Ta Leko Ta Koma: Yadda Abdullahi Ramat Ya Rasa Kujerar Shugabancin Hukumar NERC

Ta Leko Ta Koma: Yadda Abdullahi Ramat Ya Rasa Kujerar Shugabancin Hukumar NERC

  • Shugaba Bola Tinubu ya nemi majalisar dattawa ta tabbatar da sababbin Shugabannin NERC, amma sunan Abdullahi Ramat ya yi layar zana daga sakon
  • A baya, Majalisar Dattawan ta ce Injiniya Ramat, ya gamu da cikas bayan rikice-rikicen siyasa da koke-koken jama’a a kansa, wanda ya sa dole aka dakata
  • Rahotanni sun nuna rikicin siyasar Kano ya taka rawa wajen hana tabbatar da shi, yayin da gwamnati ke duba Dr. Oseni a matsayin sabon shugaban hukumar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da mutane biyu da ya zaɓa domin zama kwamishinoni a Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC).

A cikin wasikar da aka karanta a zaman majalisa ta hannun Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, an lura cewa sunan wanda aka fara bada shawara ya zama shugaban NERC, Abdullahi Ramat.

Kara karanta wannan

An samu 'yar hatsaniya a zaman tantance jakadu a Majalisar Dattawa

Ramat ya rasa kujerar shugabancin NERC
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, Abdullahi Ramat Hoto: Bayo Onanuga/Abdullahi Garba Ramat
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Tinubu ya bayyana cewa, bisa ga kundin dokar wutar lantarki ta 2023, an sake mika sunayen Aisha Mahmoud Kanti-Bello da Fouad Animashaun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu bai nemi a tabbatar da Ramat ba

Rahoton ya ce sabuwar wasikar Tinubu ta soke wacce ya turo a ranar 6 ga Agusta 2025, wacce ta ƙunshi sunan Ramat domin maye gurbin tsohon shugaban hukumar, Injiniya Garba Usman.

Bayan tura sunansa a lokacin, Ramat ya yi tattaki da magoya baya zuwa ofishin NERC yana ƙoƙarin fara aiki a matsayin shugaban rikon kwarya, bayan sanarwa da hadimin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga ya fitar ta ce zai iya fara aiki.

Sai dabayan wannan sanarwa, daga baya fadar shugaban kasa ta soke wannan umarni, ta bukaci ya jira tantancewar majalisa kafin ya shiga ofis don fara aiki.

Takaddama ta hana tabbatar da Ramat

A cikin watanni biyar bayan turo sunansa, an yi jerin zanga-zanga a majalisa domin neman tabbatar da shi. Shugaban masu zanga-zangar, Ahmed I. Suleiman, ya zargi majalisa rashin adalci.

Kara karanta wannan

Jami'in kwastam da ya yi fatali da cin hancin $50,000 ya samu karin girma

Sun rubuta wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Tinubu takarda, suna nuna cewa Ramat ya dace da mukamin saboda gogewarsa a gwamnati da harkokin makamashi.

Sai dai wasu kungiyoyin Kano sun zargi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da lalata lamarin saboda takun siyasa tsakaninsa da tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje.

Ana zargin akwai tsamin siyasa tsakanin Barau da Ganduje, kuma ya shafi Ramat
Tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Barau Jibrin Hoto: Barau I Jibrin
Source: Twitter

Har ma aka yi zargin an bada cin hancin Dala miliyan 10, wanda majalisar ta karyata, ta kira zargin da sharri karara domin bata wa Majalisa suna.

Kwamitin yada labarai na majalisa, Yemi Adaramodu, ya ce an dakatar da batun ne saboda koke-koken jama’a a kan Injiniya Ramat.

Daga bisani, Alwan Hassan — wanda ya jagoranci zargin majalisa — ya fito ya bada haƙuri, yana cewa zargin da suka yi ba daidai ba ne kuma bai yi adalci ga majalisar ba.

A yanzu, majiyar gwamnati ta ce fadar shugaban kasa na shirin aika sunan Dr. Musiliu Oseni, wanda ya rike mukamin shugaban rikon kwarya ya maye gurbin na Ramat.

Shugaba Tinubu ya ba Ramat mukami

A baya, mun wallafa cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NERC).

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Sanata Ndume ya yabi Shugaba Tinubu, ya ba gwamnoni shawara

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayar ta hannun Olusegun Dada a wallafa ta tabbatar da nadin, inda aka hango shi yana karban takarda daga Ministan Makamashi.

Sanarwar ta bayyana cewa Injiniya Ramat zai fara aiki ne a matsayin mukaddashi, har sai Majalisar Dattawa ta kammala tantance shi kamar yadda doka ta tanada domin ya kama aiki ganga-ganga.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng