Matawalle Ya Tabbatar da ba da Kudin Dusa yayin Musanta Zargin Ta’addanci
- Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya sake fitowa tare da kare kansa game da zargin alaka da yan ta'adda
- Matawalle ya ce zargi ba ya zama gaskiya sai kotu ta tabbatar, yana gargadin masu neman bata masa suna ba tare da hujja ba
- Ya kare ba da dusa ga yan bindiga bayan sulhu, yana cewa kare rayuwar mutum guda ya fi muhimmanci fiye da wata dusa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Karamin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle ya yi karin haske kan zargin alaka da yan ta'adda.
Matawalle wanda tsohon gwamna ne a Zamfara ya kare kansa game da zarge-zargen inda ya kalubalanci mutane.

Source: Twitter
Matawalle ya kare kansa kan zargin ta'addanci
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da DCL Hausa ta wallafa a Facebook yayin hira da tsohon gwamna.

Kara karanta wannan
Bello Turji ya fadi gaskiya kan alakanta shi da Matawalle, ya kira sunaye a bidiyo
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, Matawalle ya ce duk wani zargi da bai tabbata ba, bai zama zargi sai an je kotu an yi shari'a kafin sanin gaskiya.
Ya bukaci duk mai zarginsa kan alaka da ta'addanci ya garzaya kotu da hujjoji domin gano gaskiyar lamarin.
Ya ce:
"Du wani zargi da tabbatar da shi ba, ba gaskiya ba ne, duk mai zargi na ya je kotu, idan aka tabbatar abin da ya fada a kaina ba gaskiya ba ne, to duk abin da na nema na bata suna sai ya biya.
"Kamar yadda na fada, yawancinsu suna hannu yadda za a kifar da gwamnati, kuma muke binciken, ina cikin masu binciken."

Source: Original
Zargin da Matawalle ke yi masu sukarsa
Matawalle ya kuma zargi masu alakanta shi da ta'addanci da cewa suna kokari ne kawai sai dole sun ga ya bar ma'aikatar tsaro.
Ya kara da cewa:
"Saboda haka duk kokarin da za su yi, ya za a yi Bello Matawalle ya bar ma'aikatar tsaro za su yi, ko na bar ma'aikatar tsaro, binciken zai ci gaba."
Kan batun ba yan bindiga dusa, Matawalle ya ce tabbas hakan ya faru amma ya ba su ne bayan tabbatar da yin sulhu da su yan ta'adda.
Ya kare matakin ba da dusar inda ya ce ko duka dusar kasar za a ba su yafi kisan mutum guda daya.
"Misali, idan na dauki dusa na ba da, na dauki dusa na ba da a matsayin suna yan ta'adda ko kuma don an yi zaman sulhu aka ba su.
"Sannan kuma, maganar dusa, da a dauki dusa a ba su da a kashe mutum guda, gwara duk dusar kasar ka ba da ta baki daya a kan a kashe rayuwar mutum daya."
Matawalle ya tona asirin masu bata sunansa
Kun ji cewa Bello Matawalle ya ce munanan kalamai da ake furtawa kansa siyasa ce kawai, saboda ana son bata masa suna.
Karamin ministan tsaro ya bayyana cewa shi ma ya gaji da matsalar ’yan bindiga a Zamfara, kuma gwamnatinsa ta rage lamarin sosai.
Matawalle ya ce wasu manyan 'yan siyasa ne ke daukar nauyin wadanda ke aibata shi, kuma lokaci ya yi da zai fara mayar da matarni.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
