Wani mutum ya kashe mace mai juna biyu da almakashi

Wani mutum ya kashe mace mai juna biyu da almakashi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta damke wani mutum mai suna Hussain Zubairu a kan zarginsa da take da kashe makwabciyarsa mai juna biyu. Ya kashe Bose Muhammed ne a kan yar rashin jituwar da ta hada shi da ita.

An gano cewa Zubairu ya soka wa matar mai juna biyu almakashi ne a ciki a yankin Idogido da ke karamar hukumar Okene ta jihar a ranar Litinin.

Wani ganau ba jiya ba ya ce wacce ta rasun an hanzarta kai ta asibiti ne da ke yankin, amma sai da ta rasu saboda jinin da ta zubar mai yawa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Muhammed da kawarta na zaune suna tattaunawa ne a kan wata wayar hannu da ta bace a lokacin da wanda ya kasheta din ya saka baki. Wanda ake zargin an gano cewa ya fusata ne wanda hakan yasa ya soka mata wuka.

“A wannan ranar kuwa wacce ta rasun tana tattaunawa ne da kawarta yayin da wanda ake zargin ya shiga. Ta sanar da shi cewa ya daina shiga harkar da ba tashi ba amma sai hakan ya fusata shi. Ya ciro almakashi daga wandonsa sannan ya soka mata a ciki tare da tserewa.” Ya ce.

Wani mutum ya kashe mace mai juna biyu da almakashi

Wani mutum ya kashe mace mai juna biyu da almakashi
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ta barke a Kano a kan batanci ga Annabi Muhammad

“Matar ta rasa jini mai tarin yawa kuma an sanar da mutuwarta ne bayan da aka mika ta asibiti. Tana da juna biyu amma ba tare da mijinta take zama ba.” Majiyar ta kara da cewa.

Zubairu mai shekaru 30 ya shiga hannun ‘yan sanda ne bayan da aka birne mai juna biyun kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi din, William Ayah ne ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce a halin yanzu an mayar da lamarin hannun sashi na musamman na binciken manyan laifuka. Ana kammalawa kuwa za a mika wanda ake zargin gaban kotu.

‘Wanda ake zargin da wacce ta mutun makwabtan juna ne. Sun samu rashin jituwa ne. Wata kawarta ta rasa wayarta ta hannu amma daga baya ta ganta. Suna tattauna zancen ne da mamaciyar yayin da rigimar ta barke. A take kuwa ya fitar da almakashi ya soka mata a ciki wanda ya jawo ajalinta,” ya yi bayani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel