An Yi Wa Babban Dan Sanda Dukan Kawo Wuka kan Zargin Sata? Rundunar Ta Magantu
- Rundunar ‘yan sanda ta Lagos ta yi magana kan wani bidiyo da ya karade kafofin sadarwa game da jami'inta
- An yada bidiyo ne cewa an kama dan sandan yana sata, tana bayyana cewa an kai masa hari ne yayin aiki
- An kama mutane 13 da suka lakada wa jami’in duka, yayin da rundunar ta gargadi jama’a kan kai hari ga jami’an tsaro
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Rundunar ‘yan sandan Lagos ta fitar da sanarwa game da dukan wani jami'inta da aka yi a jihar.
Rundunar ta musanta wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta cewa an yi wa jami'in duka saboda ya yi sata.

Source: Facebook
Matasa sun lakadawa dan sanda duka
Legit Hausa ta samu wannan martani ne daga shafin rundunar wanda ta wallafa a manhajar X a yau Alhamis 11 ga watan Disambar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yada bidiyon ne cewa wani jami’in ‘yan sanda ana bugunsa ne kan zargin yana sata, inda ta bayyana cewa an kai masa hari ne yayin da yake kan aiki.
A cikin sanarwar, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Abimbola Adebesi ya ce bayanan da aka haɗa da bidiyon “karya ne kuma yaudara,” domin an juya gaskiyar lamarin ta hanyar yada jita-jita.
Rundunar ta ce jami’in da abin ya shafa inspekta ne da ke aiki a karkashin hukumar kula da ababen hawa ta Lagos, kuma yana aiwatar da dokar haramta ajiye motoci ba bisa ka’ida ba a titin Brown, Oshodi, lokacin da rikicin ya faru.

Source: Facebook
Yadda rigima ta barke da dan sanda
Jami’in ya dakatar da wani direba da ke ƙoƙarin ajiye mota bisa saba doka, sai dai direban ya mayar lamarin na tashin hankali.
A lokacin rikicin, inspektan ya yi harbi a ƙasa ba da gangan ba, wanda ya jawo hankulan wasu mutane da ke wucewa.
Wannan ya jawo taruwar mutane, inda aka dinga lakada masa duka har ya samu munanan raunuka.
Sanarwar ta ƙara da cewa ko da yake an ɗauki matakin ladabtarwa kan inspektan saboda rashin da’a, rundunar ta riga ta kama mutum 13 da aka gani a bidiyon suna bugunsa.
Kwamishinan ‘yan sandan Lagos ya yi Allah-wadai da yadda inspektan ya yi rashin da’a, amma ya yi gargaɗi mai tsanani kan hare-hare ga jami’an tsaro yayin da suke gudanar da ayyukansu na doka, yana mai cewa hakan babban laifi ne.
Yan sanda sun kama yan fashi a Lagos
An ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Lagos ta kama mutane 35 da ake zargi da fashi da makami a titi a yankunan Ajah da Elemoro.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama su ne a yayin atisayen sintiri da jami'an tsaro suka kaddamar don dakile ayyukan masu laifi.
Kakakin 'yan sandan jihar ya ce ana ci gaba da kai irin wadannan farmaki a jihar don tabbatar da doka da oda da maganain bata gari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

