An Kashe Mace Mai Juna Biyu da Jariri Ɗan Wata 18 a Kano, Jama'a Sun Firgita

An Kashe Mace Mai Juna Biyu da Jariri Ɗan Wata 18 a Kano, Jama'a Sun Firgita

  • Wasu da ba a san ko su waye ba sun shiga har gida, sun kashe wata mai juna biyu da ɗanta dan watanni 18 a Sheka Sabuwar Gandu
  • Mijin matar ne ya gano gawarwakin iyalansa bayan ya dawo daga aiki ya tarar an kulle gida daga waje cikin yanayi mai ban tsoro
  • Shugaban al’umma ya koka kan rashin jami’an tsaro duk da gina ofishin ‘yan sanda, yayin da 'yan sandan Kano suka fara bincike

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano – Al’ummar unguwar Sheka Sabuwar Gandu da ke cikin birnin Kano sun shiga mummunan firgici bayan wasu da ba a san ko su waye ba suka shiga wani gida tare da kashe wata mata mai juna biyu da ɗanta dan watanni 18.

Rahotanni sun ce an gano lamarin ne da misalin karfe 8:00 na daren ranar Asabar, lokacin da mijin matar ya dawo daga wurin aiki ya tarar an kulle gidansa daga waje.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Ana zargin wasu sun shiga gida sun kashe mata da danta sun kona gawar.
Taswirar jihar Kano, inda ake zargin an kashe mata da danta. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kashe mata da danta a Kano

Bisa bayanai, mutumin, wanda aka boye sunansa saboda dalilan tsaro, ya shiga damuwa bayan ya lura da yanayin da bai saba gani ba, inda ya fara tambayar makwabta abin da ke faruwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makwabta sun shaida masa cewa ba su ga matarsa ta fita daga gidan ba a tsawon wannan ranar, lamarin da ya sa ya fasa kofa domin shiga ciki.

An ce da ya shiga gidan ne, sai ya tarar da gawarwakin matarsa da ɗansa kwance babu rai, inda wasu rahotanni suka nuna cewa an kashe su ne tare da kona su.

Rashin tsaro a Sheka Sabuwar Gandu Kano

Bayan faruwar lamarin, mazauna yankin sun sanar da jami’an tsaro, yayin da jama’a suka taru a kofar gidan mutumin cikin alhini da kaduwa.

Shugaban al’ummar yankin, Ahmad Sani, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar Punch, yana mai cewa kisan ya jefa al’umma cikin firgici da tashin hankali.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami ya fadi 'gaskiyar dalilin' da ya sa EFCC ke ci gaba da tsare shi

Ahmad Sani ya nuna damuwa kan rashin isasshen tsaro a yankin, duk da cewa al’ummar yankin sun hada kai sun gina ofishin ‘yan sanda tun da dadewa.

'Yan sandan Kano sun ce sun fara gudanar da bincike
Kakakin rundunar 'yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun fara bincike. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kano: 'Yan sanda sun fara bincike

Shugaban al'ummar ya ce:

“Tun da dadewa al’umma suka gina ofishin ‘yan sanda, amma har yanzu ba a turo jami’an da za su yi aiki a wurin ba.”

Ya roki Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Ibrahim Bakori, da ya dauki matakin gaggawa ta hanyar tura jami’ai zuwa ofishin domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a da hana sake aukuwar irin wannan hari.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, CSP Abdullahi Haruna, a ranar Lahadi, ya ce rundunar na binciken lamarin domin gano gaskiyar abin da ya faru.

'Yan bindiga sun sace mata a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Yan Kwada da ke yankin Faruruwa a karamar hukumar Shanono, jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne a daren Lahadi, inda suka sace mata biyar ciki har da masu shayarwa amma wasu matan sun kubuta.

Kara karanta wannan

Dalibi ya rasa rayuwarsa wajen murna a bikin kammala digiri a jami'a

Shaidu sun ce maharan sun iso kauyen cikin tarin yawa, dauke da miyagun makamai, suna harbe-harbe kafin su shiga gidaje domin yin garkuwa da mutanen.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com