DSS Ta Saki Mutum 3 bayan Kuskuren Zargin Ta’addanci, Ta ba Su Diyyar N3m

DSS Ta Saki Mutum 3 bayan Kuskuren Zargin Ta’addanci, Ta ba Su Diyyar N3m

  • Hukumar DSS ta ba da umarnin sakin wasu mutane uku da aka tsare saboda zarginsu da ta'addanci
  • Shugaban hukumar, Oluwatosin Ajayi shi ya ba da umarnin sakin mutanen bayan binciken hukumar ya tabbatar da ba su da laifi
  • Mutanen da aka saki sun gode wa hukumar, suna cewa an kula da su cikin mutunci, kuma babu wani cin mutunci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Hukumar DSS, Oluwatosin Adeola Ajayi, ya ba da umarnin a gaggauta sakin wasu mutum uku da ke tsare.

Ajayi ya ce a sake Umar Ibrahim, Alhaji Bello Rabiu da Jaja Sarki Bamo da aka kama kan zargin hannu a garkuwa da mutane.

DSS ta saki mutum 3 bayan zarginsu da ta'addanci
Shugaban Hukumar DSS a Najeriya, Oluwatosin Adeola Ajayi. Hoto: Emma Courage.
Source: Facebook

Ta'addanci: Daliin DSS na saki mutum 3

Rahoton Leadership ya ce an cafke su tun watan Yunin 2025 bisa zargin hannu a ayyukan ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mataimakin ciyaman a Zamfara bayan karbar kudin fansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai an sake su ne saboda bincike ya tabbatar da cewa an kama su ne cikin kuskure ba tare da aikata laifi ba.

Bayan sake nazarin shari’unsu da wani kwamitin DSS ya yi, an gano cewa babu wata shaida da ta danganta su da laifin da ake zarginsu da shi.

Saboda haka, Ajayi ya amince a biya su kudin diyya na Naira miliyan uku domin tabbatar da adalci ga wadanda suka sha wahala saboda kuskuren jami’an tsaro.

Yadda DSS ke binciken kwa-kwaf kan ayyukanta

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa DSS na ci gaba da duba tsofaffin shari’u da dama, kuma hakan ya janyo saki ga wasu mutane da dama da aka samu wadanda aka kama su ba bisa ka’ida ba.

Wadanda aka samu da laifi kuwa, suna ci gaba da fuskantar shari’a kamar yadda doka ta tanada.

Wata majiya ta ce:

"Ajayi mutum ne mai gaskiya, kuma yana gyara kura-kuren da aka aikata cikin sauri, yana tabbatar da an bi ka’ida domin a tabbatar da adalci ga kowa.”

Kara karanta wannan

Abubakar Malami ya fadi 'gaskiyar dalilin' da ya sa EFCC ke ci gaba da tsare shi

Mutane na yabo shugaban DSS game da adalcinsa
Jami'an hukumar DSS a bakin aiki. Hoto: DSS.
Source: Facebook

Kudin diyya da aka ba wadanda aka sake

Wani jami’in hukumar ya ce tsarin biyan diyya kusan ya zama al’ada a karkashin jagorancin Ajayi, yana mai cewa manufarsa ita ce tabbatar da mutunci da kima ga kowa.

Bayan sakin da aka yi musu, wadanda ake zargin sun bayyana godiya ga hukumar.

Daya daga cikinsu, Ibrahim, ya ce:

“An ciyar da mu yadda ya kamata, ba a taba cin zarafinmu ba. Jami’an sun kula da bukatunmu har zuwa lokacin da aka sallame mu.”

DSS ta ba da shaida kan Tukur Mamu

A baya, mun ba ku labarin cewa hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta kara gabatar da sabon shaida a gaban kotu a shari'ar da ake yi da Tukur Mamu.

A wannan karon, shaidan ya shaidawa kotu cewa tun bayan da Tukur Mamu ya karbe kudin fansa N50m, ya canza rayuwa.

DSS ta bayyana cewa ya tura ’yan uwansa huɗu ƙasar Masar tare da sayen motocin alfarma bayan da kudin suka shiga aljuhunsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.