An Yi Babban Rashi a Sokoto, Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda Ya Bar Duniya

An Yi Babban Rashi a Sokoto, Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda Ya Bar Duniya

  • Rundunar ‘yan sandan Sokoto ta sanar da rasuwar mataimakin kwamishina mai kula da ayyuka bayan jinya mai tsawo
  • Kwamishinan ‘yan sanda Ahmed Musa ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen jami’i mai kishin kasa
  • Rundunar ta jajanta wa iyalai da abokan aiki, tana addu’ar Allah SWT ya gafarta masa, ya ba iyalansa hakuri da juriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta sanar da rasuwar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka, DCP Kabir Abdu.

Rundunar ta jajantawa iyalan marigayin wanda ya bar duniya bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Mataimakin kwamishinan yan sanda ya rasu a Sokoto
Marigayi Kabir Audu da kwamishinan yan sanda a Sokoto, Ahmed Musa. Hoto: Sokoto State Police Command.
Source: Facebook

An sanar da rasuwar babban dan sanda

Sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Lahadi 14 ga watan Disambar 2025 ta bayyana yadda DCP Kabir Abdu ya rasu, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar mataimakinsa, Gwamna Diri ya fadi gaskiya game da alakarsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce marigayin ya rasu ne yayin da yake karbar magani a asibitin koyarwa na Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.

Rahoton ya bayyana cewa an kwantar da marigayin a asibitin tun ranar 12 ga Disamba, 2025, kafin rasuwarsa bayan jinya mai tsawo.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ahmed Musa, ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen jami’i mai ladabi, kwarewa da sadaukarwa ga aiki.

CP Musa ya ce gudummawar DCP Kabir Abdu ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar Sokoto.

A cewarsa:

“DCP Kabir Abdu jami’i ne na musamman, wanda aikinsa ya bar gagarumar alama a harkar tsaro da kare rayukan al’umma.”
An yi rashin mataimakin Kwamishinan yan sanda a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Sakon ta'aziyya daga kwamishinan yan sanda

Kwamishinan ya mika sakon ta’aziyya ga iyalai, abokai da abokan aikin marigayin a madadin dukkan jami’ai da rundunar.

Ya kuma yi addu’ar Allah SWT ya jikansa da rahama, ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.

Kara karanta wannan

Jita jita ta ƙare: Mataimakin gwamna da aka garzaya da shi asibiti ya mutu

Rundunar ta ce za ta ci gaba da girmama gudummawar da marigayin ya bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da ingantaccen aikin ‘yan sanda.

Rahotanni sun nuna cewa DCP Kabir Abdu gogaggen jami’i ne da ya shafe shekaru yana aiki a rundunar ‘yan sanda a sassa daban-daban na kasa.

Kafin rasuwarsa, yana rike da mukamin DCP mai kula da ayyuka a Sokoto, inda yake jagorantar dabarun tsaro da yakar laifuka.

Ayyukansa sun zo ne a lokacin da ake kara kaimi wajen yaki da ‘yan bindiga, satar mutane da sauran manyan laifuka a Arewa maso Yamma.

Abokan aikinsa sun bayyana shi a matsayin jami’i mai tsauri kan aiki, amma mai bin ka’ida da hada kai da sauran hukumomin tsaro.

Dan kwamishinan yan sanda ya mutu a Abuja

Kun ba ku labarin cewa dan kwamishinan ƴan sandan Abuja, Tunde Olatunji Disu ya mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi.

Wannan rashi ya jefa rundunar ƴan sanda cikin jimami musamman saboda a ranar CP Disu ya je ta'aziyya gidan DPO na ofishin Ushafa wanda shi ma ɗansa ya rasu.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume da Oshiomhole sun gwabza a majalisa kan tantance Omokri

Kwamishinan ya yi ta'aziyya ga iyalan DPO bisa wannan rashi tare da fatan samun rahama ga wanda ya mutu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.