An Samu 'Yar Hatsaniya a Zaman Tantance Jakadu a Majalisar Dattawa
- Zaman tantance jakadun Bola Ahmed Tinubu ya rikice bayan wanda aka turo sunansa daga Ekiti ya gaza kiran sunayen Sanatocin jiharsa da ke zauren
- Ƙungiyar kwamitin harkokin ƙasashen waje ta nuna damuwa da wannan kuskuren, tana cewa ɗan takarar jakadanci ya kamata ya nuna cikakken ƙwarewa
- Majalisar dattawa na ci gaba da tantance mutane 65 da Shugaba Tinubu ya aiko domin mukaman jakadanci a fadin duniya bayan shekaru babu wakilci
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Zaman tantance jakadun da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike zuwa Majalisar Dattawa domin tabbatarwa ya ɗauki sabon salo a ranar Laraba.
An yi 'yar hayaniya bayan a yayin da ake tantance Emmanuel Adeyemi, tsohon ɗan takara daga jihar Ekiti da Tinubu ya nemi a tantance shi a matsayin jakada.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa Adeyemi wanda shugaban ma’aikata ne a Ma’aikatar Harkokin Waje, ya shaida wa kwamitin gogewarsa a Hong Kong da Faransa, tare da matakin digirin digirgir a fannin diflomasiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisa ta tantance wadanda za su zama jakada
Jaridar Premium Times ta wallafa da ya ke kokarin gaishe da Sanatocin jiharsa, ya ambaci Opeyemi Bamidele da Yemi Adaramodu kawai, amma ya kasa tuna sunan na uku — Sanata Cyril Fasuyi.
Wannan ya sa aka tsaya cak, har wani daga cikin tawagarsa ya fara neman sunan a intanet, lamarin da ya fusata kwamitin matuka.
Sanata Asuquo Ekpenyong ya ce irin wannan rashin sanin muhimman bayanai abin damuwa ne, musamman ga wanda zai wakilci Najeriya a ƙasashen waje.

Source: Facebook
Sanatoci Adams Oshiomhole da Seriake Dickson su ma sun mara baya wajen sukar Adeyemi, yayin da Sanata Yunus Akintunde ya roki a yi masa afuwa da ganin kuskure ne na ɗan adam.

Kara karanta wannan
Mutumin da Tinubu ya nada ya yi 'abin kunya' yayin tantance shi a Majalisar Dattawa
Adeyemi na daga cikin manyan ’yan takarar Ekiti uku da suka hada da Erelu Angela Adebayo da Olumilua Oluwayemika.
An cigaba da tantance jakadu bayan hayaniya
Bayan lamarin Ekiti, kwamitin ya ci gaba da tantance wasu kwararrun jami’an diflomasiyyar Najeriya, ciki har da Ahmed Sulu Gambari, Maimuna Besto.
Haka kuma Majalisa ta tantance Monica Enebechi, Ahmed Monguno, Kingsley Onaga, Magaji Umar, da Aminu Nasir.
Wani abu da ya kuma duakar hankali shi ne tsohon Sanata kuma ɗan takarar gwamnan Ondo, Jimoh Ibrahim, ya bayyana a zaman, inda aka ce kawai ya wuce bayan gaida majalisa duk da ba a tsara tantance shi a ranar ba.
Ana ci gaba da tantance jakadun ne biyo bayan bukatar da Shugaba Tinubu ya aika a makon da ya gabata, inda ya nemi majalisa ta tabbatar da jakadu 65, bisa tanadin sashe na 171 na kundin tsarin mulkin 1999.
Majalisa ta amince a hukunta 'yan ta'adda
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta Najeriya ta ɗauki mataki mai tsauri, inda ta amince da gyaran dokar ta’addanci ta 2022 domin a hukunta masu garkuwa da mutane yadda ya dace.
Majalisa ta tabbatar da cewa duk wanda ya ke da hannu a garkuwa da mutane ko ya taimaka ta kowace hanya, zai fuskanci hukuncin kisa domin dakile karuwar matsalar satar bayin Allah.
Sabon gyaran ya shafi masu shirya laifin, masu ɗaukar nauyi, masu tura bayanai, masu bada mafaka ko kayan aiki, da duk wanda ya san an aikata laifi amma ya taimaka aka yi shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

