Sarkin Musulmi: "Babu Ruwan Kirista da Shari'ar Muslunci"
- Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce ba daidai ba ne a tilasta Kiristoci su shiga kotun shari’a ko dokokinta
- Ya jaddada cewa Shari’a doka ce ta Musulmi kawai, kuma Najeriya ƙasa ce mai addinai daban-daban da kowa ke da ƴanci
- Ya bayyana haka ne a yayin wani taro a Abuja, inda ya bayyana alakar Najeriya da addinan mazauna kasar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa babban kuskure ne a jawo ko a tilasta wa Kiristoci bin doka ko kotun Shari’a.
Ya faɗi haka ne a taron buɗe zaman shekara uku na majalisar NIREC da aka gudanar a Abuja, mai taken “Haɗin gwiwar majalisar addinai da gwamnati wajen ƙarfafa zaman lafiya a Najeriya”.

Source: Facebook
The Guardian ta ruwaito Sarkin ya tabbatar cewa Shari’a doka ce ta Musulmi 100%, don haka bai kamata Kiristoci su yi tsari ko sutura ko ibada irin ta Musulmi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Musulmi ya magantu kan Shari'ar Muslunci
Sarkin Musulmin ya ce Najeriya ba ƙasa ce ta addini guda ba, kuma gwamnati ba ta ɗauki Musulunci ko Kiristanci a matsayin addinin ƙasa ba, sai dai tana tallafa masu duka.
Ya yi suka kan kira da wasu ke yi na soke Shari’a, inda ya ce Najeriya ta amince da ’yancin kowane addini, ba tare da tsoma bakin da ya wuce gona da iri ba
A jawabinsa, Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya nemi ƙarin haɗin kai tsakanin NIREC da gwamnatin tarayya domin ƙarfafa zaman lafiya da magance matsalolin tsaro.

Source: Twitter
Rt. Hon. Tajudeen ya ce taron ya zo ne a daidai lokacin da masu tsattsauran ra’ayi ke ƙoƙarin rura wutar addini da barazana ga haɗin kan ƙasa.
Ya yaba wa NIREC bisa aikin da take yi wajen daidaita al’umma, yana mai cewa majalisa za ta tallafa wajen aiwatar da duk wasu shawarwari.
Gwamnati na neman haɗin kan ƙasa
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya ce Najeriya na fuskantar ƙalubale da dama, ciki har da matsalar tsaro da karin maganganun siyasa da ke gurɓata zukatan al'umma.
Ya ce ƙasar na fama da matsi daga ƙasashen waje saboda rahotannin karya da suke samu game da tsaron cikin gida.
Akume ya tabbatar cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa, tare da kira ga shugabannin addini da na gargajiya su haɗa kai don wanzar da zaman lafiya.
Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, shi ma ya yi kira da a ƙara haɗin kai tsakanin gwamnati da kungiyoyin addini domin magance yawaitar rashin tsaro.
A nasa jawabin, Sakataren NIREC, Rev. Fr. Cornelius Omonokhua, ya ce dukkannin rayuka daraja ce a wurin Ubangijin, don haka wajibi ne a hada kai domin magance ta’addanci da ’yan bindiga.
Sarkin Musulmi ya fadawa gwamnoni gaskiya
A baya, mun wallafa cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa 19 da su rika sauraron masu sukar gwamnati cikin haƙuri da fahimta.
Sarkin ya ce sukar gwamnati na iya zama hanya mai amfani wajen gano matsaloli da inganta shugabanci idan aka yi amfani da ita yadda ya kamata.
Sarkin Musulmi ya yi wannan jawabi ne yayin taron hadin-gwiwar gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya da aka gudanar a Kaduna a ranar Litinin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


