Gwamnatin Bauchi Ta Gwangwaje Likitoci da Sauran Ma'aikatan Lafiya a Fadin Jihar

Gwamnatin Bauchi Ta Gwangwaje Likitoci da Sauran Ma'aikatan Lafiya a Fadin Jihar

  • Gwamnatin jihar Bauchi ta waiwayi likitoci da ma'aikatan lafiya domin kara zaburar da su kan ayyukan da suke gudanarwa
  • Likitoci da ma'aikatan lafiya a jihar Bauchi za su dara bayan gwamnati ta amince musu da karin albashi mai gwabi
  • Hakazalika ta fito da tsarin da zai ba su damar samun basussukan sayen gida da mota domin inganta jin dadin rayuwarsu

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta amince da yi wa likitoci da ma'aikatan lafiya karin albashi.

Gwamnatin Bauchi ta amince da karin albashi na kaso 100 ga likitoci da ma’aikatan lafiya a faɗin jihar.

Gwamnatin Bauchi ta yi wa likitoci karin albashi
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Muhammad Sani Dambam, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar, 13 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Bago ya goyi bayan wa'adi 1 a mulki, ya fadi amfaninsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Bauchi ta gatanta likitoci

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Bauchi.

A cewar Muhammad Sani Dambam, amincewar ta biyo bayan la’akari da shawarwarin kwamitin musamman da aka kafa.

Kwamishinan ya bayyana cewa sakamakon hakan shi ne kara tsarin albashi na yanzu gaba ɗaya da kaso 100.

Muhammad Sani Dambam ya kara da cewa an yanke wannan shawara ne domin rike kwararrun ma’aikatan lafiya tare da inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.

Ya ce a matsayin wani ɓangare na wannan tsarin, gwamnati ta amince da alawus-alawus na musamman, ciki har da alawus na aiki a wajen birane, domin karfafa likitoci da ma’aikatan lafiya su karɓi aiki kuma su ci gaba da zama a wuraren da ba birane ba.

Hakazalika, ya kuma bayyana cewa ma’aikatan lafiya karkashin hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihasu ma za su amfana da waɗannan alawus-alawus na musamman.

Kara karanta wannan

Gwamna Ahmad Aliyu zai kashe Naira biliyan 8.4 a sake gina kasuwa

Kwamishinan ya ce hakan zai kawo karshen shekaru da dama na nuna banbancin jin daɗin aiki tsakaninsu da sauran ma’aikatan lafiya.

Likitoci sun samu karin albashi a Bauchi
Gwamna Bala Mohammed na jawabi a wajen taro Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Za a kara girma ga ma'aikata

Kwamishinan ya ce majalisar ta kuma amince da warware batun ragowar karin girma na ma’aikatan lafiya, inda fiye da ma’aikata 2,000 ake sa ran za su amfana da wannan mataki.

Ya kara da cewa domin kara karfafa gwiwar likitoci da ma’aikatan lafiya, gwamnati ta amince da ba su rancen mota da na gidaje, domin rage musu nauyin kuɗi da kuma inganta rayuwarsu.

Makinde ya amince da albashin watan 13

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da biyan ma'aikata albashin wata na 13 na shekarar 2025.

Gwamna Makinde ya tabbatar da cewa biyan albashin wata na 13 ya kasance dabi’arsa tun bayan shiga ofis a shekarar 2019.

Hakazalika, Gwamna Makinde ya ba da tabbacin cewa matsalar da ta sa likitocin jami'ar LAUTECH suka shiga yajin aiki za ta warware nan gaba kadan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng