Allura Ta Tono Garma: Tsohon Hadimin Matawalle Ya Shirya Yi Masa Fallasa a Gaban Kotu

Allura Ta Tono Garma: Tsohon Hadimin Matawalle Ya Shirya Yi Masa Fallasa a Gaban Kotu

  • Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya dauki matakin shari'a kan zargin da ake yi masa na alaka da 'yan ta'adda
  • Biyo bayan karar da tsohon gwamnan na Zamfara ya shigar a gaban kotu, wani tsohon hadiminsa ya fito ya yi fallasa a gaban jama'a
  • Tsohon hadimin ya tabbatar da zarge-zargen da ake yi kan Matawalle, inda ya bayyana cewa a shirye yake ya fasa kwai a gaban kotu

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya shigar da kara gaban kotu kan zargin da ake masa na daukar nauyin ta'addanci.

Bello Matawalle ya bukaci kotu da ta hana gidajen jaridu wallafa cewa yana da alaka da ayyukan ta'addanci.

An yi zarge-zarge kan Bello Matawalle
Karamin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle Hoto: Dr. Bello Matawalle
Source: Original

Wani mai suna Ishaq Samaila ya wallafa takardar shari'ar a shafinsa na X a ranar, Alhamis 11 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Zargin ta'addanci: Matawalle ya tafi kotu, ya saka sunan malamin Musulunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a ba da shaida kan Matawalle

Sai biyo bayan shigar da karar, wani mai suna Musa Muhammad Kamarawa da ya yi ikirarin cewa shi tsohon mai ba Matawalle shawara na musamman ne lokacin da yake gwamna, ya ce a shirye yake ya ba da shaida..

A cikin wani faifan Bidiyo da shafin Sheikh Murtala Asada Sokoto ya sanya a Facebook, Musa Kamarawa ya tabbatar da wasu zarge-zargen da ake yi kan Matawalle dangane da alaka da ta'addanci.

Musa Kamarawa ya tabbatar da wasu zarge-zargen da Malam Murtala Bello Asada ya yi a kan Matawalle.

Ya tabbatar da cewa zargin da aka yi na sayowa 'yan ta'adda motoci, tabbas ya faru domin an ba su motoci a lokacin gwamnatin Bello Matawalle.

"An sayo motoci an ba da, an ba da mota, an ba Kachalla Halilu, an ba Bello Turji, an ba Ado Aliero. Wadannan motoci an sayo su an ba da."

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Sheikh Zakzaky ya dauki zafi, ya kausasa harshe kan gwamnati

- Musa Kamarawa

Hakazalika ya tabbatar da zargin cewa an sayo dussa an raba wa 'yan ta'adda, inda ya ce shi aka ba kwangila ya sayo ya kuma raba ta.

A ci gaba da bayanansa, tsohon hadimin na Matawalle ya tabbatar da zargin cewa an sayawa hatsabibin dan ta'adda, Bello Turji, gida a cikin garin Fakai.

Tsohon hadimin na Matawalle ya kuma tabbatar da zargin cewa tsohon gwamnan ya taba karbo belin wani tantirin dan ta'adda, Haru Dole, da jami'an tsaro suka cafke.

Musa Kamarawa ya bayyana cewa a shirye yake ya je gaban kotu domin ba da shaida kan abubuwan da ya sani.

Ya bayyana cewa wasu abubuwan ma ba a san da su ba, amma zai fasa kwai a gaban kotu domin duniya ta sani.

Sanata Marafa ya yi fallasa kan Matawalle

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Kabiru Marafa ya fito ya yi kalamai masu kaushi kan karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya nada mace ta farko a matsayin shugabar jami'ar gwamnati a Kano

Tsohon sanatan ya musanta ikirarin cewa Bello Matawalle ya taimake shi lokacin da yake rike da mukamin gwamnan Zamfara.

Sanata Marafa ya ce sabanin hakan, shi ne ya goyi bayan Matawalle har Allah ya ba shi nasarar zama gwamna a 2019.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng