Matatar Dangote Ta Yi Babban Rangwame, Ta Canza Farashin Litar Fetur a Najeriya

Matatar Dangote Ta Yi Babban Rangwame, Ta Canza Farashin Litar Fetur a Najeriya

  • Matatar Dangote da ke jihar Legas ta yi ragi a farashin kowace litar fetur a lokacin da 'yan Najeriya ke shirin bukukuwan kirismeti
  • Rahoto ya nuna cewa matatar ra rage N129 a kan kowace litar fetur domin saukakawa mutane musamman a fannin sufuri yayin bikin karshen shekara
  • Wata majiya daga matatar Dangote ta ce ragin na nuna yadda suke mutunta walwala da jin dadin 'yan Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Yayin da ake shirye-shiryen fara bukukuwan kirismeti, matatar Dangote ta sauke farashin man fetur domin saukaka wa mutane a Najeriya.

Katafariyar matatar ta hamshakin 'dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ta rage farashin kowace litar fetur da fiye da kaso 15.

Gidan mai.
Ma'aikacin gidan mai yana kasuwancin man fetur a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matatar Dangote ta rage farashin fetur

Tribune Nigeria ta tattaro cewa matatar Dangote saukar da farashi a rumbunan ajiya daga N828 zuwa N699 kan kowace lita.

Kara karanta wannan

NLC: 'Yan kwadago sun saka ranar zanga zanga a jihohi 36 da Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kididdigar kasuwa da Petroleumprice ta fitar a ranar Juma’a ta nuna cewa kamfanin ya sake yin sabon rangwame, inda ya rage farashin kowace litar fetur da N129, ragin da ya kai kashi 15.58.

Sabon farashin ya fara aiki tun daga 11 ga Disamba, 2025, wanda ya sa adadin da matatar ta yi rangwame a bana ya kai 20.

Dalilin Dangote na sauke farashin fetur

Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa jaridar Vanguard cewa wannan sabon ragin wani yunkuri ne na nuna cewa matatar na mutunta walwalar ‘yan kasa.

Haka zalika, majiyar ta ce rangwamen wata hanya ce ta nuna godiya ga goyon bayan da jama’a ke nuna wa matatar musamman a lokacin bukukuwan karshen shekara.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta ce matatar ta sauke farashin ne domin rage tsadar sufuri kafin Kirismeti, lokacin da miliyoyin 'yan Najeriya ke tafiya a fadin jihohi domin sake haduwa da iyalansu.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun rage sayan fetur, Dangote ya taka rawa a wadatar da mai

"Wannan wani ɓangare ne na gudummawar da muke bayarwa don tabbatar da cewa 'yan Najeriya sun ji daɗin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.
"Burinmu ne mu ga farashin zirga-zirgar 'yan Najeriya daga wani yanki na ƙasar zuwa wani ya yi araha domin saukaka wa jama'a," in ji majiyar.
Alhaji Aliko Dangote.
Shugaban rukunin kamfaninin Dangote Group, Alhaki Aliko Dangote Hoto: @Dangotegroup
Source: Getty Images

A makon da ya gabata, shugaban rukunin kamfaninun Dangote, Aliko Dangote, ya sake jaddada aniyarsa ta ci gaba da rage farashin fetur domin gogayya da kasuwannin duniya.

Ya kara da cewa dizal da fetur za su ci gaba da kasancewa a kasuwa “cikin farashi mai sauki da rahusa.”

An rage amfani da fetur a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar NMDPRA ta fitar da sabon rahoto da ke nuna cewa amfanin fetur a Najeriya ya ragu sosai a kasar nan.

Hukumar ta ce amfani da fetur din ya ragu zuwa lita miliyan 52.9 a kowace rana a watan Nuwamba, daga lita miliyan 56.74 a Oktoba na 2025.

Rahoton ya kara da cewa shigo da fetur daga waje ya karu zuwa lita miliyan 52.1 a rana, daga lita miliyan 27.6 a watan Oktoba duk da matatar Dangote ta kara yawan feturin da take samarwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262