'Dan Majalisar Amurka Ya Koma Kasarsa, Ya Fara Hada Rahoton da zai Mika wa Trump
- 'Dan majalisar Amurka, Riley Moore, ya kai ziyara Najeriya ya bayyana abin da ya ce idanunsa sun gane masa a ziyarar da ya kai jihar Binuwai
- Bayan ya koma kasarsa, Moore ya bayyana cewa sansanin yan gudun hijirar da ya ziyarta ya tabbatar masa da cewa tabbas ana kai hare-hare kan jama'a a Najeriya
- Moore na shirin gabatar da rahoto ga Shugaba Amurka don samar da hanyoyin aiki tare da gwamnatin Najeriya wajen dakile tashe-tashen hankula da ake fuskanta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Amurka – Riley Moore, 'dan majalisar Amurka, ya koma kasarsa bayan ya kawo ziyara Najeriya ya bayyana yadda tafiyarsa ta kasance.

Source: Twitter
Morre, wanda ya jagoranci tawagar Amurka zuwa Najeriya ya fara sassauta zafin kalamai a kan zargin kisan kare dangi da Shugaba Donald Trump da shi kan shi suka nace ana yi wa kiristocin kasar.

Kara karanta wannan
Allura ta tono garma: Tsohon hadimin Matawalle ya shirya yi masa fallasa gaban kotu
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Riley Moore ya ce a yayin ziyarar, ya isa sansanin 'yan gudun hijira a jihar Binuwai da ke fama da matsalolin ta'addanci a wasu sassa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan majalisar Amurka, Moore ya ziyarci Binuwai
Riley Moore ya bayyana cewa ya gana da Bishof Anagbe da Dugu da kuma takwaransa, Tor Tiv, sannan ya hadu da wasu ‘yan gudun hijira da ke zaune a sansanonin.
Ya bayyana cewa su wadannan mutane da ya gana da su, Kiristoci ne da Fulani, kuma wai Musulmai suka kai masu hari a gidajensu.
Moore ya bayyana cewa ya samu labarai masu tayar da hankali daga mutane da suka tsira daga irin wannan 'kisan kare dangi', ciki har da wata mata wacce aka tilasta mata kallo yayin da aka kashe ‘ya’yanta biyar.
A cewarsa, wannan abin da ya gani ba zai taba fita daga zuciyarsa ba har abada.
Ya ce:
“Ban taba ganin irin wannan abu ba. Abin da na gani zai zauna a raina har karshen rayuwata."
Moore zai mika bayanai ga Shugaban Amurka
Riley Moore ya bayyana cewa yana aiki kan wani rahoto da zai gabatar wa Shugaban Amurka, wanda zai bayyana yadda za a yi aiki tare da gwamnatin Najeriya.
Ya ce a wannan rahoto, zai fitar da tsari na samar da hadin kai domin kawo karshen 'kisan kiyashi na Kiristoci a yankin' da dakile barazanar ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas.

Source: Getty Images
Moore ya kuma ce zai gabatar da rahoton ga Shugaba Amurka nan gaba kadan, tare da yin karin bayani ga al’umma kan matakan da za a dauka domin kawo karshen wannan tashin hankali.
Wannan rahoto zai zama jagora wajen tsara manufofi na hadin gwiwa tsakanin Amurka da Najeriya wajen yaki da ta’addanci da kare rayukan fararen hula.
Amurka ta shiga da kayan abinci Najeriya
A baya, kun ji cewa jirgin ruwa dauke da tan 50,000 na alkamar da aka noma a Amurka — mai darajar Dala miliyan 15 — ya isa tashar ruwan Apapa da ke Legas yayin da ake karfafa alakar kasuwanci.
Jakadan Amurka a Legas, Rick Swart, tare da Chris Bielecki, jami’in kula da harkokin aikin gona na Amurka, su ne suka jagoranci karɓar jirgin yayin da ake sauke kayan daga jirgin ruwan.
Amurka ta bayyana cewa ingantaccen kasuwancin kayayyakin noma yana taimakawa wajen kara wa manoma karfi, samar da ayyuka, da fadada damar da masana’antun na samar da kaya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

