Daga na Gaba: Bukarti Ya Shawarci Tinubu Ya Rage Jami'an Tsaron 'Dansa, Seyi
- Fitaccen lauya mai kare hakkin 'dan adam, Dr. Bulama Bukarti ya yi kira da a gyara tsarin tsaro, yana mai cewa tsarin ya lalace tun daga sama zuwa ƙasa
- Ya ce maganganun Wole Soyinka kan yawan jami’an tsaro da ke rakiyar ɗan shugaban ƙasa ba sukar mutum ɗaya ba ce, ra'ayin jama'a ne a kan tsarin tsaro
- Bukarti ya nemi Shugaba Tinubu ya fara da rage tsaron da ke tattare da iyalinsa domin kafa kyakkyawan misali ga sauran shugabanni da masu rike da madafai
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fitaccen lauya, Dr. Audu Bulama Bukarti, ya bayyana damuwa kan yawan jami’an tsaro da ake bai wa iyalan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Lauyan da ke fafutukar kare hakkin 'dan adam ya kara da cewa wannan al’ada alamar lalataccen tsari ne da ke bukatar gyara cikin gaggawa.

Source: Facebook
Ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Channels TV bayan Shugaba Tinubu ya kara nanata umarnin a janye jami'an yan sanda da ke tsaron manyan 'yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bulama Bukarti ya aminta da kalaman Wole Soyinka
A hirar, Bulama Bkarti ya aminta da kalaman Farfesa Wole Soyinka, inda ya ce tawagar tsaron da ke rakiyar iyalan Shugaban Kasa sun yi yawa.
Barista Bukarti ya ce bai kamata a dauki maganar Soyinka a matsayin sukar Shugaban Tinubu ko iyalinsa kai tsaye ba, illa dai sukar tsarin da ya lalace matuka.
Ya ce:
“Bai kamata Fadar Shugaban Kasa ta dauki maganar Farfesa Wole Soyinka a matsayin suka ga mutum ɗaya ba. Suka ce kan tsarin gwamnati da ya lalace kuma yake bukatar gyara. Idan kuwa umarnin Shugaban Kasa na tsaro suna da muhimmanci, to ya kamata ya fara daga mutanen da ke kusa da shi.”
Bukarti ya bayyana cewa ko da yake ɗan shugaban kasa yana iya bukatar kariya, yawan motocin tsaro da ake tura masa ya wuce kima, kuma hakan yana kafa abin koyi mara kyau.

Kara karanta wannan
Bayan korafe korafe, Tinubu ya bada sabon umarni kan janye 'yan sanda daga gadin manya
Bukarti ya magantu a kan tsaron Najeriya
Bukarti ya ce tsarin da ake ciki, inda iyalan shugabanni ke yawo da jerin tsaro irin na manyan jami’an gwamnati, ya jawo rudani da amfani da jami’an tsaro ba bisa ka’ida ba a fadin ƙasa.
Ya ce gwamnoni ma sun dauki wannan salo, suna bai wa matansu da ’ya’yansu ’yan sanda da yawa fiye da bukata, abin da ya haifar da karancin jami’an tsaro a al’umma.

Source: Facebook
Ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki sabon matsayi na adalci da daidaito wajen al’amuran tsaro, musamman a halin tsaron kasar nan.
A kalaman Bukarti:
“Dole mu daina wannan al’ada. Kuma wurin da ya dace mu fara shi ne a wurin ɗan Shugaban Kasa. Komai na gyara daga gida yake fara faruwa.”
Bukarti ya nemi Shugaba Tinubu ya bada umarnin a janye rakiyar tsaro irin ta manyan motocin tawaga daga ɗansa, ya ce jami’an DSS biyu ko uku tare da ’yan sanda kaɗan sun isa.
Bulama Bukarti ya shawarci tawagar Amurka
A wani labarin, mun wallafa cewa fitaccen masani kan tsaro kuma lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam, Barista Bulama Bukarti, ya ba da shawara ga tawagar Amurka da ta zo Najeriya.
Tawagar ƙarƙashin ɗan Majalisa Riley Moore ya sauka a Najeriya ne domim nazarin batutuwan tsaro, musamman zargin kisan Kiristoci da aka nace cewa ana yi a ƙasar.
Bukarti ya bayyana cewa bai kamata tawagar ta tsaya a wuri ɗaya kawai ba, sai dai ta zaga Arewacin Najeriya gaba ɗaya domin ganin yadda Musulmai da Kiristoci ke rayuwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

