Dangote Ya Rubuta Wasiyya, Za a Cire Wani Kaso Mai Tsoka a Dukiyarsa idan Ya Rasu

Dangote Ya Rubuta Wasiyya, Za a Cire Wani Kaso Mai Tsoka a Dukiyarsa idan Ya Rasu

  • Ahaji Aliko Dangote ya bayyana cewa ya bar wa iyalansa wasiyyar cewa za a cire 25% na dukiyarsa a ba gidauniyarsa don ci gaba aikin taimako
  • Hamshalin dan kasuwar ya fadi haka ne a wurin kaddamar da shirin tallafin ilimi, wanda zai rika ware Naira biliyan 100 a kowace shekara
  • Ana sa ran shirin zai taimaka wa miliyoyin dalibai a fannoni da dama kamar tallafin karatu, gina makarantu, da samar da kayan koyo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Hamshakin 'dan kasuwar nan kuma attajirin mai kudi lamba daya a Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya kaddamar da shirin tallafin ilimi a karkashin gidauniyar Aliko Dangote (ADF).

Dangote, 'dan asalin jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ya tsara kashe Naira biliyan 100 a kowace shekara a shirin tallafin ilimi mafi girma a tarihi domin taimaka wa dalibai.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

Alhaji Aliko Dangote.
Attajirin dan kasuwa da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote Hoto: @AlikoDangote
Source: Getty Images

Leadership ta ce a lokacin ƙaddamar da shirin a ranar Alhamis, Dangote ya ce an tsara wannan gagarumin tallafin tare da amincewar ’ya’yansa uku da mahaifiyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace wasiyya Dangote ya rubuta?

Ya bayyana cewa ya rattaba hannu kan wasiyyar cewa ya keɓe 25% na dukiyarsa zuwa Aliko Dangote Foundation (ADF) domin tabbatar da dorewar sabon Shirin Tallafin Ilimi.

Dangote ya ce 'ya'yansa uku da mahaifiyarsa sun sa hannu a takardar yarjejeniya domin tabbatar da cewa aikin jinƙai na gidauniyarsa ya ci gaba ko da bayan ransa.

“Dorewar wannan shiri, wanda nake fatan zai ci gaba har tsawon ƙarni a gidanmu, ya ta’allaka ne kan matakin da na ɗauka na bada 25% na dukiyata ga gidauniyata.
"Na riga na rubuta wasiyya kuma 'ya'yana uku, mahaifiyata, duk sun sanya hannu, idan wani abu ya same ni na mutu, kashi 25 na dukiyata za su tafi kai tsaye zuwa gidauniyata."

Dangote ya kafa shirin tallafin ilimi

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Gwamna Abba zai dauki sababbin ma'aikata 4,000 a jihar Kano

Wannan sabon Shirin Tallafin Ilimi da zai rika lakume Naira biliyan 100 duk shekara, shi ne mafi girma daga ɓangaren masu zaman kansu a tarihin Najeriya.

Ana kuma sa ran zai taimaka wa akalla ɗalibai miliyan 1.3 cikin shekaru goma masu zuwa ta hanyar tallafin karatu, gina makarantu, da samar da muhimman kayan koyo da koyarwa.

Hamshakin dan kasuwar, Aliko Dangote ya ce shiriin wani muhimmin mataki ne ne a tarihin gidauniyar, da kuma babbar dama ga makomar ilimi a Najeriya.

Aliko Dangote.
Shugaban rukunin kamfaninin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote Hoto: Dangote Group
Source: Getty Images

Ya jaddada cewa ba za a iya samun cigaban ƙasa ba tare da zuba jari mai tsoka a bangaren ci gaban ɗan adam ba, kamar yadda Punch ta kawo.

Wannan ya nuna ƙarin jajircewar Dangote wajen ci gaba da bada gudummawa ga al’umma, musamman a bangaren ilimi wanda yanzu ya zama ginshiƙi a ayyukan jinƙai na gidauniyar.

Dangote ya rage farashin fetur

A baya, kun ji cewa matatar Dangote da ke jihar Legas ta yi rangwame a farashin kowace litar fetur a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke shirin bukukuwan kirismeti.

Matatar hamshakin dan kasuwar ta saukar da farashin kowane litar fetur a rumbunan ajiya daga N828 zuwa N699 da nufin saukaka wa 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

Wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa wannan sabon ragin wani yunkuri ne na nuna cewa matatar na mutunta walwalar ‘yan kasa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262