Za a Yi Danasha: Gwamna Zai ba Ma’aikata Kyautar N150,000 na Kirsimeti
- Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya amince da ba ma'aikata kyautar makudan kudi domin su yi bikin Kirsimeti
- Nwifuru ya amince da biyan ₦150,000 a matsayin alawus din Kirsimeti ga dukkan ma’aikatan gwamnati a jihar
- Gwamnan ya ce ba zai tsoma baki a zaben kananan hukumomi ba, yana jaddada cewa dole ne zabin jama’a ya yi rinjaye
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abakaliki, Ebonyi - Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Ogbonna Nwifuru, ya amince da biyan N150,000 ga ma'aikata.
Gwamna ya amince da kudin ne a matsayin alawus din Kirsimeti ga dukkan ma’aikatan gwamnati a jihar.

Source: Facebook
Kirsimeti: Gwamna zai ba ma'aikata kyautar kudi
Nwifuru ya sanar da hakan ne yayin wani taron ibada da aka gudanar a Cocin Fadar Gwamnati da ke Abakaliki, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki ya yi daidai da kudurin gwamnatinsa na inganta walwalar ma’aikata, duk da karancin kudaden shiga da jihar ke fuskanta a cikin shekarar da ta gabata.
Da yake magana kan zaben kananan hukumomi mai zuwa a jihar, gwamnan ya ce bai tsayar da wani dan takara ba, kuma zai tabbatar da cewa an samar da filin takara daidai ga dukkan masu neman mukamai.
Gwamnan ya kuma sake jaddada umarninsa ga dukkan mukarraban siyasa da ke da niyyar tsayawa takara a zaben kananan hukumomi da su yi murabus daga mukamansu, kamar yadda dokar zabe ta tanada.
A cewarsa:
“A gare ni, dole ne ra’ayin jama’a ya yi nasara. Jama’a su ne za su zabi wakilansu ba tare da katsalandan daga kowa ba.
“Ba aikina ba ne na zabi shugabannin kananan hukumomi. Duk wanda ke rike da mukami kuma yake son tsayawa takara dole ne ya yi murabus, kamar yadda doka ta tanada.”

Source: Facebook
Gwamna ya yi alfahari da ayyukansa
Har ila yau, Gwamna Nwifuru ya karyata jita-jitar da ke yawo game da tsaikon aikin gadar Vincent Agwu Nwankwo (VANCO), yana bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan ayyukan more rayuwa na gwamnatinsa.
A cewarsa:
“Ba za ka samu wata jiha a Najeriya a halin yanzu da ke gina gadar sama irin wannan ba."
Ya ce idan aka kammala gadar, za ta canza fasalin birnin Abakaliki tare da kara masa kyan gani da saukaka zirga-zirga, cewar Vanguard.
Legit Hausa ta tattauna da ma'aikaci
Wani ma'akaci a jihar Gombe, Abdulkadir Muhammad Umar ya ce su kam ba su taba ganin haka ba a gwamnatin nan.
Umar ya ce ko a sallah da azumi har ma Kirsimeti babu wani kyauta da suka taba shaidawa a matsayinsu na ma'aikata.
Ya shawarci gwamnati da ta rika duba irin wadannan lokuta domin taimakawa ma'aikata saboda rage musu radadi.
Gwamna ya musanta rashin lafiya a ketare
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya musanta rahoton da ke nuna cewa an kwantar da shi a asibiti a kasar waje.
Nwifuru, wanda bai jima da dawowa Najeriya daga wata ziyarar aiki da ya kai kasashen ketare ba, ya ce yana cikin koshin lafiya.
Ya kuma gargadi masu yada irin wadannan karairayi marasa tushe, inda ya bukaci su shiga taitayinau tun kafin su kai shi bango.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

