'Yan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Ciyaman a Zamfara bayan Karbar Kudin Fansa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Ciyaman a Zamfara bayan Karbar Kudin Fansa

  • ’Yan bindiga sun kashe mataimakin shugaban hukuma a jihar Zamfara duk da karbar kudin fansa da suka yi
  • Maharan sun hallaka Hon. Mu’azu Gwashi, duk da biyan wasu miliyoyi na kudin fansa bayan watanni shida
  • Mazauna sun ce an kawo mutumin cikin gari, amma daga baya ’yan bindigan suka koma da shi da daddare suka kashe shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bukuyum, Zamfara - ’Yan bindiga sun kashe mataimakin shugaban karamar hukumar Bukuyum ta jihar Zamfara.

Maharan sun yi ajalin Hon. Mu’azu Muhammad Gwashi, duk da cewa an biya su kudin fansa har Naira miliyan 15.

An hallaka dan siyasa a Zamfara bayan wata shida a hannun yan bindiga
Ministan tsaro, Christopher Musa da marigayi Mu'azu Gwashi da aka kashe. Hoto: Hoto: @DanKatsine50.
Source: Twitter

Rahoton Daily Trust ya ce Gwashi ya shafe sama da watanni shida a hannunsu, inda a farko suka nemi N30m kafin su sako shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sace mataimakin ciyaman a Zamfara

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa Fulani makiyaya da harbi, an sace shanu 168 a Filato

Hakan ya biyo bayan harin ’yan bindiga da suka kai a hanyar Manyaci zuwa Bukkuyum a watan Yulin 2025.

Yayin harin, yan bindiga sun bude wuta kan wata mota dauke da shugaban PDP na karamar hukumar.

An harbi Hon. Muhammad Sala Wuta a hannu da kafa yayin da yake kan hanyar zuwa Bukkuyum tare da wasu ’yan jam’iyya a cikin mota.

An sace mutane uku ciki har da Hon. Mu’azu Zannan Gwashi a yayin harin, lamarin da ya girgiza al’ummar Bukkuyum da kewaye.

Yan bindiga sun kashe shugaban karamar hukuma a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ake fama da hare-haren yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Mutane sun yi jimamin mutuwar dan siyasar

Wani mazaunin yankin, Malam Muhammad Mansur Sani, ya ce al’umma sun sha wahala wajen tattara kudin.

Ya ce:

“Sun fara neman N30m, mun kasa. Bayan sun karɓi N15m suka kawo shi cikin gari, mutane da dama sun gan shi. Amma daga baya suka koma da shi daji suka kashe shi.”

Kwamishinan yaɗa labarai na Zamfara, Mahmud Muhammad Dantawasa, ya yi ta’aziyya ga iyalan mamacin da al’ummar Bukuyum, yana mai cewa kisan abin takaici ne matuƙa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 5 sun hada kai, sun gano hanyar kawo karshen 'yan bindiga gaba daya

Zamfara: Yadda aka sace mata masu shayarwa

A wani harin da ya faru kwanaki biyu kafin wannan, ’yan bindiga sun kutsa Saran Wawa da ke yankin Ruwan Rana, suka sace mata masu shayarwa guda biyar da wasu mutum hudu.

Ɗan uwansu daya daga cikin wadanda aka sace, Malam Shehu, ya ce harin ya faru misalin ƙarfe 12:00 na dare a ranar 8 ga Disambar 2025.

Ya bayyana cewa kowacce daga cikin matan tana ɗauke da jaririnta, kuma an yi awon gaba da su zuwa wuri da ba a san shi ba.

Kuma ya ce har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su kira kowa ba domin sanin matakai na gaba game da lamarin.

'Yan bindiga sun yi kisa saboda yoghurt

Kun ji cewa yan bindiga sun kai hari a Danjibga da ke jihar Zamfara bayan takaddama saboda 'yoghurt' din N3,500.

Wannan lamari ya yi zafi, bayan an kashe mutane uku, yayin da ƴan ta'addan suka riƙa ɓalla shagunan jama'a.

Kara karanta wannan

Matsala ta tunkaro Ganduje kan ƙoƙarin yi wa Hisbah kishiya a Kano, an ja layi

Mutane sun yi martani mai zafi a shafukan sada zumunta, suna tambayar me gwamnati ke yi ake wannan aiki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.