Abubuwa 5 da Muka Sani game da Sababbin Yan Sanda 50,000 da Za a Dauka a Najeriya

Abubuwa 5 da Muka Sani game da Sababbin Yan Sanda 50,000 da Za a Dauka a Najeriya

Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda ta Najeriya (PSC) za ta buɗe shafin yanar gizo na ɗaukar sababbin ’yan sanda 50,000 a fadin kasar nan.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan matsalar tsaro da nufin daukar matakan dawo da zaman lafiya a Najeriya.

Yan sanda.
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

A sanarwar da hukumar PSC ta wallafa a Facebook a ranar 11, Disamba, 2025, ta bayyana cewa za a bude shafin daukar 'yan sandan a makon gobe.

Sakataren Hukumar PSC, Cif Onyemuche Nnamani, ya bayyana cewa za a dauki 'yan sandan ne bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu na ƙara yawan jami’an tsaro domin inganta tsaron ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta tattaro muku muhimmancin abubuwa biyar game da daukar aikin, wanda ya kamata kowa ya sani, ga su kamar haka:

Kara karanta wannan

Tinubu ya bada umarni kan kare manyan Najeriya bayan janye 'yan sanda

1. Rukunan yan sandan da za a dauka

Za a dauki ma’aikata ne a fannoni biyu, na farko su ne 'yan General Duty, wadanda za su shiga aikin ’yan sanda kai tsaye a matsayin kuratan 'yan sanda.

Sai rukuni na biyu, masu kwarewa a fannoni daban-daban 'Specialist'. Wannan rukuni ya haɗa da ma’aikatan kiwon lafiya, direbobi masu lasisi, masu gyaran mota, da masu kwance bama-bamai (EOD–CBRN).

Sauran sun hada da masu gyaran lantarki, masu sarrafa doki da karnuka, kafintoci, masu gyaran janareta, masu walda, teloli, masana fasaha da sadarwa da sauran makamantansu.

2. Sharuɗɗan cancanta

Dole ne masu neman aiki su kasance 'yan ƙasar Najeriya kuma dole ne su kasance masu ƙoshin lafiya a jiki da tunani.

Ana buƙatar su kasance masu kyawawan halaye, wadanda ba su taba shiga laifin kudi ba, kuma ba a yanke musu hukunci a kan wani laifi ba. Haka nan kowane mai neman aikin zai gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya za ta dauki 'yan sanda 50,000, an fitar da sharudan aikin

Masu neman aikin kuratan 'yan sanda dole su kasance tsakanin shekaru 18 zuwa 25, yayin da masu neman aiki na ƙwararru ba za su wuce shekaru 28 ba.

Haka zalika ba a bukatar matan da za su nemi aikin su kasance dauke da juna biyu a lokacin bin matakan ɗaukar ma'aikatan.

Dole masu nema su kasance ba su da wata nakasa ta jiki ba, ciki har da nakasa ta gani, nakasa a gwiwa, lankwasar ƙafafuwa, gwiwoyi, matsalar gaɓoɓi, ko yanke hannu.

Ana bukatar maza su kai mita 1.67 a tsayi, mata kada su gaza tsayin mita 1.64 ba. Ga mazan da za su nemi aikin, ana buƙatar masu fadin ƙirji wanda bai gaza santimita 86 ba (inci 34).

Dakarun sanda.
Jami'an yan sanda a wurin bikin yaye su a Najeriya Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

3. Shaidar karatu

Ana bukatar duk wanda zai nemi aikin kurtun dan sanda ya mallaki takardar kammala karatun sakandire, SSCE, NECO, GCE Ordinary Level ko wata shaida mai darajarsu.

Dole ne mutum ya ci darussa biyar akalla ciki har da Turanci da Lissafi a zama biyu ko kasa da haka.

A daya bangaren, ana bukatar masu neman aikin kwararu su ci darussa huɗu, da Turanci da Lissafi a zama biyu ko kasa da haka, kuma dole ne su nuna aƙalla shekaru uku na gogewa a cikin sana'ar da suke nema.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke wa dan sandan Najeriya hukuncin kisa, za a rataye shi har lahira

4. Yadda za a cike neman aikin

Za a cike takardar neman shiga aikin dan sandan ne a shafin yanar gizo na https://npfapplication.psc.gov.ng daga makon gobe kamar yadda hukumar PSC ta sanar.

Dole masu nema su mallaki Lambar Katin Zama dan Ƙasa (NIN), adireshin imel mai aiki da lambar waya mai aiki.

Ana buƙatar mutum ya sanya kwafin takardar shaidar firamare, sakamakon SSCE, takardar shaidar zama dan jiha ko karamar hukuma, da takardar shaidar haihuwa.

Masu neman shiga fannin ƙwararru za su saka shaidar bangaren da za su nema kamar lasisin tuƙi mai inganci.

5. Lokacin rufe daukar yan sanda

Za a bude shafin yanar gizo na daukar sababbin 'yan sanda a ranar 15 ga watan Disamba, 2025 kuma za ta rufe a ranar 25 ga Janairu, 2026.

Hakan na nufin za a bai wa masu sha'awar shiga aikin dan sanda makonni shida su kammala cike bayanansu a shafin yanar gizo, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutane saboda 'Rufaida yoghurt' a Zamfara

Tinubu ya jaddada janye yan sanda

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa ba gudu ba ja da baya a matakin janye yan sanda daga gadin manyan mutane.

Tinubu ya umarci Ministan Cikin gida ya tsara yadda za a bayar da kariya ta musamman ga manyan mutane bayan janye jami’an ’yan sanda daga gadinsu.

A cikin umarnin, Shugaban Kasan ya bayyana cewa bai kama a bar manyan mutanen a cikin haɗari bayan janye jami’an tsaro da aka yi kwanan nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262