Sababbin Jakadu: Mutane 5 da Tinubu Ya Nada da Suka Fuskanci Manyan Zarge Zarge

Sababbin Jakadu: Mutane 5 da Tinubu Ya Nada da Suka Fuskanci Manyan Zarge Zarge

Abuja - Majalisar dattawa ta fara tantance sunayen jakadu da Shugaba Bola Tinubu ya miƙa mata, inda kallo ya koma kan wasu mutane biyar da ke fuskantar zarge-zargen da ake ganin za su iya shafar yadda za su wakilci Najeriya a ƙasashen waje.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bayan sama da shekaru biyu ba tare da nada jakadu ba, Tinubu ya fara tura sunaye tun daga 26 ga Nuwamba, inda ya fara da mutum uku, daga baya ya turo jerin mutane 32, kafin ya sabunta jerin zuwa 65.

Tinubu ya nada wasu mutane 5 da suka fuskanci zarge-zarge a baya.
Okezie Ikpeazu, Femi Fani-Kayode, da Reno Omokri, da suka shiga jerin sababbin jakadun Najeriya. Hoto: @realFFK, @IkpeazuOkezie, @renoomokri
Source: Twitter

A cikin wasiƙar da ya tura, Tinubu ya nemi majalisar ta yi gaggawar duba sunayen domin cike muhimman mukaman diflomasiyya, in ji wani rahoto na jaridar Daily Trust.

Jerin sunayen jakadu ya jawo suka

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta wasiƙar a zaman majalisa, ya kuma mika sunayen ga kwamitin harkokin waje domin su tantance cikin mako ɗaya.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume da Oshiomhole sun gwabza a majalisa kan tantance Omokri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyun adawa, ƙungiyoyin farar hula da wasu ’yan Najeriya sun yi zargin cewa wasu daga cikin waɗanda aka zaɓa suna da kashi a gindinsu, don haka ba su cancanci wannan mukami ba.

Musamman jam’iyyun PDP, ADC da NNPP suka zargi Tinubu da cewa yana amfani da nadin jakadu domin saka wa abokai da manyan ’yan siyasa da suka fuskanci tuhume-tuhume a baya.

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya fi mayar da martani kan naɗin tsohon shugaban INEC, Mahmood Yakubu, inda ya ce sam nadin bai dace a irin wannan lokaci ba.

Mutane 5 da suka fuskanci tuhume-tuhume a baya

Ga jerin mutum biyar da rahoton Punch ya nuna irin tuhume-tuhume da zarge-zargen da suke fuskanta, duk da tuni wasu INEC ta gama tantance su:

1. Ayodele Oke

Ayodele Oke ya kasance tsohon shugaban hukumar NIA da ya fuskanci tuhume-tuhumen rashawa.
Ayodele Oke, tsohon shugaban hukumar NIA yana jawabi a taron Atlantic Council. Hoto: @Imranmuhdz/X
Source: UGC

Ayodele Oke, tsohon shugaban hukumar tsaro ta leken asiri (NIA), yana cikin wadanda ake tuhuma da rashin gaskiya.

A 2019, EFCC ta ayyana shi da matarsa, Folasade, a matsayin “wadanda ake nema ruwa a jallo” saboda zargin rashawar N13bn da ake yi masu.

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

Wata sanarwar da EFCC ta wallafa a shafinta na intanet, ta bayyana cewa Oke da matarsa sun tsallake sun bar ƙasar kafin gurfanarwar kotu, lamarin da ya sa kotun tarayya ta ba da umarnin kamasu.

A watan Afrilu 2017, EFCC ta gano $43m, £27,800 da N23.8m a wani gida a birnin Ikoyi, Lagos—kudin da aka danganta su da Oke.

Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin bincike ƙarƙashin Yemi Osinbajo, wanda ya ruwaito cewa NIA ta karɓi dala miliyan $289m daga ma’aikatar NAPIMS ba bisa ƙa’ida ba a 2015. Kwamitin ya nemi a tsige Oke daga aiki.

EFCC ta gurfanar da shi da matarsa, amma daga baya ta janye tuhumar saboda dalilan tsaro, kamar yadda rahoton jaridar The Cable.

Majalisa ta tantance Ayodele Oke

Duk da wadannan zarge-zarge, majalisar dattawa ta tantance Ayodele Oke, kuma har ma ta ce ya cancanci wannan mukami na jakadan Najeriya da Tinubu ya ba shi.

Mataimakin shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kasashen waje, Sanata Henry Dickson ya wallafa a shafinsa na X cewa Oke ya wanke kansa daga tuhume-tuhumen da ake yi masa.

"Bayan bayanan da Mr. Oke ya yi da kuma janye karar da EFCC ta yi a kansa, na kada kuri'ar amince wa da nadinsa, kuma na taya shi murna. Na kuma amince a tabbatar da nadin sauran jakadun biyu, Kayode Are da Aminu Dalhatu, wadanda dukkaninsu sun cancanta."

Kara karanta wannan

Ganduje ya hango matsalar da APC za ta iya shiga a Kano kan ayyana dan takara

2. Ibok-Ete Ibas

Ibok-Ete Ibas ya rike shugabancin kwarya na jihar Rivers lokacin da Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar.
Vice Admiral Ibok-Ete Ibas zaune a ofis lokacin da ya zama shugaban riko na jihar Rivers. Hoto: Ibok-Ete Ibas
Source: Facebook

Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) ya yi mulki a matsayin shugaban riko na jihar Rivers daga Maris zuwa Satumba 2025 bayan Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Rahoton jaridar The Nation ya nuna cewa ana tuhumar Ibok-Ete Ibas da karkatar da kudade har N283bn lokacin da yake mulkin Rivers.

A Oktoba, 2025, hukumar ICPC ta tabbatar da karɓar ƙorafe-ƙorafe kan binciken kuɗaɗen da Rivers ta karɓa daga FAAC lokacin mulkinsa. Lauya Deji Adeyanju ne ya kai ƙara, yana neman a binciki duk kudaden da Ibas ya kashe.

Majalisar dokokin Rivers ma ta sanar da niyyarta na binciken duk kudin da aka kashe a lokacin dokar ta-ɓaci, abin da ya sa wasu kungiyoyi da dattawan jihar suka bukaci Ibas ya bada bayanin inda kudin suka tafi.

Sai dai Ibas ya ce majalisar ba ta da hurumin bincikensa tunda ba su ne suka naɗa shi ba. Ya ce binciken zai zama tamkar bincikar shugaban kasa da majalisar tarayya ne, waɗanda suka saka shi a kujerar.

Kara karanta wannan

'Ku daina sayen motocin alfarma,' Muhimmin sakon Dangote ga masu kudi a Najeriya

Channels TV ta rahoto cewa an hango Vice Admiral Ibok-Ete Ibas a dakin tantance sababbin jakadun, kuma kwamitin tantancewar ya bukaci tsofaffin ministoci, jakadu da 'yan majalisa su yi gaisuwa su tafi ba tare da an yi masu tambayoyi ba.

3. Okezie Ikpeazu

Okezie Ikpeazu ya shiga jerin sababbin jakadun da Tinubu ya nada.
Okezie Ikpeazu tsohon gwamnan jihar Abia da Tinubu ya nada jakadan Najeriya. Hoto: @IkpeazuOkezie
Source: Twitter

Tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu (2015–2023), wanda ya koma APC a shekarar 2024, yana fuskantar tuhuma mai nauyi, in ji rahoton Premium Times.

Binciken da KPMG ta yi ya zarge shi da karkatar da N1.9tn lokacin mulkinsa bayan Gwamna Alex Otti ya ba da umarnin a gudanar da binciken.

Rahoton ya nuna an biya kudin ayyukan da ba a gudanar da su ba, an karɓi rance ba tare da bayyana dalili ba, an kasa karɓar kudaden IGR, da kuma biyan wasu kudade ba tare da takardun da za su tabbatar da hujjar biyan ba, da dai sauran zarge zarge.

Sai dai, Mr Ikpeazu, ya karyata dukkan wadannan zarge-zarge, inda ya yi bayanai dalla dalla game da kudaden da ake zargin ya karkatar da yadda aka yi amfani da su.

Majalisa ta tantance Okezie Ikpeazu

Duk da wadannan tuhume-tuhume, kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje ya tantance Ikpeazu, kuma ya tabbatar da nadinsa.

Kara karanta wannan

Cikakkun sunayen jakadun kasashe 21 da suka mika wa Tinubu takardu a Abuja

Kwamitin majalisar ya amince da nadin Ikpeazu, tsohon gwamnan Abia ne a ranar Alhamis, bayan da ya amsa tambayoyi daga sanatoci.

4. Reno Omokri

Reno Omokri ya kasance yana sukar Tinubu a baya, amma daga baya ya dawo yana kare gwamnatinsa
Reno Omokri, tsohon mai sukar Tinubu da ya shiga jerin sababbin jakadun Najeriya. Hoto: @renoomokri
Source: Twitter

Reno Omokri, tsohon hadimin Goodluck Jonathan, ya taba kasancewa cikin manyan masu sukar Tinubu kafin daga baya ya canza salo, ya koma kare gwamnatin shugaban kasar.

