Rashin Tsaro: Sheikh Zakzaky Ya Dauki Zafi, Ya Kausasa Harshe kan Gwamnati
- Shugaban kungiyar Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita
- Sheikh Zakzaky ya bayyana cewa akwai alamun tambaya kan yadda mutanen da ke rayuwa a daji suke samun manyan makamai
- Shugaban na IMN ya yi zarge-zarge kan gwamnati saboda yadda ta bari matsalar rashin tsaro ta ci gaba da ta'azzara a kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Shugaban kungiyar IMN ta Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro.
Sheikh Zakzaky ya zargi hukumomin kasar nan da hannu a tabarbarewar rashin tsaron Najeriya, yana cewa ana kulla rikicin ne da gangan.

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a taron manema labarai ranar Laraba, 10 ga watan Disamba kafin bikin tunawa da kisan kiyashin Zariya na 2015, wanda tashar Platinum Tv ta sanya a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Zakzaky ya ce kan rashin tsaro?
Sheikh Ibraheem Zakzaky ya yi tambaya kan yadda 'yan bindiga da masu satar shanu ke ci gaba da ayyukansu da manyan makamai, ababen hawa ciki har da tankoki a yankunan karkara.
“Wadannan mutanen da ake a daji, masu sace shanu, ta yaya suka samu bindigogi? Me ya sa suke da wadannan makaman?"
"Yaya waɗanda ake kira ’yan bindiga za su mallaki motoci masu sulke, har da tankuna a cikin daji, kuma a kira su ’yan ta’adda? Ina suka samo tankokin?”
“Dole ku san cewa hukumomi suna da hannu a wannan matsala ta rashin tsaron. Idan suna so su dakatar da shi yau, za su dakatar.”
- Sheikh Ibraheem Zakzaky
Sheikh Zakzaky ya zargi gwamnati da barin lamarin matsalar rashin tsaro ya ta’azzara ba tare da daukar mataki ba.
“Idan suna so su dakatar da shi yau, za su dakatar, domin su ne ke tafiyar da shi. Kuma yanzu, ta hanyar gayyatar waɗanda suke aikata laifuffukan, za su kara dagula al’amarin.”

Kara karanta wannan
Kisan Zaria: Sheikh Zakzaky ya fadi abin da ya rage tsakaninsa da Buhari duk da ya rasu
- Sheikh Ibraheem Zakzaky

Source: Twitter
Maganarsa ta zo ne a lokacin da damuwar jama’a ke karuwa kan hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran ’yan ta’adda musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Zakzaky ya nuna yatsa ga gwamnatin Buhari
Yayin tunawa da abin da ya faru a Zariya, ya zargi gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, da gaza aiwatar da rahoton kwamitin bincike da aka mika tun watan Satumban 2016.
“Babu abin da aka yi. Har ma ba su amince da cewa wani abu ya faru ba. Shugaban kasa a lokacin ya ce yana bibiyar lamarin da kulawa. Amma ya kammala zangonsa na farko da na biyu, ba su ce komai ba.”
- Sheikh Ibraheem Zakzaky
Sheikh Zakzaky ya yi wa Trump martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kungiyar IMN a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya yi wa Donald Trump martani kan zargin kisan Kiristoci.
Sheikh Ibraheem Zakzaky ya karyata ikirarin da shugaban kasar na Amurka ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.
Shugaban na kungiyar Shi'a ya bayyana zargin a matsayin karya, mai tayar da hankali, kuma hadari ga zaman lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

