‘N150m ba Zai Saya Min Takalmi ba’: Malami Ya Kalubalanci Ministan Tinubu

‘N150m ba Zai Saya Min Takalmi ba’: Malami Ya Kalubalanci Ministan Tinubu

  • Fasto Elijah Ayodele ya ce Naira miliyan 150 ba za su iya sayen takalmin da yake sawa ba, yana karyata zargin karɓar kuɗin minista
  • Limamin ya ce Ministan makamashi, Bayo Adelabu, na jin zafi ne saboda ya fahimci zai sake faduwa a yunƙurinsa na zama gwamna
  • Ayodele ya musanta zargin damfara, yana cewa Adelabu ne ya zo wajensa cikin tsananin neman taimako domin cimma burin siyasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele, ya mayar da martani ga minista kan zargin shirin damfararsa.

Ayodele ya soki ministan makamashi, Bayo Adelabu wanda ya ce malamin na neman ya karbi kdadensa domin neman takara.

Fasto ya caccaki ministan makamashi
Fasto Elijah Ayodele da minista, Bayo Adelabu. Hoto: Primate Elijah Ayodele, Bayo Adelabu.
Source: Facebook

Fasto ya ce ya fi karfn N150m

Ayodele ya fadi haka ne yayin taron ibada a cocinsa da ke Oke Afa, Jihar Legas, a ranar Lahadi 14 ga watan Disambar 2025, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

'Yana kan daidai': Gumi ya goyi bayan Matawalle, ya fadi tasirinsa a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto ya ce Naira miliyan 150 ba su kai darajar takalmin da yake sawa ba, yana mai sukar ministan kan bata masa suna.

Ya ce Adelabu na cikin damuwa ne domin ya fahimci cewa zai sake faduwa a yunƙurinsa na zama gwamnan Jihar Oyo.

Limamin yana martani ne kan rahoton da ya bayyana cewa Adelabu ya kai karar Ayodele gaban DSS, inda ya zarge shi da yunƙurin damfara da neman Naira miliyan 150 a matsayin na “addu’ar” domin ya zama gwamna.

Adelabu, wanda ya taba yin takarar gwamnan Oyo sau biyu, ya riga ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a 2027.

Fasto ya musanta neman N150m daga ministan Tinubu
Malamin addinin Kirista, Elijah Ayodele. Hoto: Primate Elijah Ayodele.
Source: Twitter

'Abin da Adelabu ya ce mini' - Ayodele

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar tun a ranar Asabar, Fasto Ayodele ya musanta zargin, yana cewa Adelabu ne ya zo wajensa cikin matsanancin hali.

Ya ce ministan ya shaida masa cewa a shirye yake ya yi komai domin ya zama gwamnan Oyo.

Kara karanta wannan

'Ko $1bn aka ba ni, ba zan shiga sabgar ba': Malamin addini ya tsinewa siyasa

Da yake jawabi a cocin, Ayodele ya bayyana Adelabu a matsayin “yaro” da bai san abin da yake fada ba.

Ya ce:

“Naira miliyan 150 za su iya sayen takalmina ne? Motata fa, za su iya sayenta?”

Ya kara da cewa ba ya yin hasashe da ubangiji ke sanar da shi domin burge mutane ko neman su zo wajensa.

Ayodele ya jaddada cewa idan har ya karbi kudi, zai fito fili ya fada, amma bai taba karbar ko sisi ba, kuma bai taba gayyatar Adelabu zuwa wajensa ba.

“Ba na yin hasashe domin a zo a bincike ni. Ka karba ko ka bar shi, ya san ya sha kaye, shi ya sa yake jin zafi.”

Fasto Ayodele ya magantu kan zaben 2025

Kun ji cewa malamin kirista, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya gargaɗi Bola Tinubu ya tashi tsaye domin daƙile rikicin siyasa.

Malamin ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da yake hasashen abin da zai iya faruwa a zaben shugaban ƙasa mai zuwa a 2027.

Kara karanta wannan

"A bayyane yake": An hango abin da Tinubu zai yi wa Shettima a zaben 2027

A wani faifan bidiyo, Ayodele ya ce matukar Tinubu da muƙarrabansa suka gaza yin abin da ya dace, za su fuskanci ƙalubale a zaɓe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.