Lokaci Ya Yi: Gwamnati Ta Tabbatar da Rasuwar Mataimakin Gwamna bayan Ya Fito Ofis

Lokaci Ya Yi: Gwamnati Ta Tabbatar da Rasuwar Mataimakin Gwamna bayan Ya Fito Ofis

  • Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya tabbatar da rasuwar mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo bayan ya fito aiki ranar Alhamis
  • Gwamnatin Bayelsa ta ayyana zaman makokin kwanaki uku domin jimamin wannan rashi tare da sauke tutoci a jihar mai arzikin mai
  • Mai girma Diri ya aika sakon ta'aziyya ga matar Lawrence Ewhrudjakpo, 'ya'yansa da sauran 'yan uwa da al'ummar jihar Bayelsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Gwamnatin jihar Beyelsa da ke Kudancin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mataimakin gwamna, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, yana da shekaru 60 a duniya.

A jiya Alhamis ne Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa da ke cikin gidan gwamnatin Bayelsa, inda aka garzaya da shi asibitin tarayya (FMC) amma rai ya yi halinsa.

Lawrence Ewhrudjakpo
Mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Marigayi Sanata Lawrence Ewhrudjakpo Hoto: Sen. Lawrence Ewhrudjakpo
Source: Facebook

Bayelsa ta tabbatar da rasuwar Lawrence Ewhrudjakpo

Kara karanta wannan

Jita jita ta ƙare: Mataimakin gwamna da aka garzaya da shi asibiti ya mutu

Tashar Channels tv ta rahoto cewa gwamnati ta tabbatar da rasuwar mataimakin gwamnan da yammacin yau Juma'a, 12 ga watan Disamba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Douye Diri ya yi alhinin wannan babban rashi, ya kuma ayyana hutun kwanaki uku domin zaman makokin rasuwar mataimakin gwamnan.

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, wayar da kan jama'a da dabaru na Bayelsa, Ebiuwou Koku-Obiyai ya rattaba wa hannu.

Gwamnatin Diri ta yi alhinin wannan rashi

Gwamnatin Bayelsa ta bayyana rasuwar mataimakin gwamnan a matsayin abin “bakin ciki wanda ya girgiza jama'a sosai."

Sanarwar ta ce:

"Gwamnatin Jihar Bayelsa na mika alhini da baƙin ciki matuƙa bisa rasuwar Mataimakin Gwamna, Mai Girma Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, Ph.D, wanda ya rasu ba zato ba tsammani ranar Alhamis, 11 ga Disamba 2025, yana da shekaru 60.”

An ce marigayin ya fito aiki kamar yadda aka saba a ranar, sai kawai ya fadi lokacin da yake kan hanyar zuwa wani taron a ofishinsa.

Rahoto ya nuna an garzaya da shi Asibitin Federal Medical Centre (FMC) da ke Yenagoa, inda aka tabbatar da rasuwarsa daga baya.

Kara karanta wannan

Allura ta tono garma: Tsohon hadimin Matawalle ya shirya yi masa fallasa gaban kotu

Gwamna Diri ya ayyana zaman makoki a Bayelsa

Gwamna Douye Diri ya ayyana zaman makoki na kwana uku, daga ranar Juma’a, tare da umarnin a sauke tutoci zuwa rabi a duk fadin jihar Bayelsa.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Rasuwarsa babban rashi ce ga gwamnati da jama’ar Jihar Bayelsa da kasar gaba daya.”
Gwamna Douye Diri da mataimakinsa.
Gwamnan Bayelsa, Douye Diri tare da mataimakinsa a wurin yakin neman zabe Hoto: Douye Diri
Source: Facebook

Gwamna Diri ya yi ta’aziyya ga matar mamacin, Beatrice, da ’ya’yansa, iyalan Ewhrudjakpo, al’ummar garin Ofoni, tsohon Gwamna Henry Seriake Dickson da daukacin mutanen jihar.

Ya roki Allah ya ba iyalan da jama’an jihar hakuri da juriya bisa wannan babban rashi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Jam'iyyar PDP ta mika sakon ta'aziyya

A wani labarin, kun ji cewa PDP ta kawo karshen jita-jitar da ake yadawa game da mutuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.

Sakataren yaɗa labarai na PDP ta ƙasa, Ini Ememobong, ta bayyana cewa mutuwar mataimakin gwamnan ta girgiza jam'iyyar matuka

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan Bayelsa ya mutu? An gano gaskiyar halin da yake ciki a asibiti

PDP ta yi addu’ar Allah ya ji ƙansa ya kuma bai wa iyalansa, gwamnatin jihar Bayelsa da al’ummar jihar haƙurin jure wannan babban rashi da suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262