Mansur Sokoto Ya Shawarci Dangote kan Sarrafa Dukiyar da Ya Yi Sadaka da Ita

Mansur Sokoto Ya Shawarci Dangote kan Sarrafa Dukiyar da Ya Yi Sadaka da Ita

  • Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana shirin ware kaso ɗaya cikin huɗu na duk arzikin da ya mallaka domin ayyukan raya ƙasa da tallafa wa jama’a
  • Rahoto ya nuna cewa an tsara a gudanar da wannan waƙafi ne ta ƙarƙashin gidauniyar Aliko Dangote, musamman idan ya rasu
  • Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya fadi yadda za a iya tafiyar da waƙafin ya cigaba da gudana lokaci mai tsawo ya kuma amfanar al’umma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Sokoto — Alhaji Aliko Ɗangote ya sanar da wani muhimmin mataki na ware kaso ɗaya cikin huɗu na dukiyarsa domin ayyukan alheri da ci gaban jama’a.

Wannan mataki ya jawo martani da yabo daga masana da masu ruwa da tsaki, inda ake kallonsa a matsayin babban sadaukarwa ga al’umma da makomar ƙasa.

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

Sheikh Mansur Sokoto da Aliko Dangote
Farfesa Mansur Sokoto tare da Aliko Dangote. Hoto: Mansur Ibrahim Sokoto|Dangote Industries
Source: Facebook

Daya daga cikin masu tsokaci kan wannan lamari shi ne Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto, wanda ya bayyana ra’ayinsa a Facebook kan muhimmanci da tasirin waƙafin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya sadaukar da sashen dukiyarsa

A cewar rahoton Punch, Alhaji Aliko Ɗangote ya shirya ware kaso ɗaya cikin huɗu na duk arzikin da ya tara a rayuwarsa domin ayyukan raya ƙasa da taimakon jama’a.

An bayyana cewa za a gudanar da wannan tsari ne ta ƙarƙashin gidauniyar Dangote, wadda ke aiki a fannoni kamar ilimi, lafiya da tallafa wa marasa ƙarfi.

Har ila yau, shirin ya haɗa da ci gaba da aiwatar da wannan waƙafi ko bayan rasuwarsa, domin alherin ya zama mai ɗorewa.

Mansur Sokoto ya yaba wa Dangote

Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ya bayyana cewa wannan mataki abin a yaba ne sosai, yana mai cewa yana daga cikin burinsa ganin manyan mawadatan ƙasa suna barin wani kaso na dukiyarsu domin alheri.

Kara karanta wannan

Ganduje ya hango matsalar da APC za ta iya shiga a Kano kan ayyana dan takara

Ya ce irin wannan sadaukarwa na iya zama hanyar samun lada a lahira tare da barin abin tunawa mai kyau a duniya.

A cewarsa, idan Allah ya so, wannan waƙafi na iya zama abin mai albarka da zai ci gaba da amfani ga jama’a har tsawon shekaru masu yawa.

Darasin da Dangote zai koya a kan wakafi

Farfesa Mansur ya yi nuni da misalin waƙafin Sayyidina Usman bn Affan (RA), wanda ya ce har yanzu ana cin gajiyar sa bayan sama da shekaru 1400.

Ya bayyana cewa a birnin Madina akwai katafaren masaukin Alhazai da ke ɗauke da sunan Sayyidina Usman, wanda ake gudanar da ayyukan alheri da kuɗin waƙafinsa.

A cewarsa, wannan na nuna cewa idan aka tsara waƙafi da kyau, zai iya dorewa tsawon lokaci yana amfani ga al’umma.

Wakafi: Kiran Mansur Sokoto ga Dangote

Farfesa Mansur ya ja hankali cewa nasarar wannan waƙafi na Ɗangote na dogara ne da yadda za a tsara shi da kuma irin mutanen da za su tafiyar da shi.

Ya ce idan aka bar gudanarwar ga masu son nuna alfarma kawai, kuɗin za su iya salwanta ba tare da cimma manufa ba.

Kara karanta wannan

Iyalai za su ɗasa, Shettima ya kaddamar da shirin tallafin N1bn ga ƴan kasuwa

Amma idan aka ba mutane masu kishin ci gaban al’umma, tare da gogewa a juya jari da tanadi, waƙafin na iya zama abin koyi mai ɗorewa.

Farfesa Mansur ya kuma ba da shawara ga Alhaji Aliko Ɗangote da ya nazarci tsarin waƙafin Sheikh Sulaiman Al-Rajhi, wanda ya kai darajar biliyan 60 na Dalar Amurka tun a shekarar 2010.

Sheikh Sulaiman Al-Rajhi da Sarkin Makkah
Sarkin Makkah tare da Sheikh Sulaiman Al-Rajhi da ya yi wakafi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce irin wannan tsari zai taimaka wajen tabbatar da dorewar waƙafin da kuma faɗaɗa tasirinsa ga jama'a masu yawan gaske.

Maganar Dangote game da Arewa

A wani labarin, mun kawo muku cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi kira game da bunkasa tattalin arzikin Arewacin Najeriya.

Attajirin ya koka da cewa rashin wutar lantarki na cikin manyan dalilan da suka sanya kamfanoni da yawa rugujewa a Arewa.

Dangote ya yi kira ga masu hannu da shuni su dage wajen saka kudinsu a harkokin samar da masana'antu a Arewa da Najeriya baki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng