NLC: 'Yan Kwadago Sun Saka Ranar Zanga Zanga a Jihohi 36 da Abuja

NLC: 'Yan Kwadago Sun Saka Ranar Zanga Zanga a Jihohi 36 da Abuja

  • Kungiyar NLC ta ayyana zanga-zanga a fadin Najeriya saboda karuwar sace-sacen dalibai da hare-haren ’yan bindiga a jihohi
  • 'Yan kwadago sun ce gwamnatin Najeriya ta gagara kare makarantu, musamman na yankunan da ke da nisa da biranen kasar
  • NLC ta bukaci a binciki janye jami’an tsaro daga makarantar Wasagu da aka sace dalibai mata a Kebbi ana dab da kai hari wajen

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) za ta yi zanga-zanga ta kasa baki daya a ranar 17, Disamba, 2025, domin nuna damuwarta game da tabarbarewar tsaro da ke kara ta’azzara a sassan kasar.

Sanarwar ta fito ne bayan zaman kwamitin zartarwar kungiyar (NEC) da aka gudanar a ranar 4, Disamba, 2025 inda NLC ta bayyana cewa hare-haren ’yan bindiga da sace-sacen mutane sun yi muni.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa Fulani makiyaya da harbi, an sace shanu 168 a Filato

Yadda aka yi zanga zangar 'yan kwadago a abya
Wasu masu zanga-zanga karkashin tare da 'yan kwadago. Hoto: NLC Nigeria
Source: Getty Images

The Cable ta rahoto cewa kungiyar ta ce karuwar hare-haren da ake kai wa makarantu, musamman tare da sace dalibai mata, na nuna gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta nuna fushi kan sace dalibai a Najeriya

A cikin sanarwar da ta aike wa dukkanin shugabannin reshen jihohi a ranar 10, Disambar 2025, NLC ta nuna takaicinta kan sace dalibai mata a makarantar kwana ta Kebbi a ranar 17, Nuwamban 2025.

Kungiyar ta ce abin mamaki ne ganin cewa an janye jami’an tsaro daga makarantar jim kadan kafin faruwar lamarin, tana mai kira da a gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk masu hannu a ciki.

'Yan kwadago sun ce gwamnati ta gaza

The Nation ta rahoto cewa kungiyar NLC ta ce karuwar sace-sacen dalibai ya kai wani mummunan matsayi da ba za a amince da shi ba a kasar nan.

Ta ce gwamnati ta gaza daukar matakan da suka dace domin kare makarantu, musamman na yankunan da ke iyaka da dazuka da karkara.

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Gwamna Abba zai dauki sababbin ma'aikata 4,000 a jihar Kano

Kungiyar ta ce akwai dalilai masu karfi da ke nuna sakaci da gazawar hukumomi wajen kare lafiyar malamai da dalibai, musamman a yankunan da suka fi fuskantar barazana.

NLC ta bukaci a shirya zanga zanga

Sanarwar NEC ta umarci kungiyoyin da ke karkashin NLC da dukkanin majalisun jihohi su shirya cikakken gangami domin nuna bukatar daukar matakan tsaro cikin gaggawa.

Ta ce dole ne a tashi tsaye wajen kare rayukan yara, musamman a lokuta da akasarin hare-haren ’yan bindiga ke kai wa ga makarantun kwana da ke yankunan karkara.

Yadda aka yi zanga zanga
Matasan Najeriya yayin wata zanga zanga. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Zanga-zanga ta zama wajibi inji NLC

Kungiyar ta ce ba za ta kara zuba ido ba yayin da yaran Najeriya ke ci gaba da fadawa hannun masu garkuwa da mutane.

A cewar sanarwar, zanga-zangar 17, Disambar 2025 za ta kasance kira mai karfi ga gwamnati domin gyara kura-kurai da kuma tabbatar da cewa rayukan dalibai da malamai sun samu cikakken kariya.

An kashe shanu kusan 200 a Filato

A wani labarin, kun ji cewa matsalolin tsaro na kara ta'azzara a Najeriya, musamman tsakanin manoma da makiyaya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya za ta dauki 'yan sanda 50,000, an fitar da sharudan aikin

Rahotanni sun nuna cewa an kai hari kan wasu makiyaya da bindigogi a kananan hukumomin jihar Filato biyu.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar ya bayyana cewa maharan sun sace shanu kusan 200 a farmakin da aka kai musu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng