Bello Turji Ya Fadi Gaskiya kan Alakanta Shi da Matawalle, Ya Kira Sunaye a Bidiyo

Bello Turji Ya Fadi Gaskiya kan Alakanta Shi da Matawalle, Ya Kira Sunaye a Bidiyo

  • Dan bindiga, Bello Turji ya fito da sabon bidiyo yana karyata zargin cewa Bello Matawalle ya ba ’yan bindiga kudi
  • Turji ya mayar da martani ne ga tsohon hadimin Matawalle, Musa Kamarawa, yana zarginsa da ƙarya
  • Duk da bayyana kiyayya ga Matawalle, Turji ya ce ba zai yarda a yi amfani da sunansa wajen bata suna ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Lamari ya fara girma tun bayan zargin karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da alaka da yan ta'adda.

Tantirin dan bindiga, Bello Turji ya fito da wani sabon bidiyo inda ya ke karyata zargin cewa Matawalle ya ba su miliyoyi.

Bello Turji ya soki alakanta shi da Matawalle a Zamfara
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da Bello Turji. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Hakan na cikin wani sabon bidiyo da shafin Zagazola Makama ya wallafa a shafin X a yau Asabar 13 ga watan Disambar 2025.

Kara karanta wannan

'Ko $1bn aka ba ni, ba zan shiga sabgar ba': Malamin addini ya tsinewa siyasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon hadimin Matawalle ya fasa kwai

Hakan ya biyo bayan zargin da tsohon hadimin Matawalle ya yi cewa tabbas akwai alaka tsakanin tsohon mai gidansa da yan ta'adda.

Musa Kamarawa ya bayyana haka ne a wani bidiyo da Legit Hausa ta samu inda yake tone-toone.

Daga bisani, Kamarawa ya ce a shirye yake ya ba da bayanai masu inganci kan zargin da ake yi inda ya tabbatar gaskiya ne.

Martanin Bello Turji kan zarginsa da Matawalle

Bello Turji ya fitar da sabon bidiyon ne domin yin raddi ga Musa Kamarawa game da maganganun da ya yi.

Ya ce Kamarawa ya tabbata dan ta'adda saboda sun yi sulhu tare da gwamnatin Zamfara inda ya ce maganganunsa akwai karairayi.

Turji ya ce:

"Na ji Matawalle ya maka Murtala Asada a kotu, wani zauna gari banza Musa Kamarawa ya zo yana cewa yana wata shaida.
"Musa Kamarawa ashe ka tabbatar kai dan ta'adda ne, mun yarda gwamnatin Zamfara ta saka ka a yi sulhu tare da mu.

Kara karanta wannan

Halin da Bello Turji ke ciki bayan hallaka na kusa da shi a Sokoto, ya zargi wasu mayaka

"Amma maganar da kake fadi karya ne wai mun zo gidan gwamnatin jihar Zamfara, an ba mu Naira miliyan 30, ni wallahi ba a taba ban ba."
Zargin Matawalle kan alaka da ta'addanci ya jawo martanin Turji
Karamin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Original

'Matawalle ya sanya ni a kunci' - Turji

Bello Turji ya ce ba wai kare Bello Matawalle yake yi ba, hasalima, babu wanda ya tsana kamarsa saboda a mulkinsa ya cutar da shi.

Ya zargi Kamarawa da rike miliyoyin da ya ce an ba su tun da shi dai bai karbi wadannan kudaden ba.

"Ni babu wanda na tsana kamar Matawalle saboda a mulkinsa sai da muka birne mutum 70 da aka tura musu bama-bamai, kuma a zamaninsa aka kama babana aka kai shi gidan yari bai ci bai sha ba.
"Wace kauna zan yi wa Matawalle, amma abin da ka fada, ni ba a amfani da sunana a batawa wani suna, a nan ka tabbata munafukin Allah, kenan kai ka rike miliyan 30 din.
"Mun je mun ga Matawalle amma bai ban miliyan uku ba wallahi tallahi, kuma maganar dusa, kwamitinku ne na makiyaya kuka saya bayan an yi sulhu, Musa ka ji tsoron Allah."

Kara karanta wannan

Gwamna Adeleke zai cigaba da cire kunya yana tika rawa a bainar jama'a

- Bello Turji

Turji ya dugunzuma bayan harin sojoji

An ji cewa majiyoyi sun bayyana cewa hatsabibin dan ta’adda, Bello Turji ya shiga tashin hankali a Sokoto bayan yi masa ta'asa.

Hakan na zuwa ne bayan sojojin Najeriya sun kashe kwamandansa, Kallamu Buzu a kwanton-bauna da aka yi.

Rahotanni sun nuna cewa Turji ya zargi wani kwamandansa saboda kuskuren da ya jawo mutuwar Buzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.