'Yan Kwadago Za Su Gudanar da Zanga Zanga a Jihohi 36, Sun Aika Sako ga Gwamnoni
- Shugaban NLC Joe Ajaero ya ce ba gudu ba ja da baya, game da zanga-zangar kasa baki daya da 'yan kwadago za su yi a mako mai zuwa
- Joe Ajaero ya ce matsalar tsaro ta shafi kowa a Najeriya, ta lalata tattalin arziki tare da korar masu zuba jari na cikin gida da waje
- NLC ta ce sace-sace da kisan gilla sun addabi ma’aikata, don haka ta bukaci gwamnati ta dauki kwararan matakai don kawo karshen matsalar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Shugaban ƙungiyar kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero, ya bayyana cewa ba gudu ba ja da baya kan zanga-zangar da NLC ke shirin yi a fadin ƙasar a ranar 17 ga Disamba, 2025.
Ajaero ya bayyana haka ne jim kadan bayan wata ziyarar girmamawa da ya kai wa shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa 19 kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, a Abuja.

Source: Facebook
Dalilin zanga-zangar NLC
A cewar Joe Ajaero, 'yan kwadago za su gudanar da zanga-zangar domin tilasta wa gwamnati daukar kwararan matakai kan matsalar tsaro da ke addabar ƙasar, in ji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban 'yan kwadago ya kuma jaddada cewa yanzu matsalar tsaro na shafar kowane ɗan Najeriya, ba tare da la’akari da matsayi, kabila ko addini ba.
Ajaero ya ce rashin tsaro na lalata tattalin arzikin ƙasa tare da raunana damar Najeriya na jawo hankalin masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje.
Ya ce:
“Zanga-zangar da muke shirin yi na da nufin jawo hankalin gwamnati kan yadda rashin tsaro ke shafar masu zuba jari da ma’aikata, wadanda ake sacewa kullum, wasu ma ana kashe su.”
Matsalar tsaro da bukatar magance ta
Ya buga misali da harin da 'yan bindiga suka kai makarantar Kebbi, inda ya ce wanda aka kashe malami ne, yayin da cikin yaran da aka sace har da ‘ya’yan ma’aikata.
Ajaero ya ce NLC na bukatar gwamnati ta gano masu aikata laifuffukan tare da kawo karshen wannan masifa gaba daya.
Ya ce zanga-zangar kuma za ta tabbatar wa hukumomi cewa jama’a na goyon bayan duk wani mataki na gaskiya da za su dauka domin shawo kan matsalar tsaro.
“Gwamnati ta sani cewa muna karfafa mata gwiwa ta yi abin da ya dace, domin ‘yan Najeriya sun fito sun yi magana da babbar murya, 'dole a kawo karshen matsalar tsaro'," in ji Ajaero.
Shugaban NLC ya jaddada bukatar daukar mataki tare, yana mai cewa sace mutane don neman kudin fansa na lalata darajar kasa da zaman lafiyar al’umma.

Source: Facebook
Matsalar tsaro ta addabi ma'aikatan Najeriya
Ya ce ma’aikatan Najeriya na shan wahala matuka, domin wadanda aka sace sau da yawa ba su da kudin fansa, sai su rika karbar aro ko roka daga jama'a domin tsira da rayuwarsu, in ji rahoton Punch.
A cewarsa:
“Ya zama wajibi ma’aikata su shiga wannan kira na kawo karshen rashin tsaro, sai dai idan gwamnati na shirin ba mu alawus din tsaro domin biyan kudin fansa.
“Ba mu da bindiga ko adda da za mu tunkari ‘yan ta’adda; zanga-zanga ita ce muryarmu daya tilo ga ‘yan Najeriya da kuma duniya"
- Joe Ajaero.
Ajaero ya kuma bukaci gwamnati da ta fadada shirye-shiryen tallafin jama’a, yana cewa mafi karancin albashi kadai ba zai wadatar wajen rage wahalhalu ba, sai an kara wasu tsare-tsare na tallafi.
Tsohon ministan kwadago ya koma PDP
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon ministan kwadago Joel Ikenya ya sanar da ficewarsa daga APC zuwa PDP, bayan tuntubar masu ruwa da tsaki.
Joel Ikenya, wanda ya taba rike mukamai daga majalisar jiha zuwa majalisar tarayya, ya ce PDP ce jam’iyyar da ta gina siyasarsa tun da farko.
Sauya shekar Ikenya ta zo ne a daidai lokacin da Gwamna Agbu Kefas ke shirin komawa APC, lamarin da ya tayar da muhawara a siyasar Taraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


