Abubakar Malami Ya Fadi 'Gaskiyar Dalilin' da Ya Sa EFCC Ke Ci gaba da Tsare Shi
- Tsohon ministan shari’a Abubakar Malami ya ce EFCC ta ci gaba da tsare shi saboda an soke belinsa ba tare da dalili mai karfi ba
- Malami ya karyata zargin daukar nauyin ta’addanci da mallakar asusun banki 46, yana mai cewa zarge-zarge ne da ba su da tushe
- EFCC dai ta ce ta soke belin Malami ne saboda bai cika sharuddan da aka gindaya masa ba, ikirarin da lauyan ya fito ya karyata
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya yi bayani kan yanayin da ya sa EFCC ta cigaba da tsare shi bayan ya je ofishin hukumar da kansa a ranar Litinin.
An ce tsohon ministan na fuskantar tambayoyi kan abubuwa da dama, ciki har da zargin daukar nauyin ta'addanci, mallakar asusun banki 46, amfani da lauyoyi da dama wajen dawo da dala miliyan $322.5 na Abacha, da kuma yadda aka yi amfani da kudaden shirin tallafin gwamnati.

Source: Twitter
EFCC ta ci gaba da tsare ministan Buhari
Amma Malami ya ce an tsare shi ba tare da wani takamaiman dalili ba, sai dai kawai an shaida masa cewa an soke belin da aka ba shi a baya – duk da cewa bai karya sharuddan belin ba, in ji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mohammed Bello Doka, ya fitar a ranar Laraba, Malami ya ce an ba shi sabon sharuddan beli, wadanda ya shirya ya cika idan EFCC ta ba da izini.
Tun da farko, Malami ya karyata zargin daukar nauyin ta'addanci da mallakar asusun banki 46, yana mai cewa, "karya ne, ba su da tushe kuma an kirkire su ne don bata mani suna."
Abubakar Malami ya karyata alaka da 'yan bindiga
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Malami ya ce:
"Ina so mutane su sani cewa, babu wani lokaci da wata hukumar tsaro, a gida ko a waje da ta zarge ni, ta gayyace ni, ta titsiye ni, ta bincike ni, ko ta gurfanar da ni da sunan wai ana zargi na da daukar nauyin ta'addanci ko makamantan laifuffuka."
A cikin sanarwar da Mohammed Doka ya fitar, shi ma ya jaddada cewa:
“Babu wata hukuma ko ta cikin gida ko ta waje da ke bincike ko zargin Malami da daukar nauyin ta’addanci. Haka kuma labarin cewa yana da asusun banki 46 karya ne gaba daya.”
Mohammed Doka ya ce ko tsohon hafsan soja da aka alakanta da wannan zargi ya fito fili ya ce bai taba zargin Malami da daukar nauyin ta’addanci ba, amma kafafen yada labarai suka yi watsi da hakan.
Yadda Malami ya dawo da kudaden Abacha
Ya kuma yi nuni da irin ayyukan Malami a lokacin yana ministan shari'a wajen karfafa dokokin yaki da hada-hadar kudi da ta’addanci a Najeriya.
Daga cikinsu akwai kafa NFIU mai zaman kanta da kafa dokokin AML/CFT na 2022, wadanda suka taimaka wajen cire Najeriya daga jerin FATF grey list.
Kan batun lauyoyi da yawa da aka ce an dauka wajen dawo da kudin Abacha, Mohammed Doka ya ce gwamnatin Buhari ta ki amincewa da sharuddan lauya Enrico Monfrini na Switzerland, wanda ya nemi a biya shi $5m a farkon aiki da kuma kashi 40% na kudin da za a dawo.
Ya ce daga baya Malami ya kulla sabuwar yarjejeniya da lauyoyin cikin gida kan kashi 5% kacal — wanda ya ceci Najeriya tsakanin ₦76.8bn zuwa ₦179.2bn.

Source: Twitter
Ina kudin Abacha da aka kwato?
Mohammed Doka ya bayyana cewa an dawo da kudaden Abacha ne a matakai, kuma duk an yi amfani da su ne bisa yarjejeniya tsakaninsu da kasashen da suka bayar da kudaden:
- $322m (2017–2018) daga Switzerland - an kashe su ta shirin NSIP a karkashin kulawar Bankin Duniya da kungiyoyin farar hula
- $321m (2020) daga Jersey - an saka su a ayyukan manyan tituna: Lagos–Ibadan, Abuja–Kano, da kuma gadar Neja ta biyu
Malami, wanda ya rike mukamin ministan shari'a daga 2015 zuwa 2023, ya tabbatar da samun gayyatar EFCC a ranar 28 ga Nuwamba kuma ya ce zai halarta “a matsayin dan kasa mai bin doka.”
Hukumar EFCC ta ce ta soke belinsa ne saboda bai cika sharuddan da aka gindaya masa ba, kuma tana tsare da shi ne saboda bincike da dama da ake yi a halin yanzu.
Tambayoyin da EFCC ta yi wa Malami
Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon ministan shari'a a Najeriya, Abubakar Malami ya fadi tambayoyi da hukumar EFCC ta yi masa bayan ziyartar ofishinsu.
Malami ya ce tuhumar da hukumar EFCC ke yi masa ta takaita ne kacokan kan bayyana batun zargin maimaita aikin dawo da kudaden Sani Abacha
Ya kara da cewa EFCC ta binciki batutuwan da suka shafi zargin cin mutunci da zargin badakalar kuɗi, amma bayan ya gabatar da cikakken bayani, hukumar ta ga babu wata hujja da za ta ci gaba da bincike.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



