Bayan Dawo da Lita N699, Dangote Ya Sa Ranar Fara Aikin Sabon Farashin Fetur

Bayan Dawo da Lita N699, Dangote Ya Sa Ranar Fara Aikin Sabon Farashin Fetur

  • Alhaji Aliko Ɗangote ya sanar cewa sabon farashin fetur zai fara aiki a wasu gidajen mai bayan rage kudin litar mai a Najeriya
  • Kamfanin ya sake jaddada kudurin sa na sauƙaƙa wa jama’a farashin man fetur musamman a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara
  • A gefe guda, Ɗangote ya nuna damuwa kan yadda ake bayar da lasisi a bangaren mai, yana mai cewa hakan na iya shafar farashi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana cewa gidajen mai na MRS da sauran gidajen da ke sayen fetur daga matatar Dangote za su fara sayar da litar fetur a kan N739 daga ranar Talata, 16 ga Disamban 2025 a jihar Lagos.

Ɗangote ya fadi hakan ne a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai, inda ya tunatar da jama’a cewa tuni kamfanin ya rage farashin fetur daga N828 zuwa N699.

Kara karanta wannan

Lamari ya munana: An hallaka matashi bayan zargin daɓawa mahaifiyarsa wuƙa a Niger

Alhaji Aliko Dangote
Dan kasuwa, Aliko Dangote da wajen sayar da mai. Hoto: Dangote Industries|Getty Images
Source: Getty Images

Daily Trust ta rahoto cewa ya ce sabon tsarin farashin na daga cikin kokarin da matatar Dangote ke yi na daidaita samar da man fetur a cikin gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe sabon farashin mai zai fara aiki?

Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana cewa sabon farashin ya fara aiki ne daga 11, Disamba, 2025, kuma shi ne karo na 20 da matatar Dangote ke sauke farashin fetur a bana.

A cewarsa, rage farashin da aka yi a wannan karo ya samu karɓuwa sosai, kasancewar ya nuna ragin kudi mai yawa a lokaci guda.

Ɗangote ya kara da cewa matatar Dangote ta kuduri aniyar tabbatar da cewa man fetur bai wuce N740 ba a fadin kasar nan a cikin watan Disamban 2025 da Janairun 2026.

Attajirin ya bayyana cewa sun yi haka ne domin sauƙaƙa wa jama’a wahalhalun rayuwa a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

Kiran Ɗangote ga kungiyar IPMAN

Kara karanta wannan

Farashin fetur zai dawo kasa da N800 bayan matatar Dangote ta tausaya wa 'yan Najeriya

Yayin da yake magana a harabar matatar Dangote, attajirin ya yi kira ga mambobin kungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu ta IPMAN da su rika sayen fetur daga matatarsa.

A cewar rahoton Trust Radio, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa kamfanin zai ci gaba da sayar da fetur ga ‘yan kasuwa a kan N699 kan kowace lita.

Wani sashe na matatar Dangote
Bangaren matatar Dangote da ke jihar Legas. Hoto: Dangote Industries
Source: UGC

A cewarsa, duk wanda zai iya sayen manyan tankoki 10 na fetur, zai samu damar saye kai tsaye daga matatar Dangote, lamarin da zai taimaka wajen yaduwar sabon farashin a kasuwa.

Dangote ya soki NMDPRA da batun lasisi

A wani bangare na jawabinsa, Ɗangote ya soki hukumar kula da harkokin mai ta kasa, NMDPRA, kan abin da ya kira bayar da lasisi ba tare da tsari ba.

Ya ce hukumar na bayar da lasisi a tsakiyar wata, inda ta shirya fitar da lasisin shigo da mai har lita biliyan 7.5 a zangon farko na shekarar 2026.

Sai dai Ɗangote ya jaddada cewa duk da haka, matatar shi na da isasshen ƙarfin samar da man fetur domin biyan bukatun cikin gida.

Kara karanta wannan

Mansur Sokoto ya shawarci Dangote kan sarrafa dukiyar da ya yi sadaka da ita

Mansur Sokoto ya shawarci Dangote

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Mansur Ibrahim Sokoto ya yi kira ga Alhaji Aliko Dangote game da wata wasiyya da ya yi.

A makon da ya wuce Dangote ya ce ya yi wasiyya da sadakar kashi 25 na dukiyar da ya tara domin ayyukan gidauniyarsa.

Farfesa Mansur Sokoto ya bukaci a bi matakan da suka dace domin tabbatar da cewa Wakafin da Dangote ya yi karko.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng