Hankula Sun Tashi, Mataimakin Gwamna Ya Fadi a Ofis, an Wuce da Shi Asibiti
- An shiga firgici bayan mataimakin gwamnan Bayelsa ya fadi a cikin ofishinsa lamarin da ya tayar da hankula a tsakanin masoyansa
- Majiyoyi sun ce Sanata Lawrence Ewhrudjakpo ya fadi yayin da aka yi gaggawar garzayawa da shi asibiti domin ceto lafiyarsa cikin gaggawa
- Likitoci sun tabbatar da cewa an kwantar da shi a asibiti, yayin da hukumomi suka ce har yanzu ba a san musabbabin matsalar ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yenagoa, Bayelsa - Fargaba ta mamaye birnin Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa game da lafiyar mataimakin gwamna.
Rahotanni sun nuna cewa Mataimakin Gwamna, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, ya fadi cak a ofishinsa a yau Alhamis 11 ga watan Disambar 2025.

Source: Twitter
Mataimakin gwamnan Bayelsa ya fadi a ofishinsa
Rahoton Vanguard ya tabbatar da cewa dan siyasar yana cikin wani hali yayin da aka garzaya da shi asibitin gwamnatin tarayya da ke Yenagoa.
Lamarin ya faru ne kusan ƙarfe 1:30 na rana a yayin da yake aiki a ofishinsa, lamarin da ya sa aka aikin gaggawa domin ceto shi.
Shaidu sun ce halin da yake ciki ya yi muni sosai lokacin da aka kai shi sashen gaggawa na asibitin.
Wane hali mataimakin gwamnan Bayelsa ke ciki
Yanzu haka an kwantar da Sanata Ewhrudjakpo a sashen kula na musamman (ICU) inda likitoci ke kula da shi.
Har yanzu babu wata sanarwa ta hukuma game da musabbabin matsalarsa, sai dai majiyoyi sun ce yana iya kasancewa matsalar zuciya.
Wata majiya mai kusanci da shi ta ce yana da son aiki matuka, tana mai cewa:
"Mutumin mai aiki ne sosai; ya kamata ya rika samun lokaci ya huta."
Jami’an tsaro sun mamaye asibitin, yayin da manyan jami’an gwamnati suke kai ziyara domin nuna damuwa.
Kokarin da aka yi don jin ta bakin mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Mista Doubara Atasi, ya ci tura, cewar Channels TV.
Sai dai majiyoyin asibiti sun tabbatar cewa yana samun cikakkiyar kulawa kuma yanayin da yake ciki ya fara daidaituwa.

Source: Twitter
Ana jita-jitar sanadin faduwar mataimakin gwamna
An tabbatar da cewa lamarin ya tayar da hankula duba da halin da aka gano shi a ciki bayan ya fadi kafin a wuce da shi asibiti domin ceto lafiyarsa cikin gaggawa.
Wadanda suka san sanatan sun bayyana cewa mutum ne jajitacce a wurin aiki wanda bai gajiya, mafi yawansu ma su na danganta hakan da sanadin faduwarsa.
Har ila yau, gwamnatin jihar ba ta ce komaiba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto domin Wakilin Legit Hausa ya leka shafukan sanatan da kuma na gwamnan jihar amma babu wata sanarwa.
Minista ya fadi yayin tantance shi a majalisa
Kun ji cewa Balarabe Abbas ya bayyana dalilin faduwar da ya yi a majalisar Dattawa yayin da ake tantance shi a matsayin minista.
Balarabe wanda shi ne ya maye gurbin Nasir El-Rufai daga jihar Kaduna ya suma ana tsaka da tantance shi domin ba shi kujerar minista.

Kara karanta wannan
Mataimakin gwamnan Bayelsa ya mutu? An gano gaskiyar halin da yake ciki a asibiti
A wancan lokaci, ya bayyana wa shugaban majalisar, Goswill Akpabio cewa ya shafe kwanaki uku ya na aiki ba tare da hutawa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

