Kotun Koli Ta Soke Afuwar Tinubu ga Maryam Sanda, Ta Tabbatar da Hukuncin Kisa
- Kotun Koli ta yanke hukunci kan afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi ga Maryam Sanda a dalilin laifin kashe mijinta
- Hukuncin ya tabbatar da matakin da kotun daukaka kara ta yi tun farko na yanke mata hukunin kisa kan kashe mijinta
- Kotun ta ce hujjojin lauyoyin gwamnati sun tabbatar da laifin Maryam Sanda fiye da kima, ta tabbatar da hukuncin kotun farko
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kotun Koli ta rusa afuwar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi ga Maryam Sanda wacce aka samu da laifin kisan kai.
An yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ne a shekarar 2020 bayan samunta da laifin kashe mijinta.

Source: Facebook
A hukuncin da aka yanke, kotun ta zartar da hukunci daga alkalai hudu, inda ta tabbatar da hukuncin kisa da kotun Abuja ta yanke, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin rusa afuwar Tinubu ga Maryam Sanda
Tinubu ya rage hukuncin zuwa shekaru 12 a kurkuku saboda nuna sauyin halaye, amma babbar kotun ta ce hakan bai dace ba.
Lamarin ya jawo maganganu da wasu ke ganin bai kamata a yi mata afuwa duba da danyen aiki da ta aikata na hallaka mijinta.
Kotun ta kuma tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yi na amincewa da hukuncin kotun farko ba tare da canji ba.
Mai shari'a, Moore Adumein shi ne ya jagoranci hukuncin, inda ya ce gwamnati ba ta da ikon ba da afuwa a lokacin da irin wannan shari'a ke gaban kotu.
Ya ce karar tana kan matakin daukaka kara, don haka afuwar ba ta da inganci kuma ba ta bi doka ba.
A cewar alkalan, lauyoyin gwamnati sun gabatar da hujjoji masu ƙarfi da suka tabbatar da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.
Kotun ta ce an tabbatar da laifin bisa ka’ida, kuma kotunan da suka gabata sun yi hukunci a bisa shaidun da suka samu.

Source: Twitter
Yadda aka yi watsi da bukatar Maryam Sanda
A cikin shari’ar, alkalin ya ce laifin kisa ba abin da za a nuna tausayi kai tsaye bane, musamman idan akwai matakin daukaka kara, cewar The Guardian.
Ya kara da cewa ikon yafiyar shugaban kasa ba zai shafi irin wannan shari'a ba har sai an kammala matakan shari'a gaba ɗaya.
Kotun Koli ta yi watsi da daukaka karar da Maryam Sanda ta gabatar, tana mai cewa ba ta da tushe ko wata hujja da za ta canza hukuncin da aka riga aka tabbatar.
Mahaifin Bilyamin ya magantu kan Maryam Sanda
Mun ba ku labarin cewa mahaifin marigayi Bilyaminu Bello, Alhaji Ahmed Bello Isa ya yi magana bayan afuwar shugaban kasa Bola Tinubu.
Dattijon ya ce ya amince da afuwar da Shugaba Tinubu ya yi ga Maryam Sanda, yana mai cewa ya dade da yafewa kuma bai rike komai a ransa ba.
Ya ce fansa ba za ta dawo da ɗansa ba, amma yafiya tana kawo zaman lafiya, yana mai kira da a bar komai ga Allah SWT.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


