Najeriya Ta Hada Kai da Faransa a Shirin Fara Aiki da Dokar Harajin Tinubu a 2026

Najeriya Ta Hada Kai da Faransa a Shirin Fara Aiki da Dokar Harajin Tinubu a 2026

  • Hukumar tara haraji ta tarayya ta kulla yarjejeniyar fahimtar juna da hukumar haraji ta Faransa domin inganta musayar bayanai da dabarun zamani
  • An ƙaddamar da sabon suna da tambari na harajin bai daya bayan sabuwar dokar haraji ta samu sahalewar shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Rahotanni sun nuna cewa sauye-sauyen da ake na zuwa ne gabanin sauya sunan FIRS zuwa Nigeria Revenue Service daga 1, Janairu, 2026

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar FIRS ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da hukumar haraji ta Faransa domin haɗa kai wajen inganta tsarin tara haraji a ƙasashen biyu.

Shugaban FIRS, Dr Zacch Adedeji, ya ce yarjejeniyar ta nuna aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke ƙara dogaro da fasahar zamani.

Kara karanta wannan

Ganduje na fuskantar barazanar shari'a game da yi wa Hisbah kishiya a Kano

Shugaba hukumar harajin Najeriya da FIRS
Shugaban hukumar FIRS ta Najeriya da jami'in Faransa. Hoto: @FIRSNigeria
Source: Twitter

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da yarjejeniyar ne a cikin wani sako da hukumar FIRS ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne gabanin sauya FIRS zuwa Nigeria Revenue Service kamar yadda sababbin dokokin haraji da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba wa hannu suka tanada.

Yarjejeniyar Najeriya da Faransa kan haraji

Dr Zacch Adedeji ya bayyana cewa yarjejeniyar da aka sanya hannu a ofishin jakadancin Faransa a Abuja za ta buɗe ƙofofi ga musayar ilimi, bayanai da sabbin dabaru tsakanin ƙasashen biyu.

Ya ce:

“Yayin da harkokin kasuwanci ke ƙara zama ba su da iyaka, haɗin kai, musayar bayanan sirri da daidaita tsare-tsare tsakanin hukumominmu zai zama muhimmi sosai.”

Ya ƙara da cewa Faransa za ta amfanar da Najeriya wajen rungumar sababbin fasahohi da hanyoyin magance kalubalen haraji a ƙasar da ke da matasa masu yawa.

An yi sabon tsarin tattara haraji a Najeriya

Kara karanta wannan

Wasu manya a Kano sun ajiye Abba a gefe, sun ce Barau suke so a 2027

A wani bangare, Adedeji ya ƙaddamar da sabon suna da tambarin harajin bai daya wanda yanzu ake kira Joint Revenue Board.

Ya ce sabon tambarin na nuna sabuntawa da sauyi, yana kuma wakiltar aniyar ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tara kuɗin shiga a fadin ƙasa.

Tashar Arise News ta rahoto ya ce:

“Sabon tambarin yana nuna alamar farfaɗowa da sauyi, kuma zai jagoranci ayyukanmu a zamanance.”

Tasirin sauyin haraji ga jihohi da ƙasa

Babban sakataren hukumar, Olusegun Adesokan, ya ce JRB za ta yi aiki da hukumomin jihohi domin haɗa bayanan masu biyan haraji zuwa ma’ajiyar ƙasa.

Ya bayyana cewa za a yi amfani da bayanan NIN wajen samar da lambar shaidar biyan haraji ta ƙasa baki ɗaya.

Bola Tinubu da shugaban Faransa
Tinubu da Macron na Faransa a Paris. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Shugabar haraji ta jihar Kwara, Shade Omoniyi, ta ce ya dace a tabbatar da dakatar da shingayen hanya gaba ɗaya domin rage tsadar kayayyaki.

A nasa bangaren, shugaban haraji na jihar Lagos, Ayodele Subair, ya ce sauye-sauyen haraji na daga cikin manyan gyare-gyaren da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

Wasu dokokin CBN za su fara aiki a 2026

A wani labarin, mun kawo muku cewa Babban bankin Najeriya, CBN ya kawo wasu tsare tsare da suka shafi kudi a bankuna.

Wata sanarwa da bankin ya fitar ta tabbatar da cewa dokokin za su shafi yadda mutum zai cire kudi da ajiye su a asusun shi.

Rahoto ya nuna cewa bankin ya sauya wasu dokoki da suka takaita adadin kudin da mutum zai iya ajiye wa a banki a kowace rana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng