Yan Najeriya Sun Rage Sayan Fetur, Dangote Ya Taka Rawa a Wadatar da Mai
- Hukumar NMDPRA ta yi magana game da raguwar amfani da man fetur a fadin Najeriya baki daya
- NMDPRA ta bayyana cewa amfani da fetur ya ragu sosai a rana a watan Nuwamba idan aka kwatanta da Oktoba
- Rahoton ya nuna cewa matatar Dangote ta ƙara samar da fetur zuwa lita miliyan 23.52 a rana
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar NMDPRA ta fitar da sabon rahoto da ke nuna cewa amfanin fetur a Najeriya ya ragu sosai a kasar.
Hukumar ta ce amfani da fetur din ya ragu zuwa lita miliyan 52.9 a kowace rana a watan Nuwamba, daga lita miliyan 56.74 a Oktoba.

Source: UGC
Yadda aka rage shan mai a Najeriya
Rahoton Tribune ya ce wannan raguwar ta nuna canji a yadda ake amfani da man fetur a fadin ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai duk da wannan raguwar, an samu karin samar da fetur a watan Nuwambar 2025, musamman ma daga matatun cikin gida.
Majiyoyi sun ce lita miliyan 19.5 a rana daga cikin jimillar da ake samu sun fito ne daga matatun cikin gida, sama da lita miliyan 17.08 da aka samu a watan Oktobar 2025.
Rawar da matatar Aliko Dangote ta taka
Babbar gudummawar karin samar da man ta fito ne daga matatar Dangote, wacce ta tura matsakaitan lita miliyan 23.52 a rana, kwatankwacin lita miliyan 18.03 da ta samar a watan da ya gabata.
Hukumar NMDPRA ta ce wannan karin aiki na Dangote muhimmin mataki ne wajen rage dogaro da shigo da fetur daga kasashen waje.

Source: Getty Images
Musabbabin karuwar shigo da mai
Rahoton ya kara da cewa shigo da fetur daga waje ya karu zuwa lita miliyan 52.1 a rana, daga lita miliyan 27.6 a watan Oktoba.
Hakan ya faru ne saboda ƙarancin man da aka samu a Satumba da Oktoba da ya kasa cika bukatar kasa, da kuma matakin da NNPC ta dauka na kara adadin man cikin kasa kafin bukatar bukukuwan karshen shekara.
Hukumar ta ce ragowar dalilan sun hada da jiragen ruwa 12 da aka shirya sauke kaya a Oktoba amma suka ja zuwa Nuwamba, tare da karin shigo da man da NNPC ta yi domin tabbatar da isasshen kaya a lokacin bukutu.
Game da diesel kuwa, rahoton ya ce an samu lita miliyan 20.4 a rana a matsayin isarwa, yayin da ake amfani da lita miliyan 15.4 a rana.
Yan kasuwa sun shigo da tulin mai Najeriya
Mun ba ku labarin cewa rahoton NMDPRA ya nuna cewa matatar Dangote ta samar da lita miliyan 512 a Oktobar 2025, ƙasa da buƙatar jama'an ƙasar.
'Yan kasuwa sun shigo da lita miliyan 828 na fetur daga kasashen waje, yayin da buƙatar fetur a ƙasar ta kai lita miliyan 56.7 a kullum.
Aliko Dangote ya dage cewa matatarsa za ta iya samar da lita miliyan 45 na fetur, amma rahoton NMDPRA ya nuna akasin haka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