A lokacin zaben 2023, Omokri ya bayyana a Arise TV yana cewa Tinubu “dillalin miyagun kwayoyi ne”, yana cewa ya je Chicago ya samo takardun da ke tabbatar da haka.

A 2022 kuma ya jagoranci zanga-zanga a Chatham House yana sukar Tinubu. Daga baya ya bayyana cewa ba zai taba aiki da Tinubu ba, yana cewa “babu wannan tunanin a jinin jikina”.

A daidai lokacin da Tinubu ya sanya sunan Omokri a jerin sababbin jakadu, tsohon magajin garin Blanco City, da ke Amurka, Mike Arnold, ya rubuta wasika ga Najeriya kan wannan nadi.

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa Mike ya aika wa majalisar dattawa ƙorafi cewa Omokri “hadari ne ga Najeriya”, yana mai cewa zai iya bata sunan ƙasar idan aka naɗa shi jakada.

Kara karanta wannan

Albishir da ministan tsaro ya fara yi ga 'yan Najeriya bayan shiga ofis a Abuja

Majalisa ta tantance Reno Omokri

A ranar Alhamis, aka samu 'yar hayaniya a majalisar dattawa game da tantance Omokri, bayan Sanata Ali Ndume da tsohon shugaban NLC, Sanata Adams Oshiomhole sun kaure da cacar baki.

Legit Hausa ta rahoto cewa, Sanata Ndume ya so Omokri ya yi gaisuwa ya wuce kawai ba tare da amsa tambayoyi ba, amma Sanata Oshiomhole ya ce bai yarda ba, dole a yi masa tambayoyi saboda kowa ya san irin maganganun da Omokri ya rika yi game da Tinubu a baya.

Sai dai, bayan rigimar sanatocin ta lafa, Oshiomhole ya yaba wa Omokri, yana cewa Shugaba Tinubu ya nuna dattako domin zaben mutumin da ya taba sukar sa a baya.

5. Femi Fani-Kayode

Femi Fani-Kayode shi ma ya kasance yana sukar Tinubu a baya kafin ya shiga APC a 2021
Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama da Tinubu ya nada jakadan Najeriya. Hoto: @realFFK
Source: Twitter

Shi ma tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya kasance shahararren mai sharhi kan lamuran kasar nan kuma ya dade yana sukar Tinubu kafin ya koma APC a 2021.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi zazzafar addu'a kan 'yan ta'adda da masu taimakonsu

A 2019, ya yi wani rubutu da ya ja hankali, inda ya ce “ba zan taba shiga APC ba har abada”. A 2015 ya zargi Tinubu da “rashin lafiya da shaye-shaye”, tare da kiran sa da “mafi girman mai cin amanar mutane” a Nigeria.

A gefe guda kuma, Femi Fani-Kayode ya fuskanci shari’o’in cin hanci da rashawa da dama, kuma EFCC ta kai shi kotu tare da jan shari'ar tsawon shekaru, daga karshe kuma aka wanke shi daga dukkan tuhuma.

Majalisa ta tantance Fani-Kayode

Femi Fani-Kayode na daga cikin sababbin jakadun da majalisar dattawa ta tantancensu a ranar Alhamis, kuma ka amince da nadinsu.

Adeyeye Ogunwusi, Ooni na masarautar Ife, ya taya Fani-Kayode murna bisa tsallake tantancewar majalisar dattawa, tare da godewa sanatocin kan amincewa da nadinsa.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa, basaraken ya ce nadin Fani-Kayode wata karramawa ce ga al'ummar kasar Ife da kuma jihar Osun gaba daya.

Nadin jakadu: Jam'iyyar PDP ta dura kan Tinubu

A wani labari, mun ruwaito cewa, jam’iyyar adawa ta PDP ta bukaci a janye jerin sunayen jakadu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika wa majalisar dattawa.

Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Kwamared Ini Ememobong, ya bayyana cewa jerin sunayen cike yake da mutanen da suke da halin rashin gaskiya.

Kara karanta wannan

Bwala: 'Yadda mahaifiyar Tinubu ta taka rawa a nadin manyan mukaman gwamnati'

Jam’iyyar ta kuma bukaci Tinubu ya sake aika jerin sunayen ’yan Najeriya masu kyakkyawan tarihin dimokuradiyya da nagartaccen hali, wadanda za su iya wakiltar kasar cikin girmamawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com