farashin fetur daga N828 zuwa N699.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da muka sani game da daukar sababbin 'yan sanda 50,000 da za a yi a Najeriya

Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana cewa sabon farashin ya fara aiki ne daga 11, Disamba, 2025, kuma shi ne karo na 20 da matatar Dangote ke sauke farashin fetur a bana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com