Kwana Ya Kare: Farfesan Ilimi na Farko a Arewacin Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Kwana Ya Kare: Farfesan Ilimi na Farko a Arewacin Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Farfesa Adamu Baikie, wanda shi ne mutum na farko da ya fara taka matsayin Farfesa a fannin ilimi a Arewacin Najeriya, ya rasu
  • Babban dansa, Manjo Muhammad Adamu (mai ritaya) ne ya tabbatar da rasuwar jigo a fannin ilimi a ranar Juma'a a gidansa da ke Zaria
  • Ya ce marigayi Farfesa Adamu Baikie ya cika ne da yammacin yau Juma'a, 12 ga watan Disamba, 2025 kuma an fara shirye-shiryan jana'iza

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zaria, Nigeria - Najeriya ta rasa daya daga cikin dattawan kasa kuma wadanda suka ba da gudummuwa sosai a ci gaban fannin ilimi a kasar nan, Farfesa Adamu Baikie.

Kara karanta wannan

'Dan majalisar Amurka ya koma kasarsa, ya fara hada rahoton da zai mika wa Trump

Adamu Baikie, wanda ya kafa tarihin zama Farfesa na farko a fannin ilimi daga Arewacin Najeriya, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 94 da haihuwa.

Adamu Baikie
Farfesa a fannin ilimi na farko a Arewacin Najeriya, Farfesa Adamu Baikie Hoto: Umar El-Faruk
Source: Facebook

Iyalan Adamu Baikie sun tabbatar da labarin rasuwarsa ga jaridar Daily Trust a yau Juma'a, 12 ga watan Disamba, 2025.

Farfesa Adamu Baikie ya rasu a Zaria

Babban dansa, Manjo Muhammad Adamu (mai ritaya) ya ce mahaifinsu, Farfesa Adamu ya rasu ne da yammacin ranar Juma'a a gidansa da ke birnin Zaria a jihar Kaduna.

Farfesa Baikie ya kasance babban masani ne a harkoki ilimi, malami, kuma jami’in gudanarwa a manyan jami’o’i a cikin Najeriya da kasashen waje.

Ya rike kujerar shugaban jami'a (VC) a jami'o'i daban-daban a Najeriya a zamanin rayuwarsa kuma ba da gudummuwa sosai wajen gina tsarin ilimi a manyan makarantu.

Manjo Muhammad ya ce ya bar ’ya’ya guda biyar, sannan za a sanar da lokacin da za a yi jana’iza nan ba da jimawa ba in ji jaridar Vanguard.

Aruwan ya tabbatar da rasuwar Farfesa Adamu

Tsohon kwamishina a jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da rasuwar Farfesa Adamu a shafinsa na Facebook da daren yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da muka sani game da daukar sababbin 'yan sanda 50,000 da za a yi a Najeriya

Aruwan ya ce:

"A yammacin yau Juma'a, Allah Madaukakin Sarki, cikin rahamarsa mara iyaka, ya karbi ran Farfesa Adamu Baikie bayan dogon lokaci yana bautar ubangiji da yi wa jama'a hidima.
"Marigayin ya na da babban tasiri a fannin ilimi. Baba Baikie shi ne Farfesa na farko na Ilimi a Arewacin Najeriya. Allah Ya jikansa da rahama, Ya sa ya huta."
Kaduna.
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewa ta Yamma a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tuni dai mutane daga sassa daban-daban na kasar nan musamman mazauna Zaria a jihar Kaduna suka fara mika sakon ta'aziyya da alhini bisa rasuwar Farfesan.

Kanwar Janar Abdulsalami ta kwanta dama

A wani rahoton, kun ji cewa an shiga jimami da alhini a jihar Neja yayin da tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya), ya yi rashin daya daga cikin 'yan uwansa.

Rahotanni sun nuna cewa Janar Abdulsalami, wanda ya shugabanci Najeriya a lokacin mulki soji, ya rasa kanwarsa, Hajiya Talatu Abubakar a ranar Litinin da ta gabata.

Bayanai sun nuna cewa an riga da an yi jana’izar marigayiya Hajiya Talatu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, inda Gwamna Umaru Bago ya halarta a Babban Masallacin Minna, jihar Neja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262