Lita Ta Haura N1,000: An Jero Jihohi 3 da Aka fi Sayen Fetur da Tsada a Najeriya
- 'Yan Najeriya sun rage amfani da fetur, inda suka iya sayen lita biliyan 1.59 a Nuwamba, sabanin lita biliyan 1.76 da suka sha a Oktoba
- Duk da haka, hukumar NMDPRA ta ce kamfanin NNPCL ya shigo da man fetur mai yawa daga kasar waje saboda wasu manyan dalilai
- Sababbin bayanai sun nuna farashin litar mai ya kai N895 zuwa N908 a Legas, amma lita ta kai N955 zuwa N1,018 a wasu jihohi uku
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Amfani da fetur a Najeriya ya ragu zuwa kusan lita biliyan 1.59 a Nuwamba 2025, bayan da aka samu karuwar masu sayen mai a Oktoba, 2025, inda aka sayi lita biliyan 1.76.
Rahoton da hukumar NMDPRA ta fitar ya nuna cewa 'yan Najeriya sun koma sayen litar man fetur miliyan 56.74 a rana, wanda ya yi kasa da yadda suka saya a Oktoba.

Source: UGC
An rage amfani da fetur a Najeriya
A cikin jimillar lita biliyan 1.59 da aka saya a Nuwamba, matatun cikin gida ne suka samar da lita miliyan 19.5 a kowace rana,sama da lita miliyan 17.08 da aka samu a Oktoba, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma an ce matatar Dangote, wadda ta kara karfin tace manta daga lita miliyan 18.03 a rana a Oktoba zuwa lita miliyan 23.52 a rana a watan Nuwamba ce ta samar da fetur mafi yawa a kasar.
Hukumar NMDPRA ta bayyana cewa wannan karin ya zama babban ci gaba wajen rage dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje.
Sai dai duk da haka, matatun gwamnati na Port Harcourt, Warri da Kaduna ba su tace ko fitar da ko lita daya ba saboda gyare-gyare da kuma rufe su da aka dade ana yi.
Shigo da fetur daga waje ya karu sosai
Duk da karin samar da mai daga Dangote, shigo da fetur daga ketare ya karu, inda ya kai lita miliyan 52.1 a rana, daga lita miliyan 27.6 a Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An kama wanda ya jagoranci kashe 'dan Majalisa a Najeriya, ya fara bayani
A cewar hukumar NMDPRA, dalilan karin shigo da mai sun hada da:
- karancin samar da mai da aka yi a Satumba da Oktoba
- bukatar tara isasshen man karshen shekara
- kokarin NNPCL na cike manyan tankuna domin tabbatar da wadataccen man kasa
- jinkirin sauke jiragen dakon mai guda 12 da aka shirya za su sauka a Oktoba amma suka sauka a Nuwamba
Farashin litar fetur ya yi tsada sosai

Source: Getty Images
Ko da yake farashin mai ya kai matsakaicin N895 zuwa N1,018 a lita, yawancin ‘yan Najeriya sun ci gaba da dogaro da fetur wajen tuka motoci, jigilar jama’a da kaya da kunna janareta saboda matsalar wutar lantarki.
A watan Oktoba kadai, kudin da ‘yan kasa suka kashe kan man fetur ya kai Naira tiriliyan 1.58, amma a Nuwamba, inda ake sayen litar fetur N900 ko sama da haka, 'yan Najeriya sun kashe Naira tiriliyan 1.43 a sayen man.
Channels TV ta rahoto cewa, bayanan NMDPRA sun nuna babban banbanci a farashin da ake sayar da litar man fetur a tsakanin jihohin kasar:
- Lagos: N898 – N908
- Sokoto, Calabar, Maiduguri: N955 – N1,018
Masana sun ce banbancin ya samo asali daga matsalolin hanyoyin sufuri, tsadar jigilar kaya zuwa Arewa da wasu jihohin Kudu da kuma kalubalen tsaro da rashin isasshen wurin ajiya.
An samu karancin fetur a Arewa
A wani labari, mun ruwaito cewa, matsalar karancin fetur ta ci gaba da addabar Arewa, musamman Sokoto, inda ta janyo tsadar sufuri da cunkoson jama’a a gidajen mai.
Rahotanni sun bayyana cewa an rufe yawancin gidajen mai, yayin da kaɗan daga cikin wadanda aka bude suke sayar da lita tsakanin ₦960 zuwa ₦970, a Oktoba, 2025.
Mazauna Sokoto sun roƙi gwamnatin jihar, da hukumar DPR, da kuma hukumomin tarayya da su hanzarta daukar mataki domin tilasta masu gidajen mai su koma aiki yadda ya dace.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

