Bayan Mutuwar Mataimakinsa, Gwamna Diri Ya Fadi Gaskiya game da Alakarsu

Bayan Mutuwar Mataimakinsa, Gwamna Diri Ya Fadi Gaskiya game da Alakarsu

  • Gwamnan Bayelsa, Douye Diri, ya shiga wani irin yanayi yayin jimamin rasuwar mataimakinsa Lawrence Ewhrudjakpo
  • Diri ya bayyana yadda alakarsu ke tafiya kafin rasuwar marigayin yana cewa mutuwarsa babbar rashi ne
  • Gwamnatin Bayelsa ta sha alwashin tallafa wa iyalan marigayin, ta ɗauki nauyin karatun ’ya’yansa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yenagoa, Bayelsa - Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana alhini da jimami kan rasuwar mataimakinsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.

An tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a ranar Alhamis 11 ga watan Disambar 2025 yana da shekaru 60 a duniya.

Gwamna Diri ya tuna alakarsa da marigayi mataimakinsa
Gwamna Douye Diri na Bayelsa da marigayi mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo. Hoto: Douye Diri.
Source: Facebook

Gwamna ya kadu bayan mutuwar mataimakinsa

Gwamnan ya ce mutuwar marigayin ta girgiza shi matuƙa, tare da barin gibi mai girma a harkokin mulki da rayuwar al’ummar jihar, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Diri ya jagoranci tawaga mai kunshe da ’yan majalisar dokoki da manyan jami’an gwamnati zuwa ziyarar ta’aziyya a gidan marigayin da ke gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Gwamnati ta tabbatar da rasuwar mataimakin gwamna bayan ya fito ofis

Diri ya bayyana Ewhrudjakpo a matsayin aboki na ƙwarai, wanda suka yi aiki tare tun daga zamanin tsohon gwamna, Sanata Seriake Dickson.

A cewar Diri, sun shafe shekaru takwas suna aiki tare a gwamnatin da ta gabata, sannan kusan shekaru shida a gwamnatinsa ta yanzu.

Ya ce dangantakarsu ba ta ta’allaka ne a kan ubangida da mataimaki ba, illa ta kasance ta ’yan’uwa da abokai masu girmama juna.

Gwamna Diri ya yaba halayen mataimakinsa

Gwamnan ya ce marigayin mutum ne abin dogaro, mai son aiki da jajircewa, tare da ƙwarewa a fannoni da dama, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ya tuno da rawar da ya taka a matsayin lauya da kuma shugaban kwamitin kula da lafiya matakin farko, yana mai cewa a ranar rasuwarsa ne jihar ta samu lambar yabo kan kiwon lafiya a Abuja.

Diri ya ce mutuwar Ewhrudjakpo ta zo ne a lokacin da jama’a ke yaba masa ƙwarai, yana mai cewa sun yi fatan kammala wa’adin shekaru takwas tare.

Ya bayyana cewa ba ya jin yadda zai yi bikin cikar gwamnatin su shekara shida ba tare da mataimakinsa ba.

Kara karanta wannan

Jita jita ta ƙare: Mataimakin gwamna da aka garzaya da shi asibiti ya mutu

Gwamna Diri ya dauki alkawari ga iyalan mataimakinsa da ya mutu
Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa. Hoto: Diri Douye.
Source: Facebook

Alkawarin Gwamna ga iyalan mataimakinsa

Gwamnan ya tabbatar wa iyalan marigayin cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin karatun ’ya’yansa har zuwa kowane mataki, tare da tabbatar da cewa ma’aikatansa za su ci gaba da kasancewa a cikin tsarin gwamnati.

Haka kuma, gwamnan ya tabbatar da cewa za a yi wa marigayin jana’iza mai alfarma wanda jihar za ta dauki nauyi.

A madadin iyalan marigayin, Dr. Oyovwhi Osusu ya gode wa gwamna da gwamnatin Bayelsa bisa goyon baya da jajircewa da suka nuna, yana cewa sun karɓi wannan rashi a matsayin ƙaddarar Allah.

Tattaunawar Tinubu, Diri bayan komawa APC

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya sauya sheka zuwa jam'iyyyar APC mai mulki a tarayyar Najeriya.

Douye Diri ya koma jam'iyyar APC ne kwanaki kadan bayan ya sanar da ficewarsa daga PDP mai adawa.

Shugaba Bola Tinubu ya kwararo yabo ga gwamnan kan matakin da ya dauka na shigowa jam'iyya mai mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.